Friday, December 19
Shadow

Duk Labarai

Ji Niqaf Yazama Silar Mutuwar Aure na Sati Daya Da Daura mana Auren nida mijina -Surayya Aminu Dan maliki

Ji Niqaf Yazama Silar Mutuwar Aure na Sati Daya Da Daura mana Auren nida mijina -Surayya Aminu Dan maliki

Duk Labarai
NiQaf Yazama Silar Mutuwar Aure na Sati Daya Da Daura mana Auren nida mijina -Surayya Aminu Dan maliki. Wanda Aka daura mana aure Dashi muna son junan mu, tun kafin bikin mu yake cewa Shi bayason ina sanya NiQaf, nikuma na fada masa irin Tarbiyyar Gidan mu kenan,baban mu baya barin kowa ta fita sai da NiQaf, Bai tashi fara nuna ɓacin Ransa akan Niqaf din sosai ba sai Ranar da yace in shirya muje shopping, aiko na dakko NiQaf shi kuma yace bazan saba, ni kuma nace sai dai in fasa fitar, daga karshe yace in zaba ko Umurnin sa ko in koma gida, bance masa komai ba dai,karshe yace ya sakeni saki Daya.
Kotu ta yi watsi da buƙatar Emefiele kan dawo masa da gidajen da EFCC ta ƙwace

Kotu ta yi watsi da buƙatar Emefiele kan dawo masa da gidajen da EFCC ta ƙwace

Duk Labarai
Wata babbar kotun tarayya a Najeriya ta yi watsi da buƙatar tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele, ta neman a dawo masa da rukunin gidajen da gwamnati ta ƙwace. A ranar 2 ga watan Disamba ne hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa ta samu amincewar kotu domin ƙwace unguwa guda mallakar Mista Emefiele da ke Abuja babban birnin ƙasar. Unguwar da ke yankin Lokogoma ta ƙunshi gidaje 753. Tsohon gwamnan ya nemi kotun ta ƙara masa lokaci domin gabatar da buƙatar neman jingine umarnin da ta bayar na ƙwace rukunin gidajen a watan Disamban 2024. Ya yi iƙirarin cewa bai san lokacin da kotun ta yanke hukuncin ƙwace gidajen ba, sannan ya zargi EFCC da wallafa sanarwar neman mamallakin gidajen a wani "ɓoyayyen sashe na shafin jarida ta yadda zai yi wahala ya iya r...
Tashin bàm ya kàshè mutum 26 a jihar Borno

Tashin bàm ya kàshè mutum 26 a jihar Borno

Duk Labarai
Rahotanni daga arewa maso gabashin Najeriya na cewa aƙalla mutum 26 ne suka rasu ranar Litinin sakamakon tashin wani bam da motar da suke ciki ta taka a kan hanyar da ke tsakanin garin Rann zuwa Gmaboru Ngala. Kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito cewa mutanen da abin ya rutsa da su sun haɗa da maza 16 da mata huɗu da ƙananan yara guda shida. Bam ɗin da ake zaton ƙungiyar Bòkò Haram ce ta dasa binne shi, ya kuma jikkata aƙalla mutum da dama waɗanda suke asibiti domin samun kulawa. Duk da cewa al'ummar yankin sun ɗora laifin kan ƙungiyar Bòkò Haram amma har kawo yanzu hukumomin tsaro ba su ce uffan ba.
Na kusa da Shugaba Tinubu kakkangeshi suke, basa bari a je kusa dashi ballantana a gaya masa halin da mutane ke ciki, watanni na 18 ina aiki a fadar shugaban kasa amma sau 3 muka taba haduwa da shugaban kasa shima a masallaci ne>>Inji Tsohon Hadimin shugaban kasa da ya ajiye aikinsa, Hakeem Baba Ahmad

Na kusa da Shugaba Tinubu kakkangeshi suke, basa bari a je kusa dashi ballantana a gaya masa halin da mutane ke ciki, watanni na 18 ina aiki a fadar shugaban kasa amma sau 3 muka taba haduwa da shugaban kasa shima a masallaci ne>>Inji Tsohon Hadimin shugaban kasa da ya ajiye aikinsa, Hakeem Baba Ahmad

Duk Labarai
Tsohon hadimin shugaban kasa da ya ajiye aikinsa, Hakeem Baba Ahmad ya bayyana daya daga cikin matsalolin da ya fuskanta a fadar shugaban kasar. Yace babbar matsala da suka fuskanta itace basa samun ganin Shugaban kasa a matsayinsu na wanda suke masa aiki kuma suna cikin fadar. Yace shugaban kasar baya samun bayanai na gaskiya akan halin da talakawa ke ciki. Yace a watanni 18 da yayi a fadar shugaban kasar, sau 3 kacal ya taba haduwa da shugaban kasar shima kuma a masallaci ne.
In ka ga dama ka tara duka Gwamnonin Najeriya a APC idan ‘yan Najeriya suka ki zabenka dole ka sauka>>El-Rufai ga Tinubu

