Thursday, March 19
Shadow

Duk Labarai

Tinubu ya jajanta wa iyalan Birgediya Janar Musa Uba

Tinubu ya jajanta wa iyalan Birgediya Janar Musa Uba

Duk Labarai
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya tabbatar da mutuwar jami'in sojan ƙasar Birgediya Janar Musa Uba, wanda mayaƙan ƙungiyar Iswap suka kashe a jihar Borno. An fara fargabar mutuwar Janar Uba ne bayan ƙungiyar ta yi iƙirarin kashe shi, da kuma fitar da wani bidiyo. Wata sanarwa da rundunar sojan Najeriya ta fitar ta ce a ƙarshen makon da ya gabata ne 'yanbindigar suka yi wa dakarunta kwanton ɓauna, waɗanda janar ɗin ke jagoranta. Zuwa yanzu rundunar ba ta ce komai ba game da bidiyon da ke yawo a intanet. Sai dai cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Talata, Shugaba Tinubu ya ce mutuwar janar ɗin "ta kaɗa" shi. "A matsayina na babban kwamandan tsaro na ƙasa, na ji takaici da mutuwar sojojinmu a bakin aiki. Allah ya bai wa iyalan Bi...
Wata Kungiyar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje tace Shugaba Trump ya gaggauta kawo Khari Najeriya inda tace Ana kokarin mayar da kasar Kasar Musulinci ce

Wata Kungiyar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje tace Shugaba Trump ya gaggauta kawo Khari Najeriya inda tace Ana kokarin mayar da kasar Kasar Musulinci ce

Duk Labarai
Wata kungiya me suna The Global Coalition for Security and Democracy in Nigeria ta 'yan Najeriya wadda suka kafa a kasar Amirka tace ta yi na'am da Amurka ta saka Najeriya cikin kasashen da zata rika sakawa ido. Kumgiyar tace tana kira ga shugaban kasar Amurka, Donald Trump da ya gaggauta kawo Kharin da yace zai kawo Najeriya. Kungiyar ta bayyana hakane a sanarwar data fitar ta bakin shugabanta, Comrade Frederick Odorige inda tace tana goyon karfafa tsaro da Dimokradiyya a Najeriya.
Kaso 90 na Musulman Najeriya Sunni ne, Inji Tsohon Hadimin Shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad

Kaso 90 na Musulman Najeriya Sunni ne, Inji Tsohon Hadimin Shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad

Duk Labarai
Tsohon Hadimin Shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad ya bayyana cewa, kaso 90 na musulman Najeriya Sunni ne. Ya bayyana hakane a martanin da yakewa 'Yar siyasar kasar Canada, Goldie Ghamari inda tace Najeriya na hada kai da kasar Iran dan Khasye Kiristoci. Yace abinda ma bata sani ba shine kaso 90 na musulman Najeriya Sunni ne. Yace 'yan kasar waje suna amfani da rarrabuwar mu ne wajan cimma burinsu inda yace sai mun hada kai. https://twitter.com/BashirAhmaad/status/1990889063834861572?t=RKCwoiSicU5RhxOM7Q_0VA&s=19
Allah Sarki Kalli Bidiyon: Yanda Tauraruwar Kannywood, Fatima Hussain Cikin kuka tare Alhinin abinda akawa daliban makarantar mata ta jihar Kebbi

Allah Sarki Kalli Bidiyon: Yanda Tauraruwar Kannywood, Fatima Hussain Cikin kuka tare Alhinin abinda akawa daliban makarantar mata ta jihar Kebbi

Duk Labarai
Tauraruwar fina-finan Hausa, Fatima Hussain ta fito ta bayyana takaici kan garkuwa da dalibai mata 25 da aka yi a jihar Kebbi. Ta bayyana hakane a shafinta na sada zumunta inda tace idan ba'a so a yi karatu ne a kulle makarantun mana. Tace duka yaushe aka sace dalibai mata amma gashi an sake yi. Tace daliban na da kananan shekaru. https://www.tiktok.com/@fateeemahussain/video/7574376952191028500?_t=ZS-91WmE2naJV3&_r=1
Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un Kalli Bidiyon Da Duminsa: Mummunan Abinda Tshagyeran dhajiy sukawa Sojowjin da aka aika su kubutar da dalibai ‘yan mata ‘yan makarantar jihar Kebbi

Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un Kalli Bidiyon Da Duminsa: Mummunan Abinda Tshagyeran dhajiy sukawa Sojowjin da aka aika su kubutar da dalibai ‘yan mata ‘yan makarantar jihar Kebbi

Duk Labarai
Rahotanni da Duminsa sun bayyana cewa 'yan Bìndìgà a Daji sun afkawa sojojin da aka aika su kubutar da dalibai 'yan mata da aka yi garkuwa dasu a jihar Kebbi. A Bidiyon wanda kafar Sahara Reporters ta wallafa, an ga sojojin kwakkwance cikin Jiyni wasu an Harbesu a kafa wasu a sassa daban-daban na jikinsu. Dalibai mata 25 ne dai 'yan Bìndìgàr suka yi garkuwa dasu inda wasu biyu suka kubuta. Danna nan dan kallon Bidiyon https://twitter.com/SaharaReporters/status/1991074295015997845?t=50Y5DUr-jQN8s0-V8zdaXQ&s=19
Kalli Bidiyon jawabinsa: Yanzu ace daya daga cikin ‘ya’yanmu ne aka dauke ya zamu ji? Gaskiya ya kamata ayi wani abu game da daliban makarantar Jihar Kebbi>>Inji Sanata Abdul Ningi

