Goodluck Jonathan na son a sauya yadda ake zaɓen shugaban INEC
Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya yi kira da a samar da sabon tsarin zaɓen shugaban hukumar zabe ta ƙasa (INEC), inda ya ba da shawarar kafa wani tsarin tantancewa da zaɓe mai zaman kansa don ƙara wa hukumar sahihanci kafin zaɓen gaba na 2027.
Jonathan ya bayyana wannan ra’ayi ne a ranar Laraba a Abuja, a yayin gabatar da shirin ƙasa na gyaran harkokin zaɓe, wanda Makarantar Nazarin Zamantakewa da Siyasa ta Abuja ta shirya.
Kiran ya zo ne a wani lokaci na siyasa mai ɗaukar hankali, yayin da wa’adin shugaban INEC na yanzu, Prof. Mahmood Yakubu, ke ƙarewa a watan Oktoba na wannan shekara.
Yakubu, wanda ya jagoranci zaɓukan 2019 da 2023, ya riga ya yi wa’adin aiki biyu, kuma zaɓen wanda zai gaje shi na janyo ƙarin hasashe a al’umma.
Masana na ganin cewa wanda zai zam...








