Wednesday, January 7
Shadow

Duk Labarai

Harin Amurka da Birtaniya ya kashe mutum 14 cikin dare a Yemen

Harin Amurka da Birtaniya ya kashe mutum 14 cikin dare a Yemen

Tsaro
Gidan talabijin na Yemen da ke ƙarƙashin jagorancin ƴan Houthi ya ruwaito cewa an kashe mutum 14 ckin dare, yayin da aka jikkata mutum sama da 30 a lokacin wani hari ta sama da dakarun hadin gwiwa na Amurka da Birtaniya suka ƙaddamar. Cibiyar da ke bai wa dakarun Amurka umurni ta tabbatar da kai harin wanda ta ce na ramuwar gayya ne kan mayaƙan Houthi da ke kai hare-hare a kan jiragen ruwa masu sufuri ta tekun Bahar-maliya, lamarin da ke haifar da tsaiko wajen shigi da ficen kaya a duniya. Cibiyar ta ce makaman da ta harba sun faɗa kan inda suka ƙuduri kai harin guda 13, yayin da aka daƙile harin jiragensu marasa matuƙa takwas. A ƴan watannin nan mayaƙan Houthi na kai hare-hare cikin tekun Bahar-maliya, tekun da ake amfani da shi wajen jigilar kaya a fadin duniya, harin da suka ce...
‘Yansanda a jihar Anambra sun kashe daya daga cikin ‘yan IPOB da suka tursasa mutane su zauna a gida

‘Yansanda a jihar Anambra sun kashe daya daga cikin ‘yan IPOB da suka tursasa mutane su zauna a gida

Tsaro
'Yansanda sun kashe daya daga cikin masu tursasawa mutane zama a gida. An yi bata kashine tsakanin 'yansandan da mutanen wanda aka kashe daya, sauran suka tsere. Hukumar 'yansandan tace lamarin ya farune ranar 30 ga watan Mayu. Kuma ta kwace Bindiga kirar gida daga hannun daya daga cikin 'yan ta'addan inda sauran suka tsere, kamar yanda kakakin 'yansandan jihar, SP Tochukwu Ikenga ya tabbatar.
Zan kori duk ministan da baya aiki yanda ya kamata>>Shugaba Tinubu

Zan kori duk ministan da baya aiki yanda ya kamata>>Shugaba Tinubu

Siyasa
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, zai kori duk ministan da baya aiki yanda ya kamata. Tinubu ya bayyana hakane a ganawar da yayi da kungiyar dattawan Arewa ta ACF da yammacin ranar Alhamis. Yace zai ci gaba da yin aiki iya kokarinsa dan ci gaban Najeriya. Ya bayyana cewa, yana godewa 'yan majalisar zartaswarsa kan kokarin da suke amma zai rika dubawa yana tankade da rairaya dan gano wanda basa aiki yanda ya kamata dan canjasu.
Kalli Hotuna da bidiyon kisan wulakancin da ‘yan I-POB masu son kafa kasar Biafra sukawa sojojin Najeriya sannan suka kona motar sojojin a jihar Abia

Kalli Hotuna da bidiyon kisan wulakancin da ‘yan I-POB masu son kafa kasar Biafra sukawa sojojin Najeriya sannan suka kona motar sojojin a jihar Abia

Tsaro
Rahotanni sun bayyana cewa, wasu da ake kira da 'yan Bindigar da ba'a sansu ba, watau Unknown Gunmen, amma ana kyautata zaton 'yan kungiyar IPOB ne dake son kafa kasar Biafra sun kashe sojoji 2 a jihar Abia. Sun kashe sojojinne a wani shingen sojojin dake Obikabia jihar ta Abia a ranar tunawa da wadanda suka yi yakin Biafra. A wani bidiyo dake ta yawo a shafukan sada zumunta, an ga 'yan Bindigar bayan sun kashe sojojin suka kuma kona motarsu kurmus. Kalli Bidiyon a kasa: https://twitter.com/MaziEminent/status/1796136640034873771?t=HYb-5JLLECXTz_AC98Phxw&s=19 https://twitter.com/PIDOMNIGERIA/status/1796144862313468210?t=hzr4r1n221O86UTZxEnPQw&s=19 https://twitter.com/Tony_Ogbuagu/status/1796123554682966269?t=rFUU8b3uT0UElDumzNKfSQ&s=19 Tuni dai gwa...
Zamu fitar da matasa miliyan 50 daga Talauci>>Gwamnatin Tarayya

