Friday, April 3
Shadow

Duk Labarai

Kalli Bidiyo yanda Hadiza Gabon Ta baiwa Abokin Aikinta, Ango Jamilu Adamu Kochila kyautar Naira Miliyan 2 ranar aurensa

Kalli Bidiyo yanda Hadiza Gabon Ta baiwa Abokin Aikinta, Ango Jamilu Adamu Kochila kyautar Naira Miliyan 2 ranar aurensa

Duk Labarai
Tauraruwar fina-finan Hausa, Hadiza Gabon ta baiwa Abokin aikinta, Jarumi, Jamilu Adamu Kochila kyautar Naira Miliyan 2 a wajan bikinsa. Bidiyon hakan ya yadu sosai a kafafen sada zumunta inda aka ga irin gudummawar da ake baiwa Jarumin. https://www.tiktok.com/@agg_multimedia_services/video/7534124829511798072?_t=ZS-8yYqv59xDEX&_r=1
Kalli Bidiyo: Matashi daga Arewa me karatun Qur’ani ya zarta Mawaki Davido mabiya a Tiktok

Kalli Bidiyo: Matashi daga Arewa me karatun Qur’ani ya zarta Mawaki Davido mabiya a Tiktok

Duk Labarai
Matashi daga Arewa me amfani da sunan Youngalajerh8 a Tiktok dake Karanta Qur'ani ya samu mabiya sama da shahararren mawakin Najeriya, Davido. Younalajerh8 ya kai mabiya Miliyan 9 a Yayin da shi kuma Davido ke da mabiya Miliyan 8.8. Hakan yasa mutane da yawa fadin cewa ba sai mutum yayi abin banza ba kamin ya daukaka a Tiktok. https://www.tiktok.com/@youngalajerh8/video/7530169409021758727?_t=ZS-8yYO9wzk9Ef&_r=1
Kalli Bidiyo:Malaman Izala na ta yabon Sheikh Maqari saboda kalaman da yayi akan Mafarki

Kalli Bidiyo:Malaman Izala na ta yabon Sheikh Maqari saboda kalaman da yayi akan Mafarki

Duk Labarai
Malaman Izala da dama na ta yabon Sheikh Ibrahim Maqari saboda kalaman da yayi akan Mafarki. Maqari ya kore samar da ayyukan addini daga mafarki. Wannan ne yasa wasu Malam Izala suka rika murna da jin wadannan kalamai tare da fadar cewa, Maqari ya kore ayyukan Dariqa. https://www.tiktok.com/@daawah.tv/video/7532276550721490232?_t=ZS-8yYMizacDE8&_r=1 https://www.tiktok.com/@daawah.tv/video/7533259051212246328?_t=ZS-8yYMXHElbzl&_r=1
Gyaran filayen jirgin sama: Hadimin Ganduje Salihu Tanko-Yakasai ya soki Tinubu, ya ce “Emi Lokan” ta zama “Lagos Lokan”

Gyaran filayen jirgin sama: Hadimin Ganduje Salihu Tanko-Yakasai ya soki Tinubu, ya ce “Emi Lokan” ta zama “Lagos Lokan”

Duk Labarai
Daya daga cikin hadiman tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, Salihu Tanko Yakasai, ya bayyana damuwarsa kan salon shugabancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa ana fifita yankin Legas da Kudu maso Yamma fiye da sauran sassan kasar. A wani rubutu na ra'ayi da ya wallafa a yau Asabar, Yakasai ya ce ko da ya ke ya fahimci taken “Emi Lokan” da Shugaba Tinubu ya yi amfani da shi a lokacin kamfen din sa, yana yawan tambayar ko shugaban Najeriya ne gaba ɗaya ko kuma na Legas kawai. “Ana nuna wariya idan aka kwatanta da Legas, ba kawai a fannin ayyuka ba har ma da na mukamai,” in ji Yakasai. “Zai yi kyau mu ce ‘Emi Lokan’ ta rikide zuwa ‘Lagos Lokan’.” Yakasai ya bayyana damuwa kan abin da Najeriya za ta fuskanta idan wannan tsarin da ake gani a yanzu ya ci gaba har z...
Ana cece-kuce tsakanin Gwamnan jihar Naija da Gwamnatin tarayya kan dakatar da gidan Rediyo

Ana cece-kuce tsakanin Gwamnan jihar Naija da Gwamnatin tarayya kan dakatar da gidan Rediyo

Duk Labarai
Ministan yaɗa labarai da wayar da kan al'umma na Najeriya, Muhammad Idris Malagi ya buƙaci kowane ɓangare ya mayar da kubensa kan batun rufe gidan rediyon Badegi FM da ke birnin Minna a jihar Neja. Ministan ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Rabiu Ibrahim ya fitar, inda a ciki ya ce hukumar kafafen watsa labarai ta Najeriya wato NBC na da hanyoyin shiga tsakani idan aka samu irin wannan matsalar. Rahotanni sun nuna cewa Gwamnan jihar Neja, Umaru Bago ya bayar da umarnin rufe gidan rediyon ne a lokacin taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC na jihar a ranar 1 ga watan Agusta. Gwamnan ya zargi gidan rediyon ya karya dokokin watsa labarai, da kuma tunzura mutane a kan gwamnatin jihar. "Duk da cewa mun fahimci abin da gwamnatin ke zargi, ma'aikatar wa...
Tilas Tinubu ya sa baki kan ɓacewar Dadiyata – Amnesty International

Tilas Tinubu ya sa baki kan ɓacewar Dadiyata – Amnesty International

Duk Labarai
Ƙungiyar Amnesty International ta yi Allah-wadai da sakacin da ta ce gwamnatin Najeriya na yi kan ɓacewar matashin ɗan gwagwarmaya, Abubakar Idris Dadiyata. Amnesty International ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ta raba wa manema labarai, inda ta ce tana mamakin yadda aka yi shekara shida ba tare da sanin halin da yake ciki ba. Dadiyata ya ɓace ne a ranar 2 ga watan Agustan shekarar 2019, bayan wasu mutane ɗauke da makamai sun kutsa gidansa da ke unguwar Barnawa a Kaduna jim kaɗan bayan ya koma, suka suka tafi da shi. "Tun lokacin ne iyalansa suke ta da jiran komawarsa, amma har yanzu da ya cika shekara shida babu bayani." Shugaban ƙungiyar a Najeriya, Isa Sanusi ya ce shi kansa ya san Dadiyata a matsayin jajirtacce mai girmama na gaba. "Mutane da dama, ciki har da...