Majalisar Wakilan Najeriya ta buƙaci gwamnati ta ceto ƴan ƙasar da ke maƙale a Saudiyya
Majalisar Wakilan Najeriya ta buƙaci gwamnati ta ceto ƴan ƙasar da ke maƙale a Saudiyya.
Majalisar Wakilan Najeriya ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta ceto ƴanƙasar da ke maƙale a Saudiyya sakamakon sabbin sauye-sauyen dokokin ayyukan ƙwadogo da hukumomin Saudiyya suka bijiro da su.
Dan majalisar wakilai daga jihar Kano, Hon. Muhammad Bello Shehu ne ya gabatar da udurin a yayin zaman majalisar na ranar Laraba.
A baya-bayan nan ne dai hukumomin Saudiyya suka bijiro da wasu sauye-sauye kan dokokin da suka shafi ayyukan baƙi a ƙasar, ciki har da daina sabunta takardun izinin aiki a ƙasar ga wasu mutanen.
Hon. Muhammad Shehu ya ce sauye-sauyen sun tilasta wa wasu ƴan Najeriya da dame da ke zaune a Saudiyya rasa ayyukansu, yayin da wasu ke fuskantar tsadar kuɗin sabunta takardun...








