Monday, December 15
Shadow

Duk Labarai

Kalli Bidiyon yanda ‘yan uwan wata mata suka je suka rama mata dukan da mijinta ya mata

Kalli Bidiyon yanda ‘yan uwan wata mata suka je suka rama mata dukan da mijinta ya mata

Duk Labarai
Wannan Bidiyon ya yadu sosai a kafafen sada zumunta inda aka ga 'yan uwan wata mata sun je har gida suka samu mijinta suka masa dukan tsiya. Rahoton yace mijin ya daki matar ne inda suma 'yan uwanta suka hada kai suka je suka sameshi suka zaneshi https://twitter.com/Lminkaeel/status/1947166276608000189?t=K30ERs65ecyGrsPzpzmvOg&s=19 Wasu dai sun ce sun yi daidai inda wasu ke cewa basu kyauta ba.
Kalli Bidiyo: Yanda wani mutum da ya saci kaji da da awaki ya koma yana kukan awaki da charar kaji, da kanshi ya kai kanshi ofishin ‘yansanda inda yace a roki me awakin ya maidoshi daidai

Kalli Bidiyo: Yanda wani mutum da ya saci kaji da da awaki ya koma yana kukan awaki da charar kaji, da kanshi ya kai kanshi ofishin ‘yansanda inda yace a roki me awakin ya maidoshi daidai

Duk Labarai
Wani mutum dake aiki a gidan gona, ya yiwa me gidansa satar awaki biyu da kaji biyu. Saidai abin mamaki shine ya tsere garin Mombasa sai ya rika kukan awaki da carar kaji. Da yawa dai sun yi amannar cewa, Asiri me gonar ya masa. Mutumin dai da kanshi ya kai kanshi ofishin 'yansanda. https://www.youtube.com/watch?v=kdvFEmVb6aA?si=1AkrGCZBURMsd5wS Sunan wanda yayi satar Baraka Joseph kuma dan ahekaru 16 ne. https://twitter.com/chude__/status/1946863679988781152?t=SOi_q_RHhieE790xz-jQ7A&s=19 Abin ya baiwa mutane mamaki sosai.

Za a yi ruwan sama da iska mai ƙarfi a sassan Najeriya>>Inji Hukumar kula da yanayi ta Najeriya NiMET

Duk Labarai
Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMET) ta fitar da hasashen yanayi na kwana uku, daga Litinin 21 zuwa Laraba 23 ga Yulin 2025, inda ta bayyana cewa za a samu ruwan sama da iska mai ƙarfi a sassa daban-daban na ƙasar. A kan haka NiMet ta shawarci al'umma da su yi taka-tsantsan kan yiwuwar samun ambaliya da kuma ɓarna da iska mai ƙarfi ke iya haddasawa. A cewar sanarwar da hukumar ta wallafa a shafin sada zumunta na X, jihohin Arewa da na Kudu da kuma yankin tsakiya, duk za su fuskanci iska mai ƙarfi haɗe da ruwan sama. Hasashen ya nuna cewa a ranar Litinin da safe, za a samu ruwan sama da iska a jihohin Taraba da Adamawa da Kebbi da Borno da Yobe da Gombe da Bauchi da Sokoto da Kaduna. Ya kuma nuna cewa yankin tsakiyar ƙasar kamar Abuja da Naija da Plateau da Nasarawa d...
Mun Dauki Tsawon Shekaru Talatin Muna Aiki Ba Dare Ba Rana, Amma Yanzu Hakkiñmu Ya Gagara Fita Da Za Mu Ciyar Da Iyalanmu, Cewar Tsoffin ‘Yan Sandan Nijeriya Dake Zañgà-Zañgà A Abuja

Mun Dauki Tsawon Shekaru Talatin Muna Aiki Ba Dare Ba Rana, Amma Yanzu Hakkiñmu Ya Gagara Fita Da Za Mu Ciyar Da Iyalanmu, Cewar Tsoffin ‘Yan Sandan Nijeriya Dake Zañgà-Zañgà A Abuja

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Mun Dauki Tsawon Shekaru Talatin Muna Aiki Ba Dare Ba Rana, Amma Yanzu Hakkiñmu Ya Gagara Fita Da Za Mu Ciyar Da Iyalanmu, Cewar Tsoffin 'Yan Sandan Nijeriya Dake Zañgà-Zañgà A Abuja
DA ƊUMIƊUMINSA: Ɗan Gidan IBB Ya Ki Karɓar Sabon Muƙamin Shugaban Bankin Manoma Da Tinubu Ya Ba Shi

DA ƊUMIƊUMINSA: Ɗan Gidan IBB Ya Ki Karɓar Sabon Muƙamin Shugaban Bankin Manoma Da Tinubu Ya Ba Shi

Duk Labarai
Daga Muhammad Kwairi Waziri Mohammed Babangida, ɗan tsohon shugaban ƙasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), ya yi watsi da nadin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya masa a matsayin Shugaban Bankin Manoma na Najeriya (BOA). Majiyoyi sun tabbatar da cewa Mohammed ya bayyana rashin amincewarsa da muƙamin, yana mai cewa wasu dalilai na sirri da kuma tsare-tsaren kansa ne suka sa ya yanke shawarar kin karɓa, duk da girmansa. Nadin nasa ya kasance cikin jerin sabbin nade-naden da shugaban ƙasa ke yi domin farfaɗo da harkokin noma da bunkasa rayuwar manoma a ƙasar nan. Sai dai wannan mataki da Mohammed ya ɗauka na watsi da mukamin ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumunta da cikin ‘yan siyasa. Har yanzu babu wata sanarwa kai tsaye daga fadar shugaban ƙasa ko daga bakin Mohammed Baban...
Kotu ta hana tsohon Gwamnan jihar Kogi, Yahya Bello Fasfo dinsa inda yace yana son ya je kasar waje a duba lafiyarsa, Saidai kotun tace bai bayar da hujjar cewa Likitocin Najeriya ba zasu iya magance rashin lafiyar tashi ba

Kotu ta hana tsohon Gwamnan jihar Kogi, Yahya Bello Fasfo dinsa inda yace yana son ya je kasar waje a duba lafiyarsa, Saidai kotun tace bai bayar da hujjar cewa Likitocin Najeriya ba zasu iya magance rashin lafiyar tashi ba

Duk Labarai
Babbar Kotun tarayya dake Maitama Abuja ta hana tsohon gwamnan jihar Kogi Yahya Bello Fasfo dinsa dan ya je kasar waje neman magani. Mai shari'a Justice Emeka Nwite ya bayyana wannan hukunci. Yace takardun da Tsohon gwamnan ya gabatar na neman ya tafi kasar ingila basu da tambarin sarki wanda kotun tace basu da wani amfani a wajanta. Dan haka tace kuma rashin lafiyar ta tsohon gwamnan ba ta yi tsananin da za'a ce sai an fitar dashi kasar waje ba. Ana zargin tsohon gwamnan da dan uwansa, Ali Bello, Dauda Suleiman da Abdulsalam Hudu wajan satar Naira N80, 246,470, 088.88.