Thursday, March 12
Shadow

Duk Labarai

An fara bincike kan harin da B0k0 Hàràm ta kai kan sojoji a Borno

An fara bincike kan harin da B0k0 Hàràm ta kai kan sojoji a Borno

Duk Labarai
Rundunar tsaron Najeriya ta ƙaddamar da bincike kan harin da ƴan Boko Haram suka kai wa sojojin ƙasar a sansaninsu da ke jihar Borno a arewa maso gabashin ƙasar. Rahotanni sun ce harin na Boko Haram ya yi ajalin aƙalla sojojin Najeriya shida a sansanin sojojin da ke Damboa a ranar Lahadi, kamar yadda kafar AFP ta ruwaito, inda ta ce tsagin Boko Haram na ISAWP ne suka kai harin. Kakakin rundunar tsaron Najeriya, Manjo Janar Edward Buba ya tabbatar da harin, amma bai bayyana adadin waɗanda aka kashe ba. Sai dai ya ƙara da ecwa, "mun fara bincike kan lamarin. Za mu fitar da sanarwa game da harin nan kusa," kamar yadda ya bayyana wa BBC.
Gwamnan jihar Bauchi ya sallami Kwamishinoni 5

Gwamnan jihar Bauchi ya sallami Kwamishinoni 5

Duk Labarai
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad ya sallami kwamishinoni 5 daga gwamnatinsa a kokarin yin garambawul da inganta tafiyar da mulki. Me magana da yawun gwamnan, Mukhtar Gidado ne ya bayyana haka a sanarwar da ya fitar ranar Talata. Kwamishinonin da aka sauke sune; Dr. Jamila Dahiru (Education) Abubakar Bununu (Internal Security and Home Affairs) Usman Danturaki (Information and Communication) Prof. Simon Yalams (Agriculture) Yakubu Hamza (Religious Affairs and Societal Reorientation) Gwamnan yace ya godewa kwamishinonin bisa gudummawar da suka bayar wajan nasarorin da aka samu a gwamnatinsa. Sannan ya bayar da sunayen sabbin kwamishinoni 8 ga majalisar jihar dan tantancewa, wadanda aka bayar da sunayen nasu sune kamar haka: Isa Tilde Abdullahi Mohamm...
Ban damu da zagin da ake min ba, gyaran Najeriya ne a gabana>>Shugaba Tinubu

Ban damu da zagin da ake min ba, gyaran Najeriya ne a gabana>>Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa yana sane da irin maganganun da ake fadi akansa amma duk basu dameshi ba saboda gyaran Najeriya ne a gabansa. Ya bayyana hakane yayin ganawa da dattawan yankin Inyamurai na kudu maso gabas a ziyarar aiki da ya kai yankin ranar Asabar. Shugaban yace yasan irin aikin da ya nema kuma yasan za'ayi ta zaginda da maganganu marasa dadi, yace amma ya toshe kunnensa. Shugaban yace cire tallafin ma da yayi duk da akwai zafi amma ya zama dole dan a samu kudin gyara kasa, musamman dan manyan gobe su ji dadi.
Gwamnatin tarayya ta ware Naira Biliyan 100 dan ciyar da yara ‘yan Makaranta a shekarar 2025

Gwamnatin tarayya ta ware Naira Biliyan 100 dan ciyar da yara ‘yan Makaranta a shekarar 2025

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya a cikin kasafin kudin shekarar 2025 ta ware Naira Biliyan 100 dan ciyar da yara 'yan Makarantar Firamare. Tsarin ciyarwar an fito dashi ne dan kawar da matsalar rashin samun abinci me gina jiki da yaran ke fama da ita da kuma karfafa ilimi da karfafa gwiwar manoma. A kokarin inganta tsarin, Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, zata yi kokarin ganin an magance matsalolin shirin kama daga rashin biyan masu aikin da manoma da rashin baiwa daliban abinci me kyau.
Jamb ta samu kudin shiga Biliyan 22.9 inda ta baiwa gwanatin tarayya Naira Biliyan 6

Jamb ta samu kudin shiga Biliyan 22.9 inda ta baiwa gwanatin tarayya Naira Biliyan 6