Zamu fitar da matasa miliyan 50 daga Talauci>>Gwamnatin Tarayya

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, zata fitar da matasa miliyan 50 daga Talauci. Ministan kimiyya da fasaha, Chief Uche Geoffrey Nnaji ne ya bayyana haka. Ya bayyana cewa, za'a saka kirkire-kirkiren da matasa ke yi a gida Najeriya cikin abubuwan da za'a rika kallo a matsayin abin afanarwa ga 'yan kasa. Ya bayyana hakane a Abuja wajan wani taro na musamman. Yace tattalin arziki na habakane idan aka ta'allakashi akan kirkire-kirkire da fasaha.
A yayin da shuwagabanni da ‘yan siyasar Najeriya basu damu ba, shugaban kasar Kenya yace shi ba mahaukaci bane, ba zai iya biyan Dala Miliyan 150 ya dauki hayar jirgin sama ba

A yayin da shuwagabanni da ‘yan siyasar Najeriya basu damu ba, shugaban kasar Kenya yace shi ba mahaukaci bane, ba zai iya biyan Dala Miliyan 150 ya dauki hayar jirgin sama ba

Siyasa
Shugaban kasar Kenya, William Ruto yace ba zai iya daukar hayar jirgin sama akan kudi dala Miliyan 150 ba ya dauki tawagarsa zuwa taro a kasar Amurka ba. Ya bayyana hakane a wajan wani taro da ya gudana a kasarsa. Ya bayyana muhimmancin yin tattalin kudin talakawa inda yace kuma ya kamata shi ya fara nuna alamar abinda yake kira akai, watau rashin almubazzaranci. A baya dai, shima shugaban kasar Kenyan an zargeshi da yin wadaka da kudin talakawa.
A kara yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu uzuri, duk matsalolin da ake fama dasu yanzu ya gajesu ne daga Gwamnatin Buhari>>Tsohon Gwamnan Kano Ganduje

A kara yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu uzuri, duk matsalolin da ake fama dasu yanzu ya gajesu ne daga Gwamnatin Buhari>>Tsohon Gwamnan Kano Ganduje

Siyasa
Shugaban jam'iyyar APC kuma tsohon Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya baiwa 'yan Najeriya hakuri inda yace su ci gaba da baiwa gwamnatin Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu uzuri. Yace matsalolin da ake fama dasu, Tinubu ya gajesu ne daga Gwamnatin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari. Ganduje ya bayyana hakane a wajan taron kaddamar da wani Littafi kan cika shekara 1 da gwamnatin Bola Ahmad Tinubu ta yi akan mulki. Ganduje ya kara da cewa, matakaj da Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yake dauka na kawo gyara aun fara nuna alamar nasara.
Bidiyo: Sabuwar Rawar da gwamnan Osun yayi ta dauki hankula

Bidiyo: Sabuwar Rawar da gwamnan Osun yayi ta dauki hankula

Duk Labarai
Sabuwar rawar da gwamnan Osun, Ademola Adeleke yayi ta dauki hankula a shafukan sada zumunta. Gwamna Adeleke ya shahara wajan rawa a guraren taruka da yake halarta. Gwamnan dai kawu ne ga shahararren mawakin Najeriya, Davido. A wannan karin ma ya sake taka rawar a wajan taron karrama mutane da jaridar Vanguard ta yi. Kalli Bidiyon a kasