Ana hasashen aƙalla shaguna sama da 100 sun ƙone ƙurmus ya yin da wata gobara ta tashi da tsakar dare a kasuwar Terminus da ke birnin Jos na jihar Filato
Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un.
An samu mummunar gobara da ta laƙume shagunan mutane da dama a babbar kasuwar Terminus a wani layi da ake ƙira da “Parlon Buhari” da ke Jos fadar gwamnatin jihar Filato a daren jiya.
Ana hasashen aƙalla shaguna sama da 100 sun ƙone ƙurmus a gobarar.








