Ji bayani dalla-dalla Abin da ya sa na fice daga PDP – Atiku
"
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP.
A wata sanarwa da ya fitar mai kwanan watan ranar 14 ga watan Yulin 2025, Atiku Abubakar ya ce "ina sanar da jama'a ficewata daga jam'iyyar PDP ba tare da ɓata lokaci ba."
"Ina son yin amfani da wannan damar na bayyana godiyata ga jam'iyyar ta PDP bisa irin damarmakin da ta ba ni: Na yi mataimakin shugaban ƙasa karo biyu a jam'iyyar sannan na yi takarar shugaban ƙsa karo biyu a PDP. A matsayina na ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa jam'iyyar ta PDP, saboda haka akwai sosa rai ƙwarai dangane da ɗaukar wannan hukunci." In ji Atiku.
Dangane kuma da dalilin da ya sa tsohon mataimakin shugaban na Najeriya ya bar jam'iyyar a wannan lokaci sanarwar ta ce:
Dole ne na raba gari da jam'i...








