An kàshè shanu 37 a jihar Plateau
Akalla shanu 37 aka harbe a ƙauyen Tashek da ke ƙaramar hukumar Riyom ta jihar Plateau a jiya Lahadi.
A cewar shugaban reshen jihar na kungiyar Miyetti Allah , Ibrahim Yusuf Babayo, lamarin ya faru ne kusan ƙarfe 1:00 na rana.
Wannan harin na baya-bayan nan ya faru ne kasa da mako guda bayan wani hari makamancin haka a ƙauyen Tanjol, wanda ma yana cikin ƙaramar hukumar Riyom, inda 'yan bindiga suka budewa makiyaya wuta, suka jikkata makiyaya biyu tare da kashe shanu biyar.
Shugaban kungiyar ya bayyana harin a matsayin wanda ba tare da wani dalili ba, yana mai cewa lamarin wani ƙulli ne na masu aikata hakan domin cimma wani ɓoyayyen buri.
Babayo ya ce, “'Yan bindiga sun mamaye yankin suka fara harbin shanun da ke kiwo, wanda ya kai ga mutuwar shanu 37 da kuma raunata wani makiya...








