Saturday, December 20
Shadow

Duk Labarai

Ji Yanda Tsohon Ministan Sufuri Amaechi ya bayar da labarin yanda Allah ya tuka motarsa bayan da bacci ya kwasheshi yana tsaka da tuki daga Kaduna zuwa Abuja

Ji Yanda Tsohon Ministan Sufuri Amaechi ya bayar da labarin yanda Allah ya tuka motarsa bayan da bacci ya kwasheshi yana tsaka da tuki daga Kaduna zuwa Abuja

Duk Labarai
Tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya bayar da labarin cewa, akwai sanda ya tuka mota daga kaduna zuwa Abuja yana bacci inda yace allah ne ya tuka motar ya kaisu Abuja lafiya. Ya ce a lokacin sun je Kanone sun nada sarki, zasu koma sai aka hana sayar musu da tikitin jirgin sama. Yace sai ya kira tsohon gwamnan Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya sanar dashi inda Kwankwason yace masa ya je gidan gwamnatin jihar. Saidai yace a yayin da yake shirin tafiyane sai shugabab DSS na Kano ya sameshi yace masa duk abinda yake ciki ya fice daga garin Kano dan ba zai iya bashi tabbacin kariyar rayuwarsa ba. Yace ya gayawa shugaban DSS din yanda suka yi da Gwamna, yace masa amma kada ya sake ya je gidan gwamnatin, su fice daga Kano kawai. Amachi yace tare dashi akwai Goje, Baraje da Pro...
Ji yanda aka kama wasu ‘yan Najeriya na shirin shiga kasar Ingila da wani yaro da suka sata daga Najeriya

Ji yanda aka kama wasu ‘yan Najeriya na shirin shiga kasar Ingila da wani yaro da suka sata daga Najeriya

Duk Labarai
Hukumomin kula da iyaka na kasar Ingila sun kama wasu mutane biyu mace da namiji daga Najeriya wanda suka yi yunkurin shiga kasar da wani yaro da aka yi amannar satoshi suka yi. Hukumomin kula da iyakar a filin jirgin sama na Manchester sun tsargu da mutanen bayan ganin yanda suke tafiya da yaron. Ko da aka bincikesu sai namijin me suna Raphael Ossai yace shine mahaifin yaron sannan kuma matar da suke tare Oluwakemi Olasanoye wai itace mahaifiyar yaron. Saidai da bincike yayi tsanani, an gano cewa, akwai kuma wata takardar haihuwa data bayyana wata mata dake zaune a kasar ta Ingila wadda aka bayyana da cewa itace mahaifiyar yaron. Tuni dai aka kama matar da namijin.
Allah Sarki:Ji yanda wata mata me ciki ta rasu a Babban Asibitin Minna ana tsaka da mata aiki Nepa suka dauke wuta kuma babu fetir a cikin Janareta

Allah Sarki:Ji yanda wata mata me ciki ta rasu a Babban Asibitin Minna ana tsaka da mata aiki Nepa suka dauke wuta kuma babu fetir a cikin Janareta

Duk Labarai
Labarin wata mata me ciki da ta rasu a babban asibitin garin Minna na jihar Naija, Babbangida Aliyu General Hospital yayin da ake mata aiki ya yadu sosai a kafafen sada zumunta. Mijin matar ne ya wallafa labarin a shafinsa inda labarin ya watsu sosai. Yace an farawa matar tasa aiki da wutar Nepa, sai aka dauke. Ashe Janaretan ba man fetur, sai da aka je aka siyo mai aka zubawa janaretan amma yaki tashi, yace sai da aka je aka kira makanike. Yace a yayin da ake duk wannan abin, matarsa na cikin dakin tiyatar an fara mata aiki ba'a gama ba. Danga nan ne ta rasu. Muna fatan Allah ya jikanta
Murtala Idris Ya Damka Kyautar Bajimin Da Ya Baiwa Rarara Ta Hannun Abdullahi Alhikma, Inda Alhikma Ya Yî Godiya A Madadin Mawaƙin

Murtala Idris Ya Damka Kyautar Bajimin Da Ya Baiwa Rarara Ta Hannun Abdullahi Alhikma, Inda Alhikma Ya Yî Godiya A Madadin Mawaƙin

Duk Labarai
Murtala Idris Ya Damka Kyautar Bajimin Da Ya Baiwa Rarara Ta Hannun Abdullahi Alhikma, Inda Alhikma Ya Yî Godiya A Madadin Mawaƙin Daga ƙarshe Alhikma ya tambeye shi "ko akwai wani abu da kake so ya sa ka yi haka? Sai Murtala yace "Ni dai nabyi masa ne saboda irin kaunar da nake masa, ina kuma fatan ganin mun haɗu da shi a gaske". Daga Abubakar Shehu Dokoki
Hotunan Kafin Auren Diyar Gwamnan Jihar Katsina, Hajia Aisha Dikko Radda Da Angonta, Ahmad Usman (Inuwar Ƙasar Hausa)

Hotunan Kafin Auren Diyar Gwamnan Jihar Katsina, Hajia Aisha Dikko Radda Da Angonta, Ahmad Usman (Inuwar Ƙasar Hausa)

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Hotunan Kafin Auren Diyar Gwamnan Jihar Katsina, Hajia Aisha Dikko Radda Da Angonta, Ahmad Usman (Inuwar Ƙasar Hausa) Za a daura auren ne a ranar Asabar mai zuwa idan Allah Ya kai mu Wace irin fata za ku yi musu? Daga Jamilu Dabawa
Gwamnatin tarayya ta samu Naira Biliyan 84 daga kudin harajin Naira 50 da take cirewa akan duk Dubu 10 da ‘yan Najeriya suke fire daga Bankinsu

Gwamnatin tarayya ta samu Naira Biliyan 84 daga kudin harajin Naira 50 da take cirewa akan duk Dubu 10 da ‘yan Najeriya suke fire daga Bankinsu

Duk Labarai
Rahotanni sun tabbatar da cewa, Gwamnatin tarayya ta samu jimullar Naira Biliyan 84.03 daga kudin harajin Naira 50 da aka sanya akan kowace Naira Dubu 10 da 'yan Najeriya suka cire daga bankinsu. An samu wadannan kudade ne a cikin watanni 3 na farkon shekarar nan da muke ciki. A watanni 3 na farko na shekarar data gabata ta 2024, kudaden shigar da aka samu ta irin wannan hanya Naira Biliyan N47.74bn ne wanda hakan ke nuna a yanzu an samu karin kaso 76 cikin 100. Wadannan kudade ana rabawa gwamnatoci ne a matakai daban-daban watau gwamnatin tarayya dana jihohi da kananan hukumomi.
Gyare-Gyaren da muka yi akwai wahala, amma suna bada sakamako me kyau>>Inji Gwamnatin Tarayya

Gyare-Gyaren da muka yi akwai wahala, amma suna bada sakamako me kyau>>Inji Gwamnatin Tarayya

Duk Labarai
Gwamnan babban Bankin Najeriya, Cardoso ya bayyana cewa, Gyare-Gyaren da gwamnatin tarayya ta zo dasu babu sauki amma suna bayar da sakamako me kyau. Ya bayyana hakane a wajan taron da aka gudanar a birnin Washington DC na kasar Amurka wanda IMF da bankin Duniya suka shirya. Yace wadannan Gyare-Gyaren sun dora Najeriya a turbar ci gaba kuma a yanzu suna bayar da sakamako me kyau. Wasu daga cikin Gyare-Gyaren da gwamnatin tarayya ta kawo sune cire tallafin man fetur, cire tallafin dala da sauransu.