A kasuwar canji ta gwamnati a ranar Alhamis, farashin Naira ya fadi inda aka sayi dalar Amurka akan Naira N1,650.20.
Hakan na zuwa ne a yayin da tsadar rayuwa ta addabi 'yan Najeriya.
Tashi da faduwar farashin dala na daya daga cikin abubuwan dake kawo hauhawa da faduwar darajar Naira.
Gwamnatin tarayya ta gabatar da kasafin kudin Naira Tiriliyan N47.9trn a matsayin kasafin kudin shekarar 2025.
Ministan kasafin kudi da tsare-tsare, Atiku Bagudu ne ya bayyana haka ga manema labarai a ranar Alhamis bayan zaman majalisar zartaswa.
Yace nan da ranar Juma'a ko Litinin ake tunanin gabatarwa da majalisar tarayya da kasafin kudin a hukumance.
An gano wani gidan Alfarma na miliyoyin daloli da tsohon me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro Sambo Dasuki ya saya a kasar Amurka.
Sambo Dasuki dai an kamashi bisa zargin cinye Biliyoyin kudade da aka ware dan yaki da kungiyar Boko Haram a zamanin gwamnatin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.
Sannan a wannan sabon bincike da ya bayyana an gano Dasuki yayi amfani da kudaden wajan sayen godajen Alfarma a biranen Los Angeles, California da kuma babbar unguwar masu kudi ta McLean, Virginia, dake babban birnin kasar Amurka, Washington, DC.
Wata kungiya dake bincike da kwarmaton yanda ake sace kudaden talakawa a kasar Afrika me suna (PPLAAF) ce ta gano lamarin.
Kungiyar tace wasu dake taimakawa Dasuki sayen gidajen alfarmar Robert da Mimie Oshodin sun karbi akalla Da...
Rahotanni sun ce biyo bayan karuwar yawan man fetur din da kamfanin man fetur na kasa NNPCL ya sanar da cewa an samu na ganga Miliyan 1.8 duk kullun, yawan kudin da gwamnatin tarayya ke samu zai karu zuwa Naira Tiriliyan N6.99tn duk wata.
Farashin man Brent yana a matsayin dala $81 kowace ganga. Idan ana samun ganga Miliyan 1.8 kullun hakan na nufin Najeriya zata samu kudin shiga da suka kai Naira Tiriliyan N6.99tn duk wata.
Shugaban kamfanin man fetur dun na kasa, Mele Kolo Kyari ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis inda yace yawan man fetur din da Najeriya ke hakowa ya karu.
Masu gudanarwa na makarantar jami'ar Federal University, Lokoja, dale jihar Kogi, sun sallami malamai 4 daga aiki saboda samunsu da aikata ba daidai ba wajan jarabawa da kuma yin lalata da dalibai mata.
Sun zartar da wannan hukunci ne ranar Alhamis bayan wani zama da suka yi kan batun.
Hakan ya biyo bayan zargin da akawa malaman na yin lalata da dalibai mata da kuma aikata ba daidai ba wajan jarabawa.
Shugaban kwamitin gudanarwar makarantar, Senator Victor Ndoma-Egba ya yabawa wadanda suka yi wannan bincike inda yace sun kyauta da suka bi ka'ida wajan yin binciken.
Yace kuma su gaggauta kammala sauran binciken da ake yo akan malamai.
Ya jawo hankalin malaman kada su saka kansu wajan cin zarafin dalibai sannan ya jawo hankalin daliban da duk wanda aka ci zarafinsa da ya fito ...
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesome Wike ya gayawa Alhaji Atiku Abubakar cewa ya daina neman takarar shugabancin Najeriya dan ba zai samu ba saboda Allah be kaddaro masa zai mulki Najeriya ba.
Wike ya bayyana hakane ta bakin kakakinsa, Lere Olayinka inda ya kara da cewa, laifuka da cin amanar da yawa jam'iyyar PDP ne a baya ke tambayarsa.
Yace ya kamata Atiku ya gane cewa shi yanzu ya zama uba dan a lokacin da yayi takara a jami'iyyar SDP Wike bai wuce shekaru 25 ba.
