Sunday, March 15
Shadow

Duk Labarai

Wasu bala’o’i sun aukawa kasar Amurka inda A birnin Los Angeles aka yi girgizar kasa, a South Carolina gobarar daji ce ta kunno kai

Wasu bala’o’i sun aukawa kasar Amurka inda A birnin Los Angeles aka yi girgizar kasa, a South Carolina gobarar daji ce ta kunno kai

Duk Labarai
An samu girgizar kasa me maki 3.9 a birnin Los Angeles na Jihar California ta kasar Amurka. Hakan na zuwane bayan da aka kammala bikin bayar da kyautar Oscar 2025. Gurare da yawa da suka hada da Pasadena, Long Beach, San Fernando Valley, Torrance, Redondo Beach da Glendale sun bayyana cewa sun ji motsin kasa. Babu dai rahoton cewa wani ya ji rauni. Hakan na zuwane kwanaki kadan bayan da aka samu mummunar gobarar daji a birnin na Los Angeles. Hakanan a jihohin South Carolina da North Carolina na kasar Amurkar ma Wutar daji ce ta barke inda ake maganar taci kadada sama da 1,600 a South Carolina inda a North Carolina kuma taci kadada sama da 500. Mahukunta a yankunan da gobarar ta tashi sun bayar da umarnin mutane su fice daga yankunan.
Masu aikata Zina ku tuba kamin Lokaci ya kure muku, Idan ka tuba ka ci banza, Allah ya yafe>>Sheikh Guruntum

Masu aikata Zina ku tuba kamin Lokaci ya kure muku, Idan ka tuba ka ci banza, Allah ya yafe>>Sheikh Guruntum

Duk Labarai
Babban Malamin addinin Islama Sheikh Yusuf Guruntum ya jawo hankalin masu laifi musamman Mazinata da su tuba kamin lokaci ya kure musu. Malam ya bayyana hakane a wajan wa'azin da yake na watan Ramadana inda yace idan ka yi laifi to zaga ka ba daidai ba saidai fa idan ka Tuba. Malam ya bayar da misali da mazinata yace su tuba su daina, idan ba haka ba kuwa suka bari lokaci ya kure musu, zasu hadu da fushin Allah.
Gwamnatin jihar kebbi ta rage awanni aiki ga ma’aikatan jihar saboda Azumin watan Ramadana

Gwamnatin jihar kebbi ta rage awanni aiki ga ma’aikatan jihar saboda Azumin watan Ramadana

Duk Labarai
Gwamnan jihar Kebbi Nasir Idris ya amince da dokar rage awannin aiki ga ma'aikatan jihar saboda Azumin watan Ramadana. Hakan na kunshene a cikin sanarwar da Kwamishinan haraji na jihar, Awwal Dogondaji ya fitar ga manema labarai ranar Litinin a babban birnin jihar, Birnin Kebbi. Yace sabuwar dokar lokacib aiki shine, daga ranar Litinin zuwa alhamis, za'a rika yin aikine daga karfe 8 zuwa karfe 1 na rana. Sannan ranar Juma'a kuma za'a rika yin aikinne daga karfe 8 zuwa karfe 12 na rana. Yace za'a koma a ci gaba da yin aiki kamar yanda aka saba bayan watan Ramadana. Ya jawo hankalin mutanen jihar da su dukufa da yiwa jihar dama Najeriya baki daya addu'ar zaman lafiya da ci gaba.
Yanzu da wata kungiyar Addinin Musulunci zata ce bata yadda da bada hutun Kirsimeti ba da ya zaka ji? Tsohon Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad inda yace bai kamata kungiyar Kiristoci ta CAN ta soki hutun da jihohin Arewa suka bayar a makarantu ba saboda watan Ramadana

Yanzu da wata kungiyar Addinin Musulunci zata ce bata yadda da bada hutun Kirsimeti ba da ya zaka ji? Tsohon Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad inda yace bai kamata kungiyar Kiristoci ta CAN ta soki hutun da jihohin Arewa suka bayar a makarantu ba saboda watan Ramadana

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Tsohon hadimin shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad ya mayar da martani kan sukar da kungiyar Kiristoci ta CAN ta yi ga jihohin Arewa da suka bayar da hutun makarantu saboda zuwan Azumin watan Ramadana. Jihohin da suka bayar da hutun sune, Kano, Katsina, Kebbi da Bauchi, Ita dai kungiyar CAN tace idan ba'a janye wannan hutu ba zasu shiga kotu da wadannan jihohi saboda ba musulmai bane kadai a wadannan jihohi ba. A martaninsa, Malam Bashir yace bai so yayi magana akan lamarin ba amma...
Kansiloli Sun Tsige Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Bauchi

