Sunday, February 22
Shadow

Duk Labarai

Babu maganar tattaunawa, ba zamu rage ko sisi a karin kudin kiran da muka yi ba>>Kamfanonin Sadarwa Irin su MTN, Airtel suka bayyana

Babu maganar tattaunawa, ba zamu rage ko sisi a karin kudin kiran da muka yi ba>>Kamfanonin Sadarwa Irin su MTN, Airtel suka bayyana

Duk Labarai
Kungiyar kamfanonin sadarwa ta bayyana cewa babu wani abu da zai sa su rage karin farashin kudin kiran waya da kaso 50 da gwamnati ta amince musu. Kamfanonin sun nemi yin karin kaso 100 bisa 100 amma hukumar sadarwa ta NCC ta amince musu da yin karin kaso 50 cikin 100. Wannan karin ne yasa kungiyoyin fafutuka suka ce basu amince dashi ba dan zai saka mutane a cikin wahala. Saidai shugaban kungiyar masu kamfanonin sadarwa ta Najeriya Gbenga Adebayo yace ba zasu rage ko sisi a cikin kaso 50 din da suka kara ba. Yace ragin zai zama kamar mutum ne dake bukatar numfashi amma a ki bashi, yace muddin ana son ci gaba da samun sabis me karfi da dorewa da kuma kara fadada ayyukansu to sai an bari an yi wannan kari.
Da Duminsa: Kungiyar kwadago ta NLC ta fasa zanga-zanga kan karin kudin kiran waya

Da Duminsa: Kungiyar kwadago ta NLC ta fasa zanga-zanga kan karin kudin kiran waya

Duk Labarai
Kungiyar kwadago ta NLC ta fasa yin zanga-zanga data shirya kan karin kudin kiran waya da kaso 50. A ranar Talata ne dai Kungiyoyin na kwadago da sauran na fafutuka suka shirya zanga-zanga dan nuna adawa da wannan kari. kungiyoyin sun bayyana dakatar da zanga-zangar ne bayan ganawa da wakilan Gwamnatin tarayya a ranar Litinin a ofishin Sakataren gwamnatin tarayya a Abuja. Shugaban kungiyar kwadagon Joe Ajaero yace sun dakatar da zanga-zangar ta yaune saboda gwamnati ta amince ta kafa kwamiti na musamman da zai duba kowane bangare dan samar da mafita akan lamarin.
Da Duminsa:Shugaba Tinubu ya amince da kafa jami’ar Kimiyyar Muhalli a Ogoni jihar Rivers

Da Duminsa:Shugaba Tinubu ya amince da kafa jami’ar Kimiyyar Muhalli a Ogoni jihar Rivers

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sakawa kudirin dokar kafa jami'ar kimiyyar Muhalli a Ogoni dake jihar Rivers, Niger Delta. Shugaban ya sakawa dokar hannu ne a fadarsa dake Abuja da yammacin ranar Litinin. Shugaban yace wannan babbar nasara ce a kokarin Najeriya wajan kawo ci gaban muhalli, Ilimi, da ci gaba me dorewa. Yace wannan jami'a na nuni da cewa gwamnati ta damu da ci gaban al'ummar yankin gaba daya inda yace shekaru da yawa mutanen yankin na ta fafutukar ganin sun samawa kansu mafita ta bangaren gyaran muhalli. Shugaban ya kuma jinjinawa majalisar tarayya bisa kokarin amincewa da wannan kudirin dokar. Ya kuma jawo hankalin masu ruwa da tsaki da suka hada da matasa, iyaye, da masu zaman kansu da su goyawa wannan jami'a baya.
Ji abinda Ma’aikatan hukumar KNUPDA na Kano suka yi bayan kkisan mutane 4 a Kano

Ji abinda Ma’aikatan hukumar KNUPDA na Kano suka yi bayan kkisan mutane 4 a Kano

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, ma'aikatan hukumar KNUPDA dake kula da gidaje a Kano sun tsere daga ofisoshinsu bayan kisan mutane 4 a Rimin Auzinawa, Ungoggo, Jihar Kano. Gidaje kusan 40 ne aka sakawa fentin rusau. Jaridar Daily Trust tace ta kai ziyara hukumar dan tattaunawa da jami'anta dan jin ba'asin yanda lamarin ya faru amma bata iske kowa ba sai ma'ikaci daya. Kuma ya shaidawa jaridar cewa, tsoron kawowa hukumar harine yasa ma'aikatan hukumar suka tsere suka dauke motoci da sauran ababen hawansu. Jaridar ta Daily Trust ta kuma kara ruwaito cewa, jami'in hukumar ta KNUPDA ya shaida mata cewa, ba sune suka je suka yi wancan rusau din ba da ya jawo asarar rayuka.
Kalli Bidiyon yanda jami’an tsaro suka kkashe mutane 4 a Rimin Auzinawa Kano,”Abba kaci Taliyar Karshe”

Kalli Bidiyon yanda jami’an tsaro suka kkashe mutane 4 a Rimin Auzinawa Kano,”Abba kaci Taliyar Karshe”

