Friday, March 20
Shadow

Duk Labarai

Ko Kadan Bana Jin tsoron Shugaban Amurka Donald kuma nasan Maqaryacine saboda yawa kasarmu karya>>Inji Sanata Barau Jibrin

Ko Kadan Bana Jin tsoron Shugaban Amurka Donald kuma nasan Maqaryacine saboda yawa kasarmu karya>>Inji Sanata Barau Jibrin

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Sanata Barau Jibrin Maliya ya bayyana cewa ko kadan baya jin tsoron shugaban kasar Amurka, Donald Trump inda yace Shi dan Najeriya ne kasa me cin gashin kanta, kuma dan Majalisa, kuma mataimakin kakakin majalisar Dattijai dan haka sai ya fadi ra'ayinsa. Ya bayyana cewa, Trump yawa Najeriya karya dan haka ya kamata a gaya masa bai yi daidai ba. Sannan ya gayawa Kakakin majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio cewa shima ya daina jin tsoron Trump ya fito ya fadi abinda ke zuciya...
Satar Arziki ne zai kawo Trump Najeriya ba taimakon Kiristoci ba>>Inji Kungiyar Kare Muradun Yarbawa, Afenifere

Satar Arziki ne zai kawo Trump Najeriya ba taimakon Kiristoci ba>>Inji Kungiyar Kare Muradun Yarbawa, Afenifere

Duk Labarai
Kungiyar Kare muradin yarbawa ta Afenifere ta bayyana cewa, shugaban kasar Amurka, Donald Trump zai shigo Najeriya ne da niyar satar arzikin kasa amma ba maganar tseratar da Kiristoci ba. Kungiyar ta bakin sakataren yada labarinta, Mr. Jare Ajayi tace hujjar da Trump ya kawo ta banza ce kawai yana neman hanyar shigowa Najeriya ne. Yace Trump na son amfani da wannan damar ne wajan tilasta Najeriya sayen abubuwa daga Amurka musamma makamai saboda baya jin dadin huldar da Najeriya ke yi da kasar China. Yace sannan Amurkar ta ji haushin kalaman da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima yayi a taron majalisar Dinkin Duniya inda ya goyi bayan kafa kasar Falasdiynawa. Kungiyar ta yi kira ga 'yan Najeriya dama shuwagabannin da su kaucewa yin kalaman da zasu kara zhugha Amurka tace ...
Da Duminsa: A karin Farko Musulmi ya zama magajin garin New York City, na kasar Amurka

Da Duminsa: A karin Farko Musulmi ya zama magajin garin New York City, na kasar Amurka

Duk Labarai
Zohran Mamdani wanda musulmi ne ya ci zaben magajin garin New York City a kasar Amurka. Wannan shine karin farko da hakan ta faru a tarihin Birnin Na New York, hakanan Zohran Mamdani dan Asalin kasar Uganda ne, daga baya ya je kasar Amirka ya zama dan kasa. Zohran Mamdani ya kayar da tsohon gwamnan jihar New York Andrew Cuomo wanda Shugaban kasar, Donald Trump da Attajirin Duniya Elon Musk suka goyi baya. A baya dai, Donald Trump yace idan Zohran Mamdani ya ci zaben magajin garin New York, zai dakatar da kudaden da gwamnatin tarayya ke aikawa birnin.
Baku isa ku hanamu kare kiristoci a Najeriya ba>>Sanatan Amurka ya mayarwa da China Martani

Baku isa ku hanamu kare kiristoci a Najeriya ba>>Sanatan Amurka ya mayarwa da China Martani

Duk Labarai
Sanatan kasar Amirka, Riley Moore ya mayarwa da kasar China martani bayan da ta gargadi America da cewa kada ta yi katsalandan akan harkar tsaron cikin gida Najeriya Sanatan yace shugaban kasarsu Trump akan Daidai yake kuma babu wanda zai hanashi kaiwa Kiristoci dauki a Najeriya Yace Ba China ce zata koya musu hulda da kasashen wajeba. https://twitter.com/RepRileyMoore/status/1985750168281698655?t=a9vfqCSiDNYmEKnvsuI-Hg&s=19
Ba addini ne kawai ke haifar da rikicin Najeriya ba – EU

