Monday, December 15
Shadow

Duk Labarai

Za mu kammala titin jirgin Kaduna zuwa Kano a 2026, in ji gwamnatin tarayya

Za mu kammala titin jirgin Kaduna zuwa Kano a 2026, in ji gwamnatin tarayya

Duk Labarai
Gwamnatin Najeriya ta ce za a kammala aikin titin jirgin ƙasa daga Kaduna zuwa Kano a cikin shekarar 2026 mai zuwa, kamar yadda Ministan Sufuri Sa'idu Ahmed Alkali ya bayyana. Da yake magana yayin wani taron tuntuɓa tsakanin 'yan ƙasa da gwamnati da ke gudana a jihar Kaduna da ke arewacin ƙasar, ministan ya ce lokacin da Shugaba Tinubu ya hau mulki kashi 15 cikin 10 na aikin kawai aka kammala. "Amma zuwa yanzu an kammala kashi 53 cikin 100," in ji shi cikin wata sanarwa da ma'aikatar yaɗa labarai ta fitar a yau Laraba. A 2024 gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ta samu rancen kuɗin da za ta kammala aikin daga wani bankin kasuwanci na ƙasar China, abin da ministan ya jaddada a yau din.
Mu ‘yan Arewa bamu yi dana sanin Zaben Tinubu ba>>Inji Ministan tsare-tsare, Atiku Bagudu

Mu ‘yan Arewa bamu yi dana sanin Zaben Tinubu ba>>Inji Ministan tsare-tsare, Atiku Bagudu

Duk Labarai
Ministan tsare-tsare Atiku Bagudu ya bayyana cewa, 'yan Arewa basu yi dana sanin zaben shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ba. Ya bayyana hakane a wajan taron Arewa House da aka yi na kwanaki biyu tsakanin shuwagabanni da wanda akw Mulka a jihar Kaduna. Ministan yace a lokacin kamin Tinubu ya hau mulki ana ta ciwo bashi ana siyo man fetur daga kasashen waje sannan ana biyan kudin tallafi. Yace amma da Tinubu yazo ya dakatar da duka wannan sannan ya cire tallafin man fetur dana dala. Yace bayan cire tallafin man fetur jihohi sun samu karin kudaden shiga. Dan haka yayi kira ga mutanen Arewa da su daina sauraren masu kokarin hure musu kunne kan cewa wai shugaba Tinubu ya ware Arewa baya mata komai a gwamnatinsa. Yace Gwamnatin Tinubu na tafiya tare da 'yan kasa wajan gudanar da...
Kalli Bidiyo: Anya Rarara ba Asiri yawa A’isha Humaira ta yadda ta aureshi ba?>>Inji Ummi Bamaiyi

Kalli Bidiyo: Anya Rarara ba Asiri yawa A’isha Humaira ta yadda ta aureshi ba?>>Inji Ummi Bamaiyi

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Wata 'yar Tiktok me suna Ummi Bamaiyi ta bayyana ra'ayinta akan Sabbin hotunan Dauda Kahutu Rarara da matarsa, A'isha Humaira. Ta bayyana cewa, ita a tunaninta akwai yiyuwar Rarara Asiri yawa A'isha Humaira ta yadda ta aureshi. Saidai bayan ta gama sukar tata, ta yi fatan itama Rarara ya aureta. https://www.tiktok.com/@ummimamabamaiyisa/video/7532645228377885958?_t=ZS-8ySlDoE1Vbt&_r=1 Hotunan ma'auratan dai sun dauki hankula inda akai ta yaba musu.
Kuma Dai: Kalli Bidiyon yanda Mamakon ruwan sama ya haifar da anbaliyya a Maiduguri

Kuma Dai: Kalli Bidiyon yanda Mamakon ruwan sama ya haifar da anbaliyya a Maiduguri

Duk Labarai
Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno sun tsere daga gidanjensu bayan wata mummunar ambaliya ta auka wa wasu sassan birnin sakamakon ruwan sama mai ƙarfin gaske. Rahotonni daga birnin sun ce lamarin ya shafi unguwannin Damboa road da Moduganari Ngomari da Bulunkutu Abuja da sauransu. An dai wayi gari da mamakon ruwan sama a faɗin birnin, lamarin da ya haifar da ambaliyar. A shekarar da ta gabata ne aka samu wata mummunar ambaliya da ta raba fiye da mutum miliyan guda da muhallansu a birnin na Maiduguri. https://www.tiktok.com/@._cbn/video/7532832958030351672?_t=ZS-8yShc7SinaK&_r=1
David Mark: ADC ba za ta lamunci kakaba ƴan takara ko cin amanar jam’iyya ba

