Ya kamata a dawo da tallafin aikin hajji ga maniyyatan Najeriya – Ndume
Jagoran ƴan kwamitin majalisar dattijan Najeriya kan harkokin ƙasashen waje a lokacin aikin hajjin 2025, Sanata Ali Ndume ya buƙaci da a mayar da tsarin bayar da tallafi kan batun aikin hajji a ƙasar domin rage tsadar kujera ga maniyyata.
Ndume ya fadi haka ne a tattaunawarsa da BBC jim kadan bayan kammala aikin hajjin 2025 a ƙasar Saudiyya.
Sanatan wanda ya nuna gamsuwa kan tsarin da aka samar ga mahajjatan Najeriya a Saudiyya ya ce "dama gwamnatin da ta shuɗe ita ce ta cire tallafin da ake bayarwa kan aikin hajji, saboda haka ya kamata a dawo da bayar da tallafi saboda aikin hajjin ya yi tsada."
Mahajjatan Najeriya a 2025 sun biya kuɗin kujera ne tsakanin naira miliyan 8.3 zuwa miliyan 8.8 dangane da ɓangaren ƙasar da suke zama.
Hakan ya ɗara abin da maniyyatan Najeriya suka ...








