Monday, March 30
Shadow

Duk Labarai

Kuma Dai: Gwamnatin Tarayya zata sae ciwo bashin Dala $1.75bn

Kuma Dai: Gwamnatin Tarayya zata sae ciwo bashin Dala $1.75bn

Duk Labarai
A yayin da Gwamnatin tarayya tace kudin shigarta daga bangarorin da bana danyen ma fetur ba sun karu da kaso 40 cikin 100, tana kuma kokarin kara ciwo Bashi. Gwamnatin dai tace duk da wannan kari data samu na kudin shiga, har yanzu tana fama da karancin kudin gudanar da ayyuka. A baya bayannan, 'yan kwangila sun gudanar da zanga-zanga inda suke neman a biyansu kudin ayyukan da suka yi a shekarar 2024 da suka kai Naira Tiriliyan 4. Domin cike gibin wannan karancin kudin, Gwamnatin tarayya na shirin ciwo bashin Dala Biliyan $1.75bn dan gudanar da ayyuka. Saidai hakan na zuwane kwanaki kadan bayan da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa sun samu duka kudin shigar da suke bukata dan gudanar da ayyuka a shekarar 2025, ba zasu kara ciwo bashi ba a wannan shekarar.
Shugaba Tinubu yayi ikirarin cewa a lokacin da ya hau mulki Ana sayen dalar Amurka akan Naira 1,900 Saidai dai da yawa sun musanta wannan ikirarin na shugaban kasar

Shugaba Tinubu yayi ikirarin cewa a lokacin da ya hau mulki Ana sayen dalar Amurka akan Naira 1,900 Saidai dai da yawa sun musanta wannan ikirarin na shugaban kasar

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yi ikirarin cewa a lokacin da ya hau mulki a watan Mayu na shekarar 2023 ana sayen dalar Amurka ne akan Naira 1,900. Saidai da yawa sun ce wannan ikirari na shugaban kasa ba gaskiya bane. Daya daga cikin wanda suka karyata maganar shugaban kasar, Akwai Rufai Oseni me gabatar da shirye-shirye na tashar Arise TV inda yace wannan magana ba gaskiya bane. https://twitter.com/ruffydfire/status/1963602411290845572?t=T-VE7gKTolinPRxqUfSWkA&s=19 Yace dala ta tashine saboda tsare-tsaren tattalin arziki na shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Babu Abinda zai hana Tinubu cin zabe a 2027>>Inji Dan majalisa Abdulmumin Jibrin

Babu Abinda zai hana Tinubu cin zabe a 2027>>Inji Dan majalisa Abdulmumin Jibrin

Duk Labarai
Dan majalisar tarayya, Abdulmumin Jibrin daga jihar Kano, ya bayyana cewa, babu abinda zai hana shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu cin zabe a shekarar 2027. Ya bayyana hakane a ganawar da aka yi dashi a Channels TV. Ya kara da cewa, akwai fahimtar juna da kyakkyawar alaka a tsakaninsa da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu duk da cewa basa jam'iyya daya. A baya dai, Abdulmumin Jibrin ya jagoranci yakin neman zaben shugaban kasa Bola Tinubu ya.
Gwamnatin jihar Naija ta Haramta yin wa’azi inda tace duk wani me wa’azi sai ya nemi lasisi

Gwamnatin jihar Naija ta Haramta yin wa’azi inda tace duk wani me wa’azi sai ya nemi lasisi

Duk Labarai
Gwamnatin Jihar Neja Ta Haramta Wa’azi Ba Tare da Lasisi Ba: Gwamnatin Jihar Neja ta sanar da haramcin yin kowace irin wa’azi a fadin jihar tare da umartar cewa duk wanda ke son yin wa’azi sai ya mallaki lasisi daga hukumar kula da harkokin addini ta jihar. Daraktan Hukumar Harkokin Addini ta Jihar Neja, Malam Umar Farooq, ya tabbatar da hakan a wata hira ta wayar tarho da jaridar Punch a ranar Alhamis. Ya bayyana cewa duk wani mai wa’azi ya kamata ya nemi lasisi daga nan zuwa cikin watanni biyu masu zuwa. “Gaskiya ne, gwamnati ta haramta yin wa’azi ba tare da izini ba. Duk mai wa’azi dole ne ya mallaki lasisi tsakanin yanzu da watanni biyu masu zuwa. Abin da ake buƙata shi ne, su zo ofishinmu, su karɓi fom, su cike, sannan su fuskanci kwamiti da zai tantance su kafin a basu damar...
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya bayar da labarin irin cin amanar da aka masa a shekarar 2015 da ya nemi sake cin zabe a karo na 2

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya bayar da labarin irin cin amanar da aka masa a shekarar 2015 da ya nemi sake cin zabe a karo na 2

Duk Labarai
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya bayar da labarin yanda ta kaya a shekarar 2015 da ya nemi sake cin zabe a karo na biyu. Ya bayyana hakane a yayin da ya je bikin cikar Chief Mike Aiyegbeni Oghiadomhe shekaru 50 da haihuwa. Yace yawanci 'yan siyasa sun yaudareshi ne a 2015, yace siyasar Najeriya akwai cin amana sosai a cikinta, yace da wuya ka samu wanda zai tsaya kan magana daya ta gaskiya. Yace amma Chief Mike Aiyegbeni Oghiadomhe mutum ne me nagarta wanda yana sonshi da gaske.
Karanta jadawalin shuwagabannin kasashen Duniya mafiya Arziki

Karanta jadawalin shuwagabannin kasashen Duniya mafiya Arziki

Duk Labarai
Wannan Jadawalin shuwagabannin kasashen Duniya ne mafiya Arziki. Vladimir Putin (Russia) – $258 Bn Donald Trump (United States) – $6.1 Bn Kim Jong Un (North Korea) – $5 Bn Xi Jinping (China) – $1.5 Bn Teodoro Obiang Nguema Mbasogo (Equatorial Guinea) – $940 Mn Ilham Aliyev (Azerbaijan) – $500 Mn Recep Tayyip Erdoğan (Turkey) – $500 Mn Paul Kagame (Rwanda) – $500 Mn Cyril Ramaphosa (South Africa) – $450 Mn William Ruto (Kenya) – $400 Mn
Bayan da wannan hoton nashi ya jawo cece-kuce Gfresh yayi Bidiyo ba Filta inda yace nasu son ganinshi ba Filta gashi

Bayan da wannan hoton nashi ya jawo cece-kuce Gfresh yayi Bidiyo ba Filta inda yace nasu son ganinshi ba Filta gashi

Duk Labarai
Tauraron Tiktok, Gfresh Al-amin yayi Bidiyo ba Filta inda yace masu son ganinshi ba Filta to gashi yayi Bidiyo ba Filta https://www.tiktok.com/@gfreshfanpage/video/7545502116895411463?_t=ZS-8zSMjK3vyfA&_r=1 Hakan na zuwane bayan hotonsa da ya bayyana inda aka ganshi a wajan biki an daukeshu hoto yayi wani iri duk tabo a fuskar.