David Mark: ADC ba za ta lamunci kakaba ƴan takara ko cin amanar jam’iyya ba

Duk Labarai
Shugaban rikon kwarya na jam’iyyar ADC, David Mark, ya bayyana cewa jam’iyyar ba za ta lamunci kakaba ‘yan takara , cin amanar jam’iyya ko rashin da’a ba a karkashin jagorancinsa. A yayin taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) na jam’iyyar da aka gudanar a Abuja, David Mark ya sha alwashin jagorantar ADC da gaskiya, adalci da dimokuradiyya. Ya jinjinawa tsohon shugaban jam’iyyar, Ralph Nwosu, bisa jajircewarsa da hidimar da ya yi. Mark ya bayyana cewa jam’iyyar ta ware kashi 35 cikin 100 na mukaman shugabanci ga mata, tare da kudurin bai wa matasa ‘yan kasa da shekara 40 mukamai. Ya kuma bayyana cewa sabon shugabancin jam'iyyar na kasa zai sake duba kundin tsarin mulki da manufofin jam’iyyar domin su dace da bukatun ‘yan kasa. Ya kara da cewa jam’iyyar za ta kafa kwamiti...
Da Duminsa: ‘Yan kasuwar Man fetur sun rage farashi suna sayar da man kasa da farashin Dangote

Da Duminsa: ‘Yan kasuwar Man fetur sun rage farashi suna sayar da man kasa da farashin Dangote

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, 'yan kasuwar Man fetur sun rage farashin man fetur dinsu inda suke sayar dashi a farashi kasa da yanda matatar man Dangote ke sayarwa. Hakan na zuwane kwanaki kadan bayan da Dangoten yayi kira ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya hana shigo da man fetur daga kasashen waje. Jaridar Punchng ta ruwaito cewa, 'yan kasuwar na sayar da man a farashin 860 akan kowace lita yayin da Dangote kuma ke sayarwa akan 865 zuwa 875 akan kowace lita. Shugaban kungiyar 'yan kasuwar man fetur ta IPMAN, Chinedu Ukadike ya tabbatar da rage farashin inda yace hakan na nuna kyawun kasuwa. Yace yana kira ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da kada ya saurari kiran da Dangote ke yi na cewa ya hada shigo da man fetur din daga kasashen waje.
Shugaba Tinubu ya nada lumode Samuel Adeyemi a matsayin sabon shugaban Hukumar kwana-kwana

Shugaba Tinubu ya nada lumode Samuel Adeyemi a matsayin sabon shugaban Hukumar kwana-kwana

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya nada lumode Samuel Adeyemi a matsayin sabon shugaban hukumar kwana-kwana masu kashe Gobara ta kasa. Lumode zai fara aiki ne ranar August 14, 2025 a matsayin sabon shugaban hukumar. Hakan na zuwane yayin da shugaban hukumar na yanzu, Engr. Abdulganiyu Jaji ke shirin zauka ya ajiye aiki bayan kaiwa shekarun ritaya watau shekaru 60.
Shugaba Tinubu na nuna tausai sosai a mulkinsa>>Inji Kashim Shettima

Shugaba Tinubu na nuna tausai sosai a mulkinsa>>Inji Kashim Shettima

Duk Labarai
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana cewa, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu na nuna tausai sosai a mulkinsa. Ya bayyana hakane a wajan taron da aka gudanar a Arewa House dake Jihar Kaduna. Kashim Shettima wanda me baiwa shugaban kasa shawara kan ayyuka na musamman, Dr Aliyu Modibbo Umar, ya wakilta a wajan taron da aka yi na kwanki biyu, ya bayyana cewa shugaban kasar ya kawo ayyukan ci gaba sosai. Ya bayar da misali a bangaren Ilimi inda yace shugaba Tinubu ya samarwa 'ya'yan talakawa damar karatu inda aka rika bayar sa bashin karatu. Yace daga baya da aka ga cewa, Guarantor da kuma kayyade yawan samun mutum kamin a bashi bashin zai zo da matsala sai aka dakatar da hakan aka rika baiwa daliban bashin kai tsaye.
Kalli Sabon Bidiyo: A karshe dai Ummi Nuhu ta fito da kanta ta fadi kuskuren da ta yi da ya jefata a wahalar rayuwa

Kalli Sabon Bidiyo: A karshe dai Ummi Nuhu ta fito da kanta ta fadi kuskuren da ta yi da ya jefata a wahalar rayuwa

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{"transform":1,"square_fit":1},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":true,"containsFTESticker":false} Tauraruwar fina-finan Hausa, Ummi Nuhu ta fito ta bayyana dalilin da yasa ta fada wahalar rayuwar da aka ganta a ciki ake ta cece-kuce bayan hirar da Hadiza Gabon ta yi da ita. Ummi Nuhu a sabuwar hirar ta da Hadiza Gaon ta bayyana cewa, Babban Kuskuren da ta aikata shine a lokacin data samu dama, bata yiwa kanta tanadin komai ba, jin dadin rayuwa akai ta yi. Tace amma tana fatan jarumai mata musamman masu tasowa a yanzu zasu dauki darasi daga Ra...