Ana rade-radin gwamnan jihar Naija yayi Murabus
WATA SABUWA: Mataimakin Gwamnan Neja, Yakubu Garba, Zaiyi murabus
Mataimakin Gwamnan jihar Neja, Yakubu Garba, zai yi murabus daga mukaminsa "kowane lokaci daga yanzu", majiyoyi da dama sun shaidawa jaridar DAILY NIGERIAN.
A shirye-shiryen murabus din, majiyoyin sun ce mataimakin gwamnan da ke cikin rikici ya fara kwashe wasu kayansa daga Gidan gwamnati a karshen mako.
Wasu majiyoyi sun tabbatar wa DAILY NIGERIAN cewa sun ga yadda aka yi ta komowar kadarorin mataimakin gwamnan daga gidan gwamnati tsakanin Asabar da Lahadi.
Majiyar ta kara da cewa "Kamar yadda nake magana da ku, ya kwashe kayansa da yawa daga gidan gwamnati zuwa gidansa na kashin kansa.
DAILY NIGERIAN ta tattaro cewa wasu sarakunan gargajiya a jihar sun ziyarce shi a daren ranar Lahadin da ta gabata domin lal...








