Saturday, December 20
Shadow

Duk Labarai

Wace Kadunar kaje? Mutanen Kaduna suna tambayi Tsohon Hadimin shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad bayan da yace ya je Kaduna yaga Gwamnatin jihar na ta aiki tukuru

Wace Kadunar kaje? Mutanen Kaduna suna tambayi Tsohon Hadimin shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad bayan da yace ya je Kaduna yaga Gwamnatin jihar na ta aiki tukuru

Duk Labarai
Hadimin tsohon shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa ya je Kaduna a karshen mako kuma yaga yanda Gwamnatin jihar ke ta ayyukan raya kasa. Yace irin abinda suke nema a Kano kenan tun shekara 1999. https://twitter.com/BashirAhmaad/status/1916925432441753937?t=-the03HnWAK_hcUAUnd99Q&s=19 Saidai 'yan Kaduna da yawa sun yi caaa a kansa inda suke tambayar shi cewa wace Kadunar ya je?
SDP ta fara kaɗa hantar jam’iyya mai mulki, mu ba gwaskaye mu ke so ba Talakawa sun ishe mu – El-Rufai

SDP ta fara kaɗa hantar jam’iyya mai mulki, mu ba gwaskaye mu ke so ba Talakawa sun ishe mu – El-Rufai

Duk Labarai
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce sabuwar jam’iyyar da ya koma, SDP, ta fi buƙatar ta tara mambobi daga tushe ba wai manyan ƴan siyasa ba. El-Rufai, wanda ya fice da ga jam’iyyar APC a watannin baya, ya baiyana hakan ne bayan wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudanar a jihar Kano a yau Litinin. A cewar sa, SDP jam’iyya ce da ke rajin farfaɗo da dimokuraɗiyya tun daga tushe domin gyaran Nijeriya. “Mu ba mu damu da tara manyan ƴan siyasa a SDP ba. Mun fi son mu ga kamar mutane miliyan 3 sun yi rijista a SDP. “SDP jam’iyya ce da za ta baiwa kowa dama iri ɗaya. Ba za mu bari wani mutum ɗaya ya riƙa iko da jam’iyyar ba. “So mu ke yi mu gyara dimokuraɗiyyar kasar nan,” in ji El-Rufai, yayin da ya ke amsa tambayoyi daga manema labarai. Hakazalika El-Rufai ya ce...
Miliyoyin mutane a kasashen Sifaniya da Portugal sun tsinci kansu cikin yanayi na duhu sakamakon katsewar lantarki a sassan ƙasashen

Miliyoyin mutane a kasashen Sifaniya da Portugal sun tsinci kansu cikin yanayi na duhu sakamakon katsewar lantarki a sassan ƙasashen

Duk Labarai
Miliyoyin mutane a kasashen Sifaniya da Portugal sun tsinci kansu cikin yanayi na duhu sakamakon katsewar lantarki a sassan ƙasashen. Lamarin ya shafi harkokin sufuri da sadarwa, da ma harkokin kasuwanci da dama. Asibitoci na gudanar da harkokinsu yadda aka saba saboda suna amfani da injinan janareto. Reuters
Da yan Kwankwasiyya yanda sukewa Kwankwaso biyayya haka sukewa Allah biyayya da duk Al’jannah Za’a shiga

Da yan Kwankwasiyya yanda sukewa Kwankwaso biyayya haka sukewa Allah biyayya da duk Al’jannah Za’a shiga

Duk Labarai
Ɗan majalisar ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da gidan radiyon Hikima, inda yake sukar yadda Kwankwaso ke tafiyar da siyasarsa, da kuma yadda yake yawan alaƙanta mutane da abubuwan da shi kansa ya ke aikatarwa. Abdullahi Sani Rogo wanda shine ɗan Majalisar tarayya mai wakiltar Karaye/Rogo dake jihar Kano. Ya bayyana haka ne yayin daya ke tabbatar wa da magoya bayansa cewa ya sauya sheka daga jam'iyyar NNPP zuwa APC. Me zaku ce???
Ku Kyale ‘yan Arewa, surutu kawai suke, Yunwar da zata kamasu nan da shekarar 2027, da kansu zasu rika rokon a basu Naira dubu 2 su zabi APC>>Inji Wike

Ku Kyale ‘yan Arewa, surutu kawai suke, Yunwar da zata kamasu nan da shekarar 2027, da kansu zasu rika rokon a basu Naira dubu 2 su zabi APC>>Inji Wike

Duk Labarai
Kafafen sada zumunta sun karade da wasu kalamai da ake zargin Ministan Abuja, Nyesome Wike da furtawa akan Arewa. Kalaman dai sun baiwa mutane mamaki matuka ace daga bakin Wike suka fito saidai sanin yanda yake da katobara, wasu sun ce basu yi mamakin jin cewa ya fadi hakan ba. Rahotannin dai na cewa, Wike yace ne a kyale 'yan Arewa surutu kawai suke, nan da shekarar 2027 yunwar da zata kama su da kansu zasu rika rokon a basu dubu biyu su zabi APC. Zuwa Yanzu dai Wike be fito ya tabbatar ko karyata wannan kalamai da aka zargeshi da furtawa ba.
Kamata yayi ka yi hakuri ka barwa dan kudu ya tsaya takara a 2027>>Wasu ‘yan PDP daga kudu suka gayawa Atiku

