Thursday, May 7
Shadow

Duk Labarai

‘Yan majalisar Tarayya sun nemi Kotu ta tursasa Gwamnonin PDP su biyasu Naira Biliyan 1 saboda gwamnonin sun shigar da karan neman Shugaba Tinubu ya janye dakatarwar da yawa Gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara

Majlisar tarayya ta shigar da kara inda take kalubalantar Gwamnonin PDP 11 da suka shigar da kara suna neman a Tursasa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya janye dakatarwar da yawa gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara. Majalisar tace Kotun ma bata da hurumin sauraren wannan karar. Sannan ta nemi kotun ta sa Gwamnonin PDP din su biya majalisar Naira Biliyan 1 saboda shigar da wanan karar da ta sabawa doka. Gwamnonin PDP da suka shigar da karar sune Gwamnonin jihohin Adamawa, Enugu, Osun, Oyo, Bauchi, Akwa Ibom, Plateau, Delta, Taraba, Zamfara, da Bayelsa. Sun bayyana cewa shugaban kasa bashi da hurumin shiga harkar zababben gwamna da mataimakinsa ko ya saukesu ya maye gurbinsu da wasu wanda ba zababbu, hakanan shugaban bashi da hurumin dakatar da majalisar jihar. Hakanan sun ce ...
Talauci na karuwa a Najeriya, Musamman a kauyuka>>Inji Bankin Duniya

Talauci na karuwa a Najeriya, Musamman a kauyuka>>Inji Bankin Duniya

Duk Labarai
Bankin Duniya ya bayyana cewa, Talauci na karuwa a Najeriya musamman a cikin kauyukan Kasar. Bankin yace kaso 75.5 na mazauna kauyuka na fama da Talauci inda suke rayuwa a kasa da layin Talauci na Duniya. Bankin ya bayyana hakane a rahoton da ya fitar na watan Afrilun shekaar 2025. A watan da ya gabata ne dama bankin ya bayyana cewa, 'Yan Najeriya da yawa zasu fada cikin matsanancin Talauci nan da shekaru 5 masu zuwa. Rahotan yace a biranen Najeriya kuma kaso 41.3 cikin 100 ne na mutane ke rayuwa a kasa da layin Talauci. Layin Talauci dai an dorashi ne akan Mutum ya rika rayuwa akan dala akalla $2.15 kwatankwacin Naira Dubu 3440 kullun, duk wanda yake rayuwa a kasa da wannan kudi a kullun to yana cikin wanda ake kallo a matsayin Matalauta. Rahoton yace Talaucin yafi yawa ...
Kalli Bidiyo daga wajan Bikin Diyar Gwamnan Katsina, A’isha Dikko Radda, Kudin da aka yi wasa dasu a waja yasa wasu na fadin Wanan watan babu Albashi a Katsina

Kalli Bidiyo daga wajan Bikin Diyar Gwamnan Katsina, A’isha Dikko Radda, Kudin da aka yi wasa dasu a waja yasa wasu na fadin Wanan watan babu Albashi a Katsina

Duk Labarai
A ranar Asabar din data gabata ne aka daura auren diyar Gwamnan jihar Katsina, A'isha Dikko Radda da Angonta, Usma Ahmad. Bikin Yayi Armashi, hadda Shugabab kasa, Bola Ahmad Tinubu ya damu halarta. A ci gaba da shagalin Bikin, Matan Gwamnoni musaman na jihohin Arewa sun halarci wajan wannan daurin aure. A wani Bidiyo dake ta yawo a kafafen sada zumunta, an ji yanda ake kashe kudi sosai a wajan bikin wanda hakan yasa mutane da yawa kokawa. Wasu sun ce mutanen jihar Katsina a wannan watan babu Albashi. https://twitter.com/hadd1nzarewa/status/1919161055344828494?t=y4aSZbQ802WwnGrxwL_eMg&s=19 Wasu na ganin a yayin da mutane ke fama da matsin rayuwa da kuma matsalar tsaro wannan bikin na kece raini bai dace ba.
YA SUBHANALLAH: Al’ummar Wasu Kauyuka Sama Da Ashirin Kenan A Yayin Da Suke Gudu Suna Barin Matsugùnansu Bayan Barazanar Kai Hàrì Da Riķaķken Dàn Bìndiga Kuma Babban Yaron Beĺlò Ťùŕjì, Wato Kallamu YaÝi Musu, Inda Suka Shigo Garin Gatawa Neman Mafaka