In ka ga dama ka tara duka Gwamnonin Najeriya a APC idan ‘yan Najeriya suka ki zabenka dole ka sauka>>El-Rufai ga Tinubu

Duk Labarai
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya mayar da martani kan yanda Gwamnoni ke rububin komawa jam'iyyar APC. El-Rufai yace idan gwamnatin Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta ga dama, ta tara duka 'yan Adawa a jam'iyyar APC idan 'yan Najeriya suka ki zabensa dole ya sauka. El-Rufai yace kuma hadakar da suke ta 'yan Adawa tsaf cikin sauki zasu iya kawar da gwamnatin Tinubu ba tare da Gwamna ko daya ba. El-Rufai ya bayyana hakane yayin ganawa da 'yan Jarida a Kano, ranar litinin inda yace Idan Tinubu ya ga dama ya tara duka Gwamnonin Najeriya a APC amma idan 'yan Najeriya suka ki zabarsa shikenan ta kare. A jiyane dai APC ta karbi gwamnan jihar Delta daya canja sheka daga PDP. Hakanan Shugaban APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje yace akwai karin gwamnoni da zas...
Gwamnoni da yawa zasu dawo APC Saboda Tinubu na mulki na Adalci>>Inji Ganduje

Gwamnoni da yawa zasu dawo APC Saboda Tinubu na mulki na Adalci>>Inji Ganduje

Duk Labarai
Shugaban jam'iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayar da tabbacin cewa, Gwamnoni da yawa zasu sake komawa jam'iyyar. Ya bayyana hakane a wajan taron karbar gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori da ya koma jam'iyyar ta APC. Ganduje ya jinjinawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu saboda shugabanci na gari da yake samarwa a Najeriya. Ganduje yace a yanzu suna da gwamnoni 22 kenan a jam'iyyar APC inda yace mutane su saka ido su gani akwai karin gwamnonin da zasu dawo APC nan gaba.
Ku baiwa Zuciyarku hakuri ko tana so ko bataso ku sake zaben mu, saboda mu samu kammala gyaran da muka fara, idan kuka zabi wani shugaban kasa, ba Tinubu ba, za’a samu babbar matsala dan zai dakatar da duka ayyukan ci gaban da ya fara ne>>Gwamnatin Tinubu ta roki ‘yan Najeriya

Ku baiwa Zuciyarku hakuri ko tana so ko bataso ku sake zaben mu, saboda mu samu kammala gyaran da muka fara, idan kuka zabi wani shugaban kasa, ba Tinubu ba, za’a samu babbar matsala dan zai dakatar da duka ayyukan ci gaban da ya fara ne>>Gwamnatin Tinubu ta roki ‘yan Najeriya

Duk Labarai
Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta mika kokon bararta ga 'yan Najeriya cewa su sake zabenta dan ta sami ta kammala gyaran da ta dauko na tattalin arziki. Gwamnatin tace idan aka zabi wani shugaban kasa wanda ba tituba, za'a samu matsala dan kuwa zai zo ya dakatar da dukkanin ayyukan da shugaba Tinubun ya fara ne. Ministan harkokin jiragen sama, Festus Keyamo ne ya bayyana haka a wata hira da aka yi dashi a gidan talabijin na channels TV. Keyamo yace duk wani dan APC ko yana so ko bayaso ya kamata ya ajiye son zuciya ya yi aiki tukuru dan ganin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sake darewa kan mulki. Yace ta hakane kawai zai samu damar kammala ayyukan ci gaba da ya fara dan kuwa a baya an ga yanda idan aka zabi sabon shugaban kasa yake dakatar da ayyukan ci gaba n...
Abin Kunya:Wata Daya da gama gyaran Matatar Man fetur ta Warri ta sake lalacewa duk da kashe Dala Miliyan $897m wajan gyaranta

Abin Kunya:Wata Daya da gama gyaran Matatar Man fetur ta Warri ta sake lalacewa duk da kashe Dala Miliyan $897m wajan gyaranta

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Matatar Man fetur ta Warri da gwamnati ta kashe Dala Miliyan $897m wajan gyaranta ta sake lalacewa. Rahoton yace ko da aka kammala gyaran, matatar man ta fara aiki a watan Nuwamta na shekarar data gabata ne kuma kaso 40 cikin 100 na matatar ne ke aiki. Saidai a ranar January 25, 2025 an sake kulle matatar ta daina aiki saboda ta kara lalacewa. An yi wannan gyaranne a karkashin shugabancin Tsohon shugaban NNPCL, Mele Kolo Kyari wanda tuni ya ajiye aiki. Wannan lamari yasa ana sukar kamfanin na NNPCL da gazawa.