Kansiloli Sun Tsige Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Bauchi

Duk Labarai
Gamayyar kansiloli sun tsige shugaban karamar hukumar Shira da mataimakinsa ne a dalilin rashin iya jagoranci da rashin sanin makamar aiki, inda kansilolin suke zargin shuwagabannin biyu suna tafiyarda harkokinsu tareda tauye hakkin kansilolin da al'ummarsu Lamarin ya faru ne a safiyar yau litinin a karamar hukumar mulkin Shira dake jihar Bauchi, inda zuwa yanzu kansilolin sun tura takardar hukuncin a gaban majalisar jihar Daga Real Buroshi Mawaka Sokoto
Naira Miliyan 70 Tsohon shugaban kasa, Obasanjo ya so baiwa kowannen mu a matsayin cin hanci dan mu barsa ya zarce a karo na 3>>Sanata yayi Tonon Silili

Naira Miliyan 70 Tsohon shugaban kasa, Obasanjo ya so baiwa kowannen mu a matsayin cin hanci dan mu barsa ya zarce a karo na 3>>Sanata yayi Tonon Silili

Duk Labarai
Sanata Olusola Adeyeye ya bayyana cewa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya yi yunkurin basu naira Naira Miliyan 70 kowannensu dan su bashi dama ya zarce akan kujerar mulki karo na 3. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na ChannelsTV ranar Lahadi inda yace an musu matsin lamba sosai akan su yadda Obasanjo ya zarce a karo na 3 inda aka hada musu hadda kudi. Adeyeye yace a lokacin Aminu Bello Masari ne kakakin majalisar kuma yana gode masa sosai da bashi kariya da yayi. Yace Masari yayi kamar yana tare da shugaban kasa amma a zahiri baya tare dashi, yace bayan da aka sha zanga-zanga da matsi da tattaunawa, 'yan majalisar sun ki amincewa da canja fasalin kundin tsarin mulki wanda zai ba tsohon shugaban kasar, Olusegun Obasanjo damar ci gaba da mulki wand...
Ban santa ba, Har Gaban Allah tazo ta yi karya, Fasto ya nesanta kansa da matar data ce addu’arsa tasa ta yi kudi amma daga baya aka ganta tana saida lemu

Ban santa ba, Har Gaban Allah tazo ta yi karya, Fasto ya nesanta kansa da matar data ce addu’arsa tasa ta yi kudi amma daga baya aka ganta tana saida lemu

Duk Labarai
A jiyane dai muka ga wata mata data fito take ikirarin fasto Ebuka Obi na cocin Zion Prayer Movement Outreach ya mata addu'a inda daga Dubu dari uku da take dashi har ta sayi gidan Naira Miliyan 500. Saidai daga baya an ga matar na sayar da lemu wanda lamarin ya baiwa mutane mamaki akai ta yada hotunan ta i da aka rika zargin faston da hada baki da ita dan ya nuna addu'ar sa na aiki. Saidai da yake martani game da lamarin, Fasto Ebuka Obi yace bai san matar ba kuma babu wani a cocinsa da ya santa inda yace har gaban Allah ta zo ta yi karya. Yace dama a baya ya fada cewa, sunansa zai ta yawo a kafafen yada labarai nan ba da dadewa ba akan labarin karya.
An kubutar da daya daga cikin daliban da aka yi gàrkùwà dasu a jami’ar FUDMA jihar Katsina

An kubutar da daya daga cikin daliban da aka yi gàrkùwà dasu a jami’ar FUDMA jihar Katsina

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Katsina na cewa, jami'an tsaro sun kubutar da daya daga cikin dalibai 4 da aka yi garkuwa dasu daga jami'ar FUDMA dake Dutsimma jihar Katsina. Hakanan rahoton yace ana kan kokarin kubutar da sauran dalibai 3 din da suka rage a hannun masu garkuwa da mutanen. Dalibin da aka kubutar shine Fahad Muhammad me shekaru 20 dake tsangayar kimiyyar Kwamfuta aji daya. Kuma an kubutar dashine ranar lahadi bayan bin sahun 'yan Bindigar. Sauran daliban da suka rage sune Adewale Bolaji Ajayi, 23, Emmanuel Michael, 24, da Favour Michael, 22. Dukansu daliban suna ajinsu na farko ne a jami'ar.
Kalli bidiyo inda Shiekh Adam Muhammad Dokoro yace Idan akwai wanda ya taba yin Zina ya tashi tsaye a wajen wa’azinsa

Kalli bidiyo inda Shiekh Adam Muhammad Dokoro yace Idan akwai wanda ya taba yin Zina ya tashi tsaye a wajen wa’azinsa

Duk Labarai
Babban malamin Islama, Shiekh Adam Muhammad Dokoro ya nemi idan akwai wanda ya taba yin zina ya mike tsaye. Sai dai babu wanda aka samu ya mike. https://www.tiktok.com/@mhaliru92/video/7477552048578284806?_t=ZM-8uNPYcIktPh&_r=1 Dan haka yace idan mutum yana yi ya daina ya tuba dan idan bai daina ba sai ya mike a gaban Allah. Kalli Bidiyon anan