Kalli Bidiyon jawabinsa: Yanzu ace daya daga cikin ‘ya’yanmu ne aka dauke ya zamu ji? Gaskiya ya kamata ayi wani abu game da daliban makarantar Jihar Kebbi>>Inji Sanata Abdul Ningi

Duk Labarai
Sanata Abdul Ningi ya bayyana takaici kan matsalar tsaron da ake fama da ita a Najeriya. Yace kwanaki kadan da Khashye Brigadier General gashi an sace daliban makaranta yace dan haka ya kamata ayi wani abu. Yace a daina cewa wannan bangaren ne ke yiwa wancan bangare ko kuma wannan addinine kewa wancan addini, inda yace a hada kai a magance matsalar. Kalli Bidiyon hirar anan https://twitter.com/ChuksEricE/status/1990836849506500627?t=7pF3ObU4kFRKrjbke33xGQ&s=19
Ji yanda Gwamnan jihar Kebbi ya bayyana cewa DSS sun gargadesu game da yunkurin dauke daliban makarantar ‘yanmata ta MAGA, kuma sun kai jami’an tsaro amma Mintuna 30 kamin tshageran daji su kwashe daliban sai jami’an tsaron suka bar makarantar

Rahotanni na fitowa cewa hukumar 'yansandan Farin kaya ta DSS yi gargadin cewa ana shirin kai wa makarantar 'yan mata ta MAGA dake jihar Kebbi hari. Gwamman jihar Kebbi, Mohammed Nasir Idris ya tabbatar da cewa DSS sun sanar dasu game da gargadin kuma suka bayar da shawarar a gudanar da taron tsaro kan lamarin. Gwamnan yace sun gudanar da taro akan tsaro aka kai jami'an tsaro makarantar dan su tsare daliban amma sai suka buge da daukar hotuna da dalibai 'yan mata 'yan makarantar. Gwamnan yace mintuna 30 kamin a kai harin, jami'an tsaron dake baiwa makarantar kariya sun janye suka kama gabansu. Gwamnan ya kai ziyara makarantar ranar Litinin da misalin karfe 6:45 na safe kamar yanda kafar Pointblacknews.com ya ruwaito. Kafar tace wani jami'in tsaro ya bayyana mata cewa, gwamna...
Kalli Bidiyo: Mun Gano Najeriya na aiki da qasar Iyràn a munafurce sannan Gwamnatin Najeriya na da hannu kan matsalar tsaro dake faruwa>>Inji Tsohuwar Firaiministar Canada, Goldie Ghamari

Kalli Bidiyo: Mun Gano Najeriya na aiki da qasar Iyràn a munafurce sannan Gwamnatin Najeriya na da hannu kan matsalar tsaro dake faruwa>>Inji Tsohuwar Firaiministar Canada, Goldie Ghamari

Duk Labarai
Tsohuwar Firaiministar kasar Canada, Goldie Ghamari ta bayyana cewa, sun gano Najeriya na aiki da kasar Iran a munafurce. Sannan ta zargi Gwamnatin Tarayya da hannu a matsalar tsaron da ake fama da ita a Najeriya. Ta bayyana hakane a wata hira da aka yi da ita da dan jaridar kasar Ingila, Piers Morgan da ministan harkokin kasashen waje na Najeriya, Yusuf Tuggar Maitama. Tace A tsarin Najeriya ya kamata idan shugaban kasa ya zama musulmi, mataimakinsa ya zama kirista hakanan idan shugaban kasa kiristane, mataimakinsa zai zama Musulmi. Tace amma a gwamnatin tinubu babu wakilcin kiristoci inda ta zargi cewa ana muzgunawa Kiristoci.
Tabbas ana Mhuzghuna mana a Najeriya kuma muna maraba da zuwan Trump>>Inji Reverend Ezekiel Dachomo

Tabbas ana Mhuzghuna mana a Najeriya kuma muna maraba da zuwan Trump>>Inji Reverend Ezekiel Dachomo

Duk Labarai
Babban malamin Kirista, Reverend Ezekiel Dachomo ya bayyana cewa, lallai anawa Kiristoci Khisan Kyiyashi a Najeriya. Yace kuma Gwamnati saboda ta musulunci ce bata damu ba. Ya bayyana hakane a hirar da dan jaridar Ingila, Piers Morgan yayi dashi. Yace a rana daya ya taba binne gawarwaki sama da 500. Yace dan haka su zuwa Trump Najeriya kamar taimakon da Allah yawa Bani Israyla ne. https://twitter.com/PiersUncensored/status/1990829682086797805?t=bgW-mLErLOHixlAB7I87Lg&s=19
Lauya ya bayyana yanda kowa zai iya mallakar gida kyauta

Lauya ya bayyana yanda kowa zai iya mallakar gida kyauta

Duk Labarai
Wani Lauya ya bayyana yanda mutane zasu iya mallakar Gida Kyauta ba tare da ko sisi ba. Ya bayyana cewa mutum kawai duk gudan da ya ba kowa ya shiga ya zauna. Yace idan mutum ya kai shekaru 10 zuwa 12 a cikin gidan kuma me gida bai zo ba, to gidan ya zama nashi, yace amma idan me gidan yazo kamin shekaru 10 zuwa 12 za'a kwace ne a bashi kayanshi. Yace amma idan ya wuce wadancan shekarun bai zo ba, to gidan ya zama mallakin wanda ke zaune a ciki kuma ko kotu aka je ba za'a kwace gidan ba. https://www.youtube.com/watch?v=rrOTVJOPDJk?si=566krDWNS8mYpcgi