YA SUBHANALLAH: Al'ummar Wasu Kauyuka Sama Da Ashirin Kenan A Yayin Da Suke Gudu Suna Barin Matsugùnansu Bayan Barazanar Kai Hari Da Riķaķken Dàn Bìndiga Kuma Babban Yaron Beĺlò Ťùŕjì, Wato Kallamu YaÝi Musu, Inda Suka Shigo Garin Gatawa Neman Mafaka
Almajiri Mahaddacin Ķùr’ani Ya Kafa Tarihi A Jami’ar Jihar Nasarawa, nda Ya Fita Da Sakamako Mafi Daraja (First Class

Almajiri Mahaddacin Ķùr’ani Ya Kafa Tarihi A Jami’ar Jihar Nasarawa, nda Ya Fita Da Sakamako Mafi Daraja (First Class

Duk Labarai
Almajiri Mahaddacin Ķùr'ani Ya Kafa Tarihi A Jami'ar Jihar Nasarawa, nda Ya Fita Da Sakamako Mafi Daraja (First Class) {"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Sama da shekara biyar ba a samu wanda ya fita da 'First Class' a bangaren Geology ba sai wannan Almajiri mai suna Muhammad Jafar Usman. Kuma tunda aka kafa jami'ar ta jihar Nasarawa a 1992 dalibi mušùĺmì a bangaren geology bai taba zama 'First class' ba sai shi. Daga Abdurrahaman Goni Shuaibu
Kalli Bidiyo: Hukumar Hisbah ta Kano ta kai ziyara gidan yarin Goron Dutse dan binciken zargin Luwadi da aka ce ana yi da yara

Kalli Bidiyo: Hukumar Hisbah ta Kano ta kai ziyara gidan yarin Goron Dutse dan binciken zargin Luwadi da aka ce ana yi da yara

Duk Labarai
Bayan yaduwar Bidiyon wani zargin Luwadi da aka ce ana yo da yara a gidan yarin Goron Dutse dake Kano, Hukumar Hisbah ta aike da wakilanta gidan yarin. Kuma bayan kammala bincike, sun ce wannan zargi da aka yi ba gaskiya bane. Hukumar tace a kwanannan har saukar Qur'ani aka yi a gidan yarin hakanan wasu masu laifin da ake tsare dasu ma sun Samu Digiri da sauransu amma duk ba'a yada ba sai masha'a aka yada. https://twitter.com/babarh_/status/1919094366817116378?t=MvYMlzSD2W_2rOvyP3PnUw&s=19 Hukumar ta yi kira ga mutane dasu daina yada abinda basu da tabbaci akansa.
ABIN A YABA: Gwamna Abba Kabir Ya Gana Da Iyayen Wasu Yara Almajirai Biyu Da Ya Ci Karo Da Suna Kwance A Bakin Titi Cikin Dare, Inda A Take Cikin Daren Ya Sa Aka Kwashe Su Aka Kai Su Fadar Gwamnati Aka Ba Su Masauki Da Abinci

ABIN A YABA: Gwamna Abba Kabir Ya Gana Da Iyayen Wasu Yara Almajirai Biyu Da Ya Ci Karo Da Suna Kwance A Bakin Titi Cikin Dare, Inda A Take Cikin Daren Ya Sa Aka Kwashe Su Aka Kai Su Fadar Gwamnati Aka Ba Su Masauki Da Abinci. Yau kuma cikin ikon Allah Gwamnan ya gana da iyayen yaran. Inda ya ba su kudi su sayi kayan abinci.
Kalli Bidiyo: An zargi Ana yiwa kananan yara maza fyade a gidan yarin Goron Dutse dake Kano

Kalli Bidiyo: An zargi Ana yiwa kananan yara maza fyade a gidan yarin Goron Dutse dake Kano

Duk Labarai
Wani faifan Bidiyo ya bayyana inda aka ji wani bawan Allah na ikirarin cewa ana yiwa yara maza fyade a gidan yarin Goron Dutse dake Kano. Yace ana amfani da kananan shekaru da yaran ke da su da kuma bukata ta abinci da suke da ita ana lalata dasu. Yace a wasu lokutan ma ana hada baki da wasu bata garin ma'aikatan gidan yarin ana basu kudi ana baiwa yaran a daukesu, yace a wasu lokutan kuma yawan kudin da za'a baiwa yaranne ke daukar hankalinsu su aikata wannan masha'a. https://twitter.com/bapphah/status/1918931313190412518?t=Ul1rceH1xKpQnZ_oIIHdpQ&s=19 Yace yana kira ga hukumomi da su je su bincika abubuwan da ya fada inda yace akwai ma abubuwan da bai fada ba wanda ake yi a gidan yarin.