Monday, May 11
Shadow

Duk Labarai

Mahara sun shiga coci suka yankewa Fasto yatsu suka kuma harbeshi sannan suka sace mutane 6

Mahara sun shiga coci suka yankewa Fasto yatsu suka kuma harbeshi sannan suka sace mutane 6

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Delta sun bayyana cewa, wasu mahara sun shiga coci a garin Asagba Ogwashi dake karamar hukumar, Aniocha South ta jihar ina suka harbi fasto suka sace mutane 6. Kakakin 'yansandan jihar, Mr. Bright Edafe ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace tuni jami'ansu suka bazama daji dan bin sahun masu garkuwa da mutanen. Zuwa yanzu dai maharan basu kira 'yan uwan wadanda suka sace din ba. Tuni aka garzaya da faston zuwa Asibiti dan duba lafiyarsa.
Hattara: An gano masu gasa kaji na gefen hanya suna amfani da lalatatun Kaji

Hattara: An gano masu gasa kaji na gefen hanya suna amfani da lalatatun Kaji

Duk Labarai
Wani Rahoto na musamman da Jaridar Vanguard ta yi ya gano cewa wasu masu gasa kaji na gefen hanya na amfani da kajin da suka lalace suna sayarwa mutane. Rahoton yace matsin tattalin arziki da rashin kasuwa yasa dole wasu masu gasa kajin da nama na bakin titi suka daina kasuwancin. Inda wasu kuma a kokarin rage Asara da ci gaba da kasuwancin kamar yanda hausawa ke cewa da babu gara ba dadi ke siyo kajin da suka dade a ajiye suka fara lalacewa. Rahoton yace masu sayarwa da masu gasa kajin naman sukan ajiyesu a firjin ne, to dalilin rashin kasuwa, idan kajin suka dade ba'a siya ba sai su fara lalacewa har dandanonsu ya fara canjawa. Amma maimakon a yaddasu, saboda gudun Asara, sai a rika sayarwa da masu gasa naman irin wadannan kaji da suka fara lalacewa a farashi me sauki. Su ...
Ku daina baiwa Azzaluman shuwagabannin mu bashi>>NLC ta roki Bankin Duniya da IMF

Ku daina baiwa Azzaluman shuwagabannin mu bashi>>NLC ta roki Bankin Duniya da IMF

Duk Labarai
Kungiyar kwadago ta roki bankin Duniya da kungiyar bada lamuni ta Duniya, IMF da su daina baiwa mugayen shuwagabanni bashi. Kungiyar tace baiwa irin wadannan shuwagabannin bashi bashi da amfani dan kuwa tana kara rikita harkar mulki ne da kara jefa gwamnatocin wadannan kasashe cikin bashi da rashin ci gaba. Shugaban kungiyar NLC, Joe Ajaero ne ya bayyanawa hukumomin kudin na Duniya haka inda ya kuma gaya musu cewa shawarwari da suke baiwa Najeriya game da tattalin arzikinta na kara jefa kasar ne cikin talauci da rashin ci gaba. Joe Ajaero ya baiwa IMF da Bankin Duniyar shawarar cewa su daina bayar da shawarar tattalin arziki ga kasashe a dunkule, su rika bada shawarar da zata rika kawowa kowace kasa ci gaba.
Masu garkuwa da mutane sun sace wata mata a Asibitin dake Kano

Masu garkuwa da mutane sun sace wata mata a Asibitin dake Kano

Duk Labarai
Masu garkuwa da mutane sun sace wata mata me shekaru 60 da haihuwa a Asibitin mahaukata dake Dawanau, Karamar hukumar Dawakin Tofa Kano. Matar me suna Talatu Ali an yi garkuwa da itane a yayin da take jiran ganin Likita. Dan matar da dan uwanta ne suka kai ta Asibitin, saidai a yayin da suma suke jiran layi ya zo kanta taga likita, sai suka nemeta sama da kasa suka rasa. Lamarin ya farune ranar February 19, 2025 da misalin karfe 8 na safe, saidai ranar February 21 da misalin karfe 7 na safe an kira danginta inda aka tabbatar musu da cewa an yi garkuwa da itane. Hukumar 'yansandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin.
Ji yanda aka gano gawarwakin mutane 30 a Najeriya da aka yanke musu sassan jikinsu dan yin tsafi

Ji yanda aka gano gawarwakin mutane 30 a Najeriya da aka yanke musu sassan jikinsu dan yin tsafi

Duk Labarai
A yankin Oriendu na jihar Abia, mutane na cikin fargaba da tashin hankali bayan da aka rika tsintar gawarwakin mutane musamman mata wadanda aka cire musu al'aura. Lamarin ya fara faruwane tun daga shekarar data gabata. Basaraken yankin, HRH Eze Philip Ajomiwe, ya tabbatarwa da jaridar Leadership hakan. Yace 'yan sa kai sun kasa magance matsalar saboda mahara da ame zargin matsafa ne na da muggan makamai. yace dan haka suna kira da gwamnati data kai musu dauki.
Gwamnatin jihar Sokoto ta fara biyan malaman firamare mafi ƙanƙantar albashi