Kamata yayi ka yi hakuri ka barwa dan kudu ya tsaya takara a 2027>>Wasu ‘yan PDP daga kudu suka gayawa Atiku

Duk Labarai
Atiku Abubakar 2011 President campaign Photo by www.mortenfauerby.dk ©mortenfauerby 2010 - all rights reserved Wasu 'yan PDP daga Kudancin Najeriya sun baiwa Atiku Abubakar bakin cewa ya hakura da maganar tsayawa takara a shekarar 2027 ya barwa dan kudu. Sun ce ba ma Atiku kadai ba, duk wani dan Arewa kamata yayi ace ya hakura da tsayawa takara a barwa dan kudu ya tsaya takarar shugaban kasa a shekarar 2027. Kungiyar tace dama can Atiku ne ya fara jawowa jam'iyyar PDP koma baya a shekarar 2014 inda ya jagoranci gwamnoni 5 suka fice daga jam'iyyar suka koma APC suka juyawa Goodluck Jonathan baya. Shugaban kungiyar, Dennis Shima ne ya fadi haka inda yace ya kamata a bar dan kudu ya kammala shekara 8 kamar yanda Buhari yayi
Gwamnatin Jihar Akwa-Ibom ta tilastawa ma’aikatan Lafiya shiga jarjejeniya da rantsuwa cewa idan ta dauki nauyinsu suka yi karatu ba zasu tsere zuwa kasashen waje ba

Gwamnatin Jihar Akwa-Ibom ta tilastawa ma’aikatan Lafiya shiga jarjejeniya da rantsuwa cewa idan ta dauki nauyinsu suka yi karatu ba zasu tsere zuwa kasashen waje ba

Duk Labarai
Gwamnatin jihar Akwa-Ibom ta bukaci ma'aikatan lafiya a jihar da su sha rantsuwa cewa ba zasu tsere ba idan ta dauki nauyinsu suka je suka yi karatu. Shugaban ma'aikatan jihar, Elder Effiong Essien ne ya bayyana hakan inda yace zasu dauki ma'aikatan lafiya 600. Yace wannan bukata dolece saboda a tabbatar da cewa ma'aikatan lafiyar sun gudanar da aiki daidai da yawan kudin karatun da aka kashe a kansu.
Jarumin Maza, ya auri mata 3 cikin kwana 3

Jarumin Maza, ya auri mata 3 cikin kwana 3

Duk Labarai
Wani dan kasar Ghana dake zaune a birnin Dubai na hadaddiyar daular larabawa me suna Nicholas Mbir ya auri mata 3 a cikin kwanaki 3. Sunayen matan da ya aura sune kamar haka: Angelina Prah, Grace Agyarko, sai Esther Abass. An daura aurenne ranar April 26, 2025 a garin Winneba dake kasar ta Ghana. Da yawa sun jinjina masa.
Duk Arewa Babu Dan siyasar da ya kai Kwankwaso Butulci>>Inji Dan Balki Kwamanda

Duk Arewa Babu Dan siyasar da ya kai Kwankwaso Butulci>>Inji Dan Balki Kwamanda

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} A wata hira da ya yi da gidan radiyon jakadiya ɗan siyasar ya bayyana irin salon siyasar madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da cewa ya butulce wa duk waɗanda suka taimake shi a siyasa, saboda haka canza shekar da ’yan majalissar jam'iyyarsa suka yi alama ce ta rasin ingantaccen shugabanci na jagoran na Jam'iyyar NNPP.
Ba mu damu da manyan ƴan siyasa a SDP ba, mun fi buƙatar ƴan dangwale – El-Rufai

Ba mu damu da manyan ƴan siyasa a SDP ba, mun fi buƙatar ƴan dangwale – El-Rufai

Duk Labarai
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce sabuwar jam'iyyar da ya koma, SDP, ta fi buƙatar ta tara mambobi daga tushe ba wai manyan ƴan siyasa ba. El-Rufai, wanda ya fice da ga jam'iyyar APC a watannin baya, ya baiyana hakan ne bayan wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudanar a jihar Kano a yau Litinin. A cewar sa, SDP jam'iyya ce da ke rajin farfaɗo da dimokuraɗiyya tun daga tushe domin gyaran Nijeriya. "Mu ba mu damu da tara manyan ƴan siyasa a SDP ba. Mun fi son mu ga kamar mutane miliyan 3 sun yi rijista a SDP. "SDP jam'iyya ce da za ta baiwa kowa dama iri ɗaya. Ba za mu bari wani mutum ɗaya ya riƙa iko da jam'iyyar ba. "So mu ke yi mu gyara dimokuraɗiyyar kasar nan," in ji El-Rufai, yayin da ya ke amsa tambayoyi daga manema labarai. Hakazalika El-Rufai ya ce...