Duk Labarai
Wannan bidiyon yanda lamarin rikicin rusau ya faru ne a jihar Kano inda Rahoton Daily Trust yace jami'an tsaro sun kashe mutane 4. Lamarin ya farune a Rimin Auzinawa inda aka rushe gidajen mutane su kuma suka mayar da martani ta hanyar jifar jami'an tsaron. https://twitter.com/Mk__maitama/status/1886337089412714757?t=zdl2zRvXaG1ctDykEILFMw&s=19 Su kuma jami'an tsaron sun bude wuta inda hakan yayi sanadiyyar kisan mutane 4. Kalli Bidiyon faruwar lamarin anan
Kalli Bidiyon cikakkiyar hirar da aka yi da matar marigayi Albani Zaria

Kalli Bidiyon cikakkiyar hirar da aka yi da matar marigayi Albani Zaria

Duk Labarai
Matar marigayi Sheikh Albani Zaria ta fito ta yi cikakken bayani kan matsalar da suke ciki game da 'yan damfara da kuma daliban malamin. A wani Bidiyo da ya yadu sosai a kafafen sada sumunta, an ga me dakin Albani tana zubar da hawaye saboda bakin cikin da ta samu kanta a ciki. https://youtu.be/3U7poakQT3k?si=uqg92n2W86Sf8Kn8 Da yawan mutane sun tausayawa iyalan malam inda aka rika tambayar ina dalibansa da sauran malamai 'yan uwansa? Kalli Bidiyon anan
Tonon Silili: An kama basarake da karbar Naira Miliyan 1.5 ya baiwa ‘yan Bìndìgà masauki a masarautarsa

Tonon Silili: An kama basarake da karbar Naira Miliyan 1.5 ya baiwa ‘yan Bìndìgà masauki a masarautarsa

Duk Labarai
Mahukunta a jihar Taraba sun kama wani basaraken jihar da karbar Naira Miliyan 1.5 ya baiwa 'yan Bindiga mafaka a masarautarsa. Mutane 23 ne aka kama ciki hadda wasu mata 4 wanda ake zargin basarakenne ke basu mafaka. Basaraken ya karbi kudinne dan baiwa 'yan Bindigar mafaka, kamar yanda sanarwar ta tabbatar. Sojoji sun kashe daya daga cikin 'yan Bindigan da kuma kwati makamai ciki hadda Bindigar AK47. Lamarin ya farune ranar Lahadi, 2 ga watan Janairu a kauyen Angwan-Bala dake kamar Hukumar Karim Lamido ta jihar. Kakakin rundunar sojin dake jihar ta taraba, Captain Oni Olubodunde ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace 'yan Bindigar sun tserone daga jihar Filato inda suka nemi mafaka a wajan basaraken.
Kalli Bidiyon mawakiyar Najeriya me shigar banza, Tiwa Savage tana waka a Kasar Saudi Arabia

Kalli Bidiyon mawakiyar Najeriya me shigar banza, Tiwa Savage tana waka a Kasar Saudi Arabia

Duk Labarai
Mawakiyar Najeriya wadda ta shahara wajan nuna tsiraici, Tiwa Savage ta je Jedda kasar Saudiyya inda ta yi waka. A baya dai 'yar shekaru 44 din har sai da bidiyonta ya bayyana inda aka ganta wani yana lalata da ita. Saidai a ziyarar data kai jedda, wadi abinda ya dauki hankula shine yanda aka ga tayi shiga data rufe mafi yawan jikinta, ba kamar yanda ta saba a baya ba. An ga larabawa da iyalansu suna daukar hotuna da ita bayan wasan. kalli Bidiyon anan Kallo karin bidiyon anan Ga wani Kuma:
Kalli Hotuna:Yanda aka ceto wata Budurwa da saurayi ta ya mata tsìràrà ya daureta dan yin tsafi a dakin Otal

Kalli Hotuna:Yanda aka ceto wata Budurwa da saurayi ta ya mata tsìràrà ya daureta dan yin tsafi a dakin Otal

Duk Labarai
Wata budurwa ta tsallake rijiya da baya biyo bayan bin saurayinta da ta yi zuwa Otal. Budurwa ta hadu da saurayinne a kafar sada zumunta inda ya bayyana mata cewa shi ma'aikacin kamfanin man fetur ne inda suka yi mahada a wani Otal dake Abuja. Masu otal din sun bayyana cewa, mutumin ya bayyana sunansa da cewa, shi Emmanuel Okoro ne kuma daga jihar legas yake. Ita kuma budurwar sunanta Promise Eze daga jihar Ebonyi. An isketa a dakin Otal daure a jikin kujera bayan da ma'aikatan Otal din suka kira 'yansanda. Bayan da aka kwaceta aka kaita Asibiti ta dawo hayyacinta, ta bayyana cewa mutumin ya ce mata sunansa, Michael Prince. Kakakin 'yansandan babban birnin tarayya, Abuja, SP Josephine Adeh ta tabbatar da faruwar lamarin inda tace suna kan neman wanda ake zargi...