Gwamnatin Tarayya ta amince ta biya sama da Naira dubu 60 a matsayin mafi karancin Albashi
Gwamnatin Najeriya ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da kungiyoyin kwadagon NLC da TUC a wani taron gaggawa da ta gudanar a ranar Litinin karkashin jagorancin sakataren gwamnatin kasar, George Akume a wani yunkuri na kawo karshen yajin aikin sai abinda hali ya yi da kungiyoyin kwadagon suka fara a wannan rana.
Bangarorin biyu sun shafe sa’oi biyar zuwa shidda suna tattaunawa da juna kuma a karshe sun cimma matsaya a kan wasu batutuwa.
Ministan yada labaran kasar Mohammed Idris ya shaida wa BBC cewa gwamnati ta amince ta yi kari a kan naira dubu 60 wanda shi ne sabon albashin mafi karanci na ma’aikata da ta gabatar wa kungiyoyin kwadagon tun farko, wanda suka yi fatali da shi.
Ministan ya yi ikirarin cewa a karkashin yarjejeniyar da suka cimma kungiyoyin kwadagon sun amince su ...