Gwamnatin jihar Sokoto ta fara biyan malaman firamare mafi ƙanƙantar albashi

Duk Labarai
Makonni uku bayan wani rahoton da BBC ta yi game da ƙorafin da malaman makarantun firamaren jihar Sokoto suka yi na rashin biyansu sabon albashi mafi ƙanƙanta na naira 70,000, gwamnatin jihar ta biya su, har ma da yi musu ƙari. Malaman makarantun firamaren sun shaida wa BBC irin farin cikin da suka ji game da alƙawarin da gwamnan jihar, Ahmad Aliyu ya cika, na biyansu sabon albashin kamar kowa tare da sauran ma’aikatan gwamnatin jihar da suka hada da na kananan hukumomi 23. Mai magana da yawun gwamnan jihar, Abubakar Bawa, ya shaida wa BBC cewa gwamnatin ta saurari ƙorafin da ma’aikatan suka yi ne, shi ya sa ta cika alƙawarin da ta ɗaukar musu tun da farko. A watan Yulin shekarar 2024 ne, shugaban Najeriya Bola Tinubu ya amince da ƙara albashi mafi ƙanƙanta ga ma'aikatan ƙasar dag...
Mutum huɗu sun mutu goma sun ji rauni a wata motar bas da ta ƙone a jihar Jigawa

Mutum huɗu sun mutu goma sun ji rauni a wata motar bas da ta ƙone a jihar Jigawa

Duk Labarai
Mutane huɗu sun ƙone ƙurmus wasu goma kuma sun ji raunuka yayin da wata mota ƙirar bas (Hummer) ta kama da wuta a garin Gwaram da ke jihar Jigawa. Lamarin wanda ya faru da misalin ƙarfe 4 na yamma, a jiya Asabar a kusa da makarantar sakanadare ta haɗaka ta gwamnati ta 'yammata da ke garin na Gwaram (Government Girls Unity Secondary School ) Wata sanarwa da kakakin 'yansanda na jihar SP Lawan Adam ya fitar a yau Lahadi ta nuna cewa motar ta tashi ne daga ƙaramar hukumar Zaki ta jihar Bauchi zuwa ƙauyen Ribadi da ke ƙaramar hukumar Gwaram ta jihar Jigawa. Sanarwar ta ce, ''motar na ɗauke ne da fasinja 44, da suka haɗa da manya 25 da yara 19.'' Kakakin 'yansandan ya ce, wutar ta kama ne sakamakon katifa da aka ɗaure a bayan motar da ke kusa da salansa. Sanarwar ta ƙara da cewa ...
Minista ya yi barazanar barin APC idan ba a sauya shugabancinta na Kano ba

Minista ya yi barazanar barin APC idan ba a sauya shugabancinta na Kano ba

Duk Labarai
Minista a ma'aikatar gidaje, Yusuf Abdullahi Ata ya yi barazanar cewa shi da magoyansa za su iya ficewa daga jam'iyyar APC a Kano, matuƙar ba a canja shugabancin jam'iyyar a jihar ba. Ministan ya ce furucin jagoran jam'iyyar ne ya jawo faɗuwar jam'iyyar a zaɓen da ya gabata na 2023, kamar yadda ya bayyana a wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafofin sadarwa, wanda aka ce ya yi a taron masu ruwa da tsaki na ƙaramar hukumarsa ta Fage a jihar Kano. Ata ya ce, “muna faɗa wa kowa, idan aka mayar da irinsu, duk irinmu fita za mu yi." Ya ƙara da cewa, "mu an mana tarbiya, mun san waye malami, mun san waye babba. Saboda haka ba za mu sauka daga turbarmu ba. Idan suka dawo da shi, mu za mu fita, kuma na rantse da Allah sai jam'iyyar ta sake faɗi zaɓe," in ji shi. "Dole a canja, dole a nemo...
Zan iya sauka daga mulki idan hakan zai sa a samu zaman Lafiya>>Inji Shugaban kasar Ukraine

Zan iya sauka daga mulki idan hakan zai sa a samu zaman Lafiya>>Inji Shugaban kasar Ukraine

Duk Labarai
Shugaban ƙasar Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce a shirye yake ya haƙura da kujerar shugabancin ƙasar idan haka ne zai zama silar samar da zaman lafiya a ƙasarsa. Zelensky ya bayyana haka ne a daidai lokacin da aka cika shekara uku ana gwabza yaƙi tsakanin Ukraine da Rasha. "Idan kuna so in sauka daga mulki, zan amince. Amma ina so ƙasata ta shiga ƙungiyar Nato," in ji shi a lokacin da yake amsa tambayoyi a wani taron manema labarai. Wannan jawabin na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan Shugaban Ƙasar Amurka Donald Trump ya kira shi da "mai kama-karyar mulki ba tare da zaɓe ba." "Maganarsa ba ta ɓata min tai ba," in ji Zelensky wanda aka zaɓa a watan Mayun shekarar 2029. Zelensky ya ƙara da cewa tabbatar da zaman lafiyae ƙasar ne a gaban shi, amma ba ya tunanin daɗewa a mulkin ƙasar...