Peter Obi na da masaniya kan ziyarar da na kai wa Abure – Datti
Peter Obi na da masaniya kan ziyarar da na kai wa Abure - Datti
Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour a zaɓen 2023, Datti Baba-Ahmed, ya ce jagoran jam'iyyar, Peter Obi, na da masaniya kan matakin da ya ɗauka na halartar taron ɓarin jam'iyyar da ke ƙarƙashin shugabancin Julius Abure.
Datti ya ce ya ɗauki matakin ne a wani yunƙuri na sulhunta ƴaƴan jam’iyyar da suka fusata.
Datti ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels, bayan ziyarar tasa ta janyo ce-ce-ku-ce.
“Jam’iyyar Labour ba jam’iyya ba ce da za a yi watsi da ita, ko a gudu daga cikinta, ko a yi watsi da muhimmancinta ba," in ji Datti.
“Ina tabbatar muku cewa kowanne mataki da nake ɗauka, ɗaukacin masu ruwa da tsaki (na jam'iyyar) na da masaniya a kai. Ba sai na shiga ...








