Kalli Bidiyon: Na taba aure sau daya amma yanzu bani da aure amma ina fatan in yi aure in haihu>>Inji Ladidi
Tauraruwar fina-finan Hausa, Ladidi tubeless ta bayyana cewa, ta taba aure a baya amma auren ya mutu.
Tace bata taba haihuwa ba amma tana fatan nan gaba ta sake yin aure ta haihu.
Ladidi Tubeless ta bayyana hakane a hirar da BBCHausa suka yi da ita.
https://www.tiktok.com/@ladidi_tubbles/video/7535082673556032824?_t=ZS-8ydI3fmSNjF&_r=1








