Idan da gaske kake game da daina Shigo da abubuwa daga kasashen waje a rika Amfani da wanda aka yi a Najeriya, ka ajiye motocin Alfarma da kake hawa ka koma Amfani da motocin Innoson da ake kerawa a jihar Anambra>>Atiku ya gayawa Tinubu
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya cewa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu idan da gaske yake maganar daina amfani da abubuwan da aka kera a kasashen waje to ya daina amfani da motocin Alfarmar da yake hawa ya koma Amfani da motar Innoson da ake kerawa a jihar Anambra.
Ya bayyana hakanne bayan da shugaba Tinubu ya baiwa ma'aikatun gwamnati umarnin su daina shigo da kayan da ake yin irin su a Najeriya.
Saidai Atiku yace wannan duk yaudara ce wadda 'yan Najeriya sun saba ji, yace idan Gwamnatin da gaske take, ta fara daga kan kanta.
Yace kamata yayi shugaba Tinubu ya fara da kanshi, ya daina amfani da motocin Alfarma da yake amfani dasu ya koma amfani da motocin Innoson ko makamantansu da ake kerawa a Najeriya.
Yace ministocin Buharin ma haka ya kamata su ...








