Saturday, March 21
Shadow

Duk Labarai

Da Duminsa:Kotu ta kwace kujerar dan majalisar wakilai daga jihar Zamfara bayan da ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC

Da Duminsa:Kotu ta kwace kujerar dan majalisar wakilai daga jihar Zamfara bayan da ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC

Duk Labarai
Babbar Kotun tarayya dake Abuja ta kwace kujerar dan majalisar wakilai, Abubakar Gummi bayan da ya bar jam'iyyar PDP zuwa APC Abubakar Gummina wakiltar mazabun Gummi/Bukkuyum ne a majalisar wakilai ta tarayya. Mai shari'a, Obiora Egwuatu ne ya yanke wannan hukunci inda yace kada kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas ya sake kallon Abubakar Gummi a matsayin dan majalisar. Hakanan alkalin ya kuma baiwa hukumar zabe me zaman kanta INEC umarnin sake shirya wani zabe dan cike gurbin dan majalisar nan da kwanaki 30.
Duk da Jhuyin mulkin bai faru ba, ji yanda ministan kudi, Wale Edun ya yanke jiki ya Fhadi sumamme bayan da ya ga sunansa cikin wadanda sojojin da suka Shirya yiwa shugaba Tinubu Jhuyin mulki zasu Shekye

A kwanakin da suka gabata ne Ministan Kudi, Wale Edun ya kwanta rashin lafiya inda har ta kai ga an kaishi kasar Ingila dan ya ga Likitocin sa. Sahara reporters sun ce yanke jiki yayi ya fadi saidai gwamnati ta musanta hakan amma daga baya Gwamnatin ta tabbatar da rashin lafiyar ministan. A yanzu sabon Labari da Sahara reporters din suka samu shine cewa, Ministan Kudin, ya ga sunanshi a cikin jerin sunayen wadanda sojojin da suka shirya juyin mulki zasu kashene, abinda ya firgitashi kenan ya yanke jiki ya fadi sumamme. Rahotan yace Wale Edun shine Mutum na 4 a cikin jerin wadanda Sojojin da suka shirya Jhuyin mulkin suka so shekyewa.
Da Duminsa: Sojoji 2 cikin wadanda akw zargi da yunkurin yiwa shugaba Tinubu Jhuyin mulki sun tsere an nemesu an rasa

Da Duminsa: Sojoji 2 cikin wadanda akw zargi da yunkurin yiwa shugaba Tinubu Jhuyin mulki sun tsere an nemesu an rasa

Duk Labarai
Rahotanni sun ce 2 daga cikin sojojin da ake zargi da yunkurin yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu Jhuyin mulki sun tsere. Jaridar Cable ce ta ruwaito labarin inda tace cikinsu akwai JM Ganaks wanda ke da mukamin Major da lambar aiki N/14363 sannan yana aiki ne a Jaji. Sannan akwai G Binuga wanda shi kuma Captai ne me lambar aiki N/167722 wanda dan Asalin jihar Taraba ne. Thecable tace zuwa yanzu akwai sojoji 30 da ake tsare dasu ake tuhumarsu bisa zargin yunkurin yin Jhuyin mulkin.
Da Duminsa: Kwanaki kadan da Bayyanar rahotannin yunkurin Jhuyin mulki, An sake canjawa sojojin Najeriya wajan aiki

Da Duminsa: Kwanaki kadan da Bayyanar rahotannin yunkurin Jhuyin mulki, An sake canjawa sojojin Najeriya wajan aiki

Duk Labarai
Rahotanni sun ce hukumar sojojin Najeriya ta canjawa manyan sojoji 60 guraren aiki. Hakan na kunshe a wata sanarwa ne data bayyana a yau 30 ga watan October inda aka ce sojojin su koma sabbin guraren aikin da aka turasu nan da 3 ga watan Nuwamba. Tun ranar Juma'ar data gabata ne shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya amince da canjawa manyan sojojin wajan aiki. Hakan na zuwane bayan bayyanar rahotanni dake cewa an yi yunkurin yiwa shugaba Tinubu juyin mulki.
Da Duminsa: cikin sojojin da ake zargi da shiryawa shugaba Tinubu Jhuyin mulki, SB Adamu ne aka baiwa aikin Shekye Malam Nuhu Ribadu

Da Duminsa: cikin sojojin da ake zargi da shiryawa shugaba Tinubu Jhuyin mulki, SB Adamu ne aka baiwa aikin Shekye Malam Nuhu Ribadu

Duk Labarai
Rahotanni sun ce a cikin sojojin da aka kama da zargin yunkurin yiwa shugaba Tinubu Jhuyin mulki, SB Adamu ne aka baiwa aikin Shekye babban me baiwa shugaban kasa, shawara kan tsaro, watau Malam Nuhu Ribadu. Shi dai SB Adamu an kaishi aiki ofishin Malam Nuhu Ribadu wanda kuma aka bashi aikin ya kula dashi ya shekye. Kafar Thecable ce ta ruwaito labarin inda tace wata majiyar gidan soji ce ta sanar da ita hakan. Tace ba kamar yanda ake yadawa cewa sauran sojojin da suka shirya juyin mulkin a ofishin me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro suke ba, tace SB Adamu ne kadai a ofishin. Majiyar sojin tace wannan alamace dake nuna cewa masu juyin mulkin sun kama manyan sojoji sosai a gidan sojan.
Da Duminsa: Sanata Natasha Akpoti ta shirya da Sanata Godswill Akpabio har ma ta gayyaceshi…

Da Duminsa: Sanata Natasha Akpoti ta shirya da Sanata Godswill Akpabio har ma ta gayyaceshi…

Duk Labarai
Rahotanni daga majalisar dattijai na cewa akwai alamu masu karfi dake nuni da cewa, an shirya tsakanin Sanata Natasha Akpoti da Sanata Godswill Akpabio. Hakan ya bayyana ne bayan da sanata Natasha Akpoti ta gayyaci Sanata Godswill Akpabio zuwa mazabarta Ihima, Kogi da kaddamar da wani aiki da ta yi. Sanata Godswill Akpabio ne ya karanta takardar gayyatar a zauren majalisar Dattijai ranar Alhamis inda tace tana gayyatarshi da sauran sanatocin zuwa kaddamar da aikin. A baya dai Sanata Natasha Akpoti ta zargi Sanata Godswill Akpabio ta neman ta da lalata wanda lamarin ya jawo zazzafar Muhawara.