Dan haka yace Atikun ya hakura dan a shekarar 2027, PDP ba zata sake bata tikitin takarar shugaban kasarta ta baiwa wanda ba zai ci zabe ba dama.
Masu bincike sun ce an samu ƙarin waɗanda suka kamu da ciwon suga daga shekara ta 1990.
Binciken ya nuna cewa an samu ƙarin daga kashi 7 zuwa kashi 14 na manya da suka kamu da ciwon.
Zuwa yanzu akwai mutane miliyan 800 da suka kamu da ɗaya daga cikin nau'ukan ciwon suga.
Masu binciken sun gano cewa cutar na haifar da yanke gaɓa da ciwon zuciya da ciwon ƙoda da rashin gani da kuma mutuwa.
Sun ƙara da cewa mutanen da suka fi kamuwa da cutar sun fito ne daga ƙasashe masu tasowa, inda samun magani ya ke da matuƙar wahala.
Waɗanda suka gudanar da binciken sun ƙara da cewa abinci marasa inganci ne sahun gaba cikin abubuwan da ke haifar da ciwon suga tsakanin manya.
Wasu ƴan bindiga haye kan babur sun yi garkuwa da wasu yara maza ɗalibai guda biyu da ke kan hanyarsu ta zuwa ƙaramar makarantar sakandire da ke garin Babban Duhu a ƙaramar hukumar Safana da ke jihar Katsina.
Wani malamin makarantar wanda ba ya son a ambaci sunansa ya shaida wa BBC cewa al’amarin ya faru ne da safiyar yau ɗin nan, inda ƴanbindigar suka yi awon gaba da yaran guda huɗu kafin daga bisani yara biyu su tsere.
Malamin ya ƙara da cewa "har kawo yanzu ba bu labarin cewa ƴanbindigar sun kira iyalan yaran domin neman kuɗn fansa."
Babu wani bayani da ya nuna cewa jami'an tsaro sun bi ƴanbindigar domin ceto yaran guda biyu da suka yi garkuwa da su. Sai dai jami'an tsaro da gwamnati sun sha fadin cewa suna samun nasara a kan ƴanbindigar.
An kashe mutum fiye da 1500 da sace fiye da 2000 a Najeriya - NHRC.
Hukumar kare haƙƙin bil-adama ta Najeriya, wato NHRC, ta bayyana cewa, tsakanin watan Janairu zuwa Satumba na wannan shekara, an sami aukuwar sace-sacen jama'a kusan 2000, aka kuma halaka wasu kusan 1500 a sassan kasar.
Jami'an hukumar ne suka bayar da wannan rahoto, a wajen wani taron tuntuɓa na kuniyoyin farar hula, kan halin da ake ciki game da batutuwan da suka shafi al'amuran kare hakkin bil'adama a kasar, wanda hukumar ta shirya tare da hadin gwiwar ƙungiyar tarayyar Turai, kuma aka gudanar yau a babban birnin tarayya Abuja.
Rahoton ya ce an sace mutum 1712 sannan an kashe mutum 1463 a wurare daban-daban na Najeriya, daga watan Janairu zuwa watan Satumba na bana.
Hukumar kare haƙƙin bil'adaman ta Naje...
Kamfanin mai na Najeriya NNPCL ya ce ya samu nasarar kai ga haƙo ɗanyen mai ganga miliyan ɗaya da dubu ɗari takwas a kowacce rana.
Shugaban Kamfanin Malam Mele Kyari ne ya bayyana hakan a yau Alhamis, yayin taron manema labarai da ya gudana a Abuja.
Ya ce alƙaluman da aka samu sun haɗa daga watan Yuni zuwa Nuwamban da muke ciki.
Kamfanin wanda cikin shekaru 15 da suka gabata ya yi ta fama da rashin taron na masu ruwa da tsaki, ya mayar da hankali ne kan harkokin kasuwancin masu zuba jari kuma hakan ya ja raguwar yawan gangar man da yake samarwa a kowacce rana.
Malam Mele ya ce suna ta fafutukar ganin yadda za su haɓaka yawan man da ake haƙowa domin ci gaban ƙasar da kuma saukakawa al'umma.
"An taɓa haƙo ganga miliyan biyu da dubu ɗari biyar a sehkarun baya, amma daga nan aka...