Daga cikin Naira Biliyan 13 da aka mana Alkawari na tallafi daga mutane daban-daban, Naira Biliyan 4.5 kadai suka shigo hannunmu>>Inji Gwamna Zulum
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa ya zuwa ranar Lahadin da ta gabata, gwamnatin jihar ta karɓi kusan naira biliyan huɗu da rabi daga cikin fiye da naira biliyan 13 da aka yi musu alƙawari a matsayin tallafi ga waɗanda ibtila'in ambaliya ya shafa a Maiduguri.
"...naira 4,441,494,902.81 ne suka shigo hannunmu daga cikin alƙawuran N13,195,500,000 da aka yi mana. Za mu ci gaba da sanar da jama'a duk lokacin da aka samu ƙarin shigowar kuɗi" In ji gwamna Zulum.
Farfesa Zulum ya bayyana hakan ne a lokacin da yake kafa kwamitin mutum 35 da zai kula da raba wannan tallafi ga waɗanda al'amarin ya shafa.
Wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Bukar Tijjani ya fitar, ya wallafa a shafin X na gwamna Zulum, gwamnan ya ce kwamitin zai ƙunshi wakilai daga hukumomi da ...