Duk Labarai
Hukumar shirya jarabawar shiga jami'a ta Jamb ta sanar da cewa ta baiwa gwamnatin tarayya kudi shiga da suka kai Naira Biliyan 6 a shekarar 2024. Kakakin JAMB, Dr Fabian Benjamin ne ya bayyana haka a sanarwar da ya fitar ranar Litinin inda yace sun samu jimullar kudin shiga da suka kai Naira N22,996,653,265.25 a shekarar 2024 din. Yace sun baiwa Gwamnatin tarayya Naira N6,034,605,510.69 daga cikin kudin. Sanarwar tace kudin da suka baiwa gwamnatin tarayya rara ce da suka samu bayan kammala aikin shirya jarabawar ta shekarar 2024 da cire duk wasu kudade da suka kamata. Ya kara da cewa a cikin shekaru 7 da suka gabata, sun baiwa Gwamnatin tarayya jimullar kudaden shiga da suka kai naira Biliyan 50.
Baku da Godiyar Allah>>Shugaban kasar Faransa ya caccaki shuwagabannin kasashen Africa

Baku da Godiyar Allah>>Shugaban kasar Faransa ya caccaki shuwagabannin kasashen Africa

Duk Labarai
Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron ya caccaki shuwagabannin kasashen Africa inda yace basu da godiyar Allah. Ya bayyana hakane yayin da yake tattauna ci gaban da aka samu a yankunan Africa. Yace tun shekarar 2013 suka girke sojojinsu inda suke taimakawa wajan yaki da ta'addanci da kuma magance matsalar juyin mulki da aka rika samu a wasu kasashen African. Yace ba dan taimakon da suka bayar ba da wasu kasashen African yanzu ba kasashe bane sun dade da arwatsewa. Yace amma shuwagabannin African basa ganin irin kokarin da kasar Faransar take musu, sojojinsu na sadaukar da rayuwarsu, amma ba'a godewa. Idan dai za'a iya tunawa, kasar Nijar ta kori sojojin faransa daga cikinta.
Shugaba Tinubu ya amince a rika baiwa manyan sojojin da suka ajiye aiki Naira Miliyan 34 duk shekara da canja musu motoci duk bayan shekara 4

Shugaba Tinubu ya amince a rika baiwa manyan sojojin da suka ajiye aiki Naira Miliyan 34 duk shekara da canja musu motoci duk bayan shekara 4

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sakawa sabuwar dokar canja fasalin biyan manyan sojoji da suka ajiye aiki hakkokinsu. A sabuwar dokar, Soja da ya aije aiki yana da mukamin CDS, za'a rika bashi Dala dubu $20 duk shekara na kula da lafiyarsa a kasar waje, sannan za'a bashi mota jif wadda harsashi baya hudata, kuma hukumar soji ce zata rika kula da motar sannan bayan duk shekara hudu za'a rika canja mai motar. Sannan za'a bashi mota Peugeot 504 ko wata kwatankwacinta sannan kuma za'a bashi ma'aikata 5, da suka hada da masu dafa abinci 2, me ban ruwan fulawa, da wasu karin masu hidima biyu. Zakuma a bashi me gadi mutum daya da Mataimaki na musamman guda daya, sai direbobi 3, sannan kuma duk sanda yake bukatar karin jami'an tsaro, za'a bashi. Sannan kuma zai ci gaba da rike bin...
Kwankwaso ba zai yi nasara a zaben 2027 a Kano ba>>Inji Ganduje

Kwankwaso ba zai yi nasara a zaben 2027 a Kano ba>>Inji Ganduje

Duk Labarai
Shugaban Jam'iyyar APC ta kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa, Mutanen Kano ba zasu sake goyawa Kwankwaso baya ba. Yace ko da a 2023 ma rikicin cikin gida na Jam'iyyar APC ne yasa Kwankwaso yayi nasara a zaben, yace amma wanda suka zabi Jam'iyyarsa ta NNPP a yanzu suna nadama. Ya bayyana hakane a wajan taron karrama jiga-jigan Jam'iyyar da aka yi inda shugaban APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas ya wakilceshi. Ganduje yace yakan yi mamaki idan yaji Kwankwaso na cewa yana da goyon bayan mutanen jihar, yace gashinan Gwamna Abba Kabir Yusuf ma duk a rude yake bai san abinda ke tafiya a gwamnatinsa ba. Ganduje yayi kira ga 'yan Jam'iyyar ta APC da su hada kansu inda yace ta hanyar hakane musamman zasu samu nasarar kwace Jiyar daga hannun NNPP.