Ba addini ne kawai ke haifar da rikicin Najeriya ba – EU

Duk Labarai
Ƙungiyar Tarayyar Turai ta EU ta ce ta fahimci cewa ba addini ne kaɗai ke haifar da rikice-rikice a Najeriya ba. Cikin wata sanarwa kakain ƙungiyar da Anouar El Anouni ya fitar ya ce ƙungiyar EU na jajanta wa imjutanen da rikicin ya rutsa da su kudanci da arewa maso gabashin ƙasar. Matakin na ƙungiyar EU na zuwa ne bayan da shugaban Amurka, Donald Trump ya yi barazanar ɗaukar matakin soji kan Najeriya, kan abin da ya kira kisan Kiristoci a ƙasar. Sai dai EU ta ce akwai abubuwa da dama da ke haifar da rikicin ba addini kaɗai ba. “Mun fahimci cewa akwai abubuwa masu yawa da ke haifar da rikici a Najeriya, addini guda ne daga cikinsu, amma ba shi kaɗai ba,'' in ji Mista El Anouni.
A karo na 2, Sanata Godswill Akpabio karara ya bayyana tsoron Trump yake ji yayin da ‘yan Najeriya suka bukaci jin Abinda majalisar Dattijai zata ce kan Barhazhanar da Trump din yawa Najeriya

A karo na 2, Sanata Godswill Akpabio karara ya bayyana tsoron Trump yake ji yayin da ‘yan Najeriya suka bukaci jin Abinda majalisar Dattijai zata ce kan Barhazhanar da Trump din yawa Najeriya

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa an samu wata sa in sa tsakanin Kakakin majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio da mataimakinsa, Sanata Jibrin Barau. A na daf da gama zaman majalisar na ranar Talata ne sai Akpabio yace 'yan Najeriya da yawa sun mika musu bukatar jin abinda zasu ce kan barazanar da shugaban kasar Amurka, Donald Trump yawa Najeriya. Saidai yace wanene shi, bai isa ya baiwa Trump Amsa ba, suna jiran abinda duk Gwamnatin tarayya tace akan lamarin haka za'a yi. Saidai Sanata Barau Jibrin ya mike yacewa Akpabio ka daina jin tsoron Trump kai ne mutum na 3 mafi mukami a Najeriya kasa me cin gashin Kanta. Barau yace Trump makaryaci ne kuma yawa Najeriya karyar cewa ana yiwa kiristoci kisan kiyashi kuma ya kamata a gaya masa ba gaskiya bane abinda ya fada. Saidai Akpab...
Gwamnatin Najeriya ta gargadi Trump kada ya dauki matakin da zai Tharwatsa Najeriya ta koma kamar kasar Sudan

Gwamnatin Najeriya ta gargadi Trump kada ya dauki matakin da zai Tharwatsa Najeriya ta koma kamar kasar Sudan

Duk Labarai
Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar ya yi watsi da gargaɗin Shugaba Trump na ɗaukar matakin soji kan Najeriya. Yayin da yake jawabi a taron manema labarai da ya gudanar a birnin Berlin tare da takwaransa na Jamus, Mista Tuggar ya ce Najeriya na bayar da ƴancin addini tare da aiki bisa doron doka. ''Kundin tsarin mulkin Najeriya da dokokin ƙasar sun haramta cin zarafin addini tare da bayar da damar ƴancin gudanar da addini'', in ji shi. ''Babu yadda za a yi gwamnatin Najeriya ta goyi bayan ta kowane fanni na yadda za a ci zarafin mabiya wani addini'', in ji Tuggar. Ministan harkokin wajen na Najeriya gwamnatin ƙasar ba za ta yarda a mayar da ƙasar tamkar Sudan ba. ''Abin da muke so duniya ta fahimta shi ne ba ma so a ƙirƙiri wata Sudan ɗin, Najeriya na da y...
Hukumar ‘Yansandan farin kaya DSS ta kori ma’aikata 115 daga aiki

Hukumar ‘Yansandan farin kaya DSS ta kori ma’aikata 115 daga aiki

Duk Labarai
Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya, DSS ta ce ta kori wasu jami'anta 115 daga aiki, saboda abin da ta kira wasu sauye-sauye da hukumar ke yi. Cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, a ranar Talata, DSS ta shawarci al'umma su kauce wa mu'amala da jami'an a matsayin wakilan hukumar. Hukumar ta kuma wallafa sunaye da hotonan jami'an 115 da ta ce ta koran a shafinta intanet. Bayanan mutanen da hukumar ta fitar sun nuna cewa an kori mutanen ne tsakanin shekarar 2024 zuwa 2025. Matakin na zuwa ne bayan da a watan Oktoban da ya gabata hukumar ta kama wasu tsoffin jami'anta biyu bisa zargin amfani sa sunan hukumar suna damfarar mutane.