Yadda manoma ke kwana a gonaki domin gadin amfanin gonarsu a jihar Yobe
A Najeriya, ana ci gaba da nuna damuwa kan yadda tsananin sata ke tilasta manoma fara kwana a gonakinsu domin gadi saboda yadda ɓarayi suka addabe su da satar amfanin gonakinsu.
A jihar Yobe da ke yankin arewa maso gabas - inda aka samu rahoton ƙamarin lamarin - manoma da dama sun fara tarewa a gonakinsu ne musamman a cikin dare, wasu kuma aka tilasta musu su girbe amfanin ko da kuwa ba su isa girba ba saboda gudun kada su yi asara baki ɗaya.
Daga cikin ƙananan hukumomin da matsalar ta fi ƙamari akwai Gujiba, da Damaturu, da Gashuwa, da sauransu.
Lamarin ya kai ga wasu manoman na ɗaukar hayar mutane domin taya su gadi a gonakinsu, inda suke kwana ido biyu.
Wannan matsala ba za ta rasa nasaba da yanayin da ake ciki a Najeriya ba na tsadar rayuwa, da hauhawar farashin kayan masar...







