Ji yanda Ɗaurarre a gidan yari ya lashe zaɓen cike-gurbi na majalisa a jihar Enugu
Hukumar zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta bayyana wani ɗan gidan yari, Bright Ngene na jam'iyyar Labour da aka ɗaure saboda satar naira miliyan 15, a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar Enugu ta kudu da aka yi a ƙarshen makon da ya gabata.
Mai magana da yawun hukumar a jihar, Sam Olumekun ya gabatar da sakamakon, bayan soke wanda aka yi a 2023.
RFI ya rawaito cewa a ranar 28 ga watan Yulin wannan shekara alkali ya ɗaure Ngene shekaru 7 a gidan yari, saboda samun sa da laifin satar naira miliyan 15 kuɗaɗen al'ummar yankin da ya fito da ke Jihar Enugu.
Rahotanni sun ce ya aikata laifin ne tun a shekarar 2017, amma a lokacin alkali ya bada damar cewar a kai shari'ar hukumar sasanta al'umma.
Amma bayan nasarar da ya samu a zaɓen shekarar 2023, sai alkalin ya ce an ba shi uma...








