YANZU-YANZU: Gwamna Bago Ya Sanya Dokar Ta Baci A Garin Minna Biyo Bayan Rikìçe-Ŕikicen Ta Ta’ďdançi
Gwamnan jihar Neja, Umaru Mohammed Bago, ya sanya dokar taƙaita zairga-zirgar baburan haya daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe a Minna babban birnin jihar sakamakon yawaitar rikicin 'yan daba a birnin.
A cewar gwamnan, yanzu haka an takaita zirga-zirgar 'yan acaɓa da babura masu ƙafa uku a wannan tsakanin.
Bago ya bayyana hakan ne yayin wani muhimmin taron tsaro da masu ruwa da tsaki suka yi da sarakunan gargajiya da shugabannin hukumomin tsaro a gidan gwamnati yau Talata.
''Babu wanda zai sake ɗaukar kowane irin nau'i makami a garin Minna. Ina bai wa jami'an tsaro umarni, duk mutumin da kuka gani da makami ku ɗauke shi a matsayin ɗanfashi da makami.'' in ji shi.
Ya bayyana cewa sabon matakin na da nufin daƙile matsalolin tsaro da ke ƙara taɓarɓarewa a babban birnin jihar.
...








