Friday, February 27
Shadow

Duk Labarai

Najeriya ta samu tsaro sosai a zamanin mulkin Tinubu >>Inji me magana da yawun shugaban kasa, Daniel Bwala

Najeriya ta samu tsaro sosai a zamanin mulkin Tinubu >>Inji me magana da yawun shugaban kasa, Daniel Bwala

Duk Labarai
Me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar sadarwa, Daniel Bwala ya bayyana cewa, An samu tsaro sosai a Najeriya a mulkin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV. Daniel Bwala yace kamin hawan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu mulki ana garkuwa da mutane yanda aka ga dama har cikin Abuja da rana tsaka ana garkuwa da mutane amma wannan duk ya kau. Yace an fasa gidajen yari da dama a mulkin baya amma a zamanin Tinubu lamura sun gyaru
Kalli Bidiyon: A karshe dai an yi zama da Malam Lawal Triumph kuma duk ya kawo litattafan da suka fadi kalaman da yayi

Kalli Bidiyon: A karshe dai an yi zama da Malam Lawal Triumph kuma duk ya kawo litattafan da suka fadi kalaman da yayi

Duk Labarai
A zaman da kwamitin Shura suka yi da malam Lawal Triumph bayan zargin da aka masa na cewa yayi kalaman batancin ga Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam). Malamin ya kawo litattafan da ya dauko kalaman da yayi. Saidai duk da haka ya bayar da hakuri ga wadanda kalaman basu musu dadi ba. https://www.tiktok.com/@habibou.adamou..227/video/7560773874778901816?_t=ZS-90Wa91oEQJl&_r=1 https://www.tiktok.com/@habibou.adamou..227/video/7560773548990565643?_t=ZS-90WaGecFDrU&_r=1 https://www.tiktok.com/@habibou.adamou..227/video/7560760486921391371?_t=ZS-90WaKIYg7l2&_r=1
Kasar Burkina Faso ta samu kudin Shiga Dala Biliyan $18 ta hanyar sayar da Gwal tun bayan da Ibrahim Traore ya zama shugaban kasar

Kasar Burkina Faso ta samu kudin Shiga Dala Biliyan $18 ta hanyar sayar da Gwal tun bayan da Ibrahim Traore ya zama shugaban kasar

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, kasar Burkina Faso ta samu kudin shiga da suka kai Dala Biliyan $18 tun bayan da Ibrahim Traore ya zama shugaban kasa a shekarar 2022. Bayan da ya zama shugaban kasa, Ibrahim Traore ya kwace kamfanonin hakar ma'adanai na turawa inda ya mayar dasu mallakar kasar ta Burkina Faso. Hakan ya taimaka sosai wajan kara yawan kudin shigar da kasar ke samu daga Gwal. A baya, kamin ya zama shugaban kasa, Kasar ta Burkina Faso na samun kudin shiga Dala Biliyan $1 ne kacal daga sayar da Gwal. A shakerar 2024, kasar Burkina Faso ta fitar da Ton 60 na Gwal.
Dan Shugaban kasa, Seyi Tinubu ya cika shekaru 40 da haihuwa, za’a raba Baibul guda Miliyan daya dan murna

Dan Shugaban kasa, Seyi Tinubu ya cika shekaru 40 da haihuwa, za’a raba Baibul guda Miliyan daya dan murna

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, dan shugaban kasa, Seyi Tinubu ya cika shekaru 40 da haihuwa. Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya taya dan nasa murna. A wani mataki na nuna murna da wannan rana, An shirya raba Baibul har guda Miliyan daya a fadin Najeriya. Hon. Belusochukwu Enwere ne ya bayyana haka a cibiyar kiristanci ta kasa dake Abuja ranar Lahadi. An yiwa Seyi Tinubu addu'a a coci guda 40 a fadin Najeriya saboda murnar wannan rana.
Kalli Bidiyon: Bana karbar kasa da Naira Miliyan daya kamin in fito a Fim>>Hadiza Gabon

Kalli Bidiyon: Bana karbar kasa da Naira Miliyan daya kamin in fito a Fim>>Hadiza Gabon

Duk Labarai
Tauraruwar fina-finan Hausa, Hadiza Gabon ta bayyana cewa, bata fitowa a Fim sai an biyata kudi sama da Naira Miliyan 1. Ta bayyana hakane a wata hira da ta yi da abokiyar aikinta, Fati Washa inda take cewa an saba biyanta Naira Miliyan 1 kudin aiki shiyasa a yanzu ba zata yadda a biya kasa da hakan ba. https://www.tiktok.com/@gabon.talk.show1/video/7559286787902885138?_t=ZS-90WBUEmKC4v&_r=1
‘Yar Najeriya ta yi kokarin shiga Kundin Tarihin Duniya ta hanyar yiwa mutane 145 kwalliya a cikin kwana daya

‘Yar Najeriya ta yi kokarin shiga Kundin Tarihin Duniya ta hanyar yiwa mutane 145 kwalliya a cikin kwana daya

Duk Labarai
'Yar Najeriya, Tsohuwar Tauraruwar BBNAIJA, Natacha Akide wadda aka fi sani da Tacha ta yiwa mutane 145 kwalliya a cikin awanni 24 dan ta shiga kundin tarihin Duniya. Ta aikata hakanne a Legas inda aka dauke ta Bidiyon yayin da take aikata hakan. Duk da cewa an samu matsalar daukewar wuta amma tasha ta kammala wannan abu nata Lafiya.
Tabbas Ministan Kudi bashi da lafiya, kuma ta dan yi tsanani, amma ba shanyewar rabin jiki bace>>Fadar Shugaban kasa

Tabbas Ministan Kudi bashi da lafiya, kuma ta dan yi tsanani, amma ba shanyewar rabin jiki bace>>Fadar Shugaban kasa

Duk Labarai
Fadar shugaban kasa, ta tabbatar da cewa, ministan Kudi, Wale Edun Bashi da lafiya Wata majiya daga fadar ta tabbatar wa da gidan jaridar Punchng hakan inda tace rashin lafiyar ta matsa masa. Saidai tace ba Shanyewar rabin jiki bane sannan ba'a fitar dashi zuwa kasar waje ba, sannan shugaban kasa Bola Tinubu bai fara neman wanda zai maye gurbinsa ba. Rahotanni sun ce Likitocin Najeriya ne ke kula da Ministan amma idan lamarin yayi kamari za'a iya fita dashi kasar waje.
Kalli Bidiyo: Matashi me suna Abdullahi, wada yace shi dan Izala ne, ya bar Musulunci inda ya koma Kirista

Kalli Bidiyo: Matashi me suna Abdullahi, wada yace shi dan Izala ne, ya bar Musulunci inda ya koma Kirista

Duk Labarai
Wani matashi daga jihar Katsina wanda yace ya fito ne daga garin Radda na jihar katsina kuma da uwane a wajan gwamnan Katsina watau Dikko Raddah ya koma Kirista. Matashin wanda yace sunansa Abdullahi yace ya koma Kirista ne a Makaranta bayan da ya fara karanta Baibul ya kuma fahimceshi. Matashin yace da ya gayawa mahaifiyarsa ta dauki abin da wasa amma daga baya da aka ga da gaske yake, an kamashi an daure tsawon watanni indaa yace amma duk da haka bai koma musulmi ba. https://www.tiktok.com/@chizo_1_germany/video/7559944553420295446?_t=ZS-90VjSzhe8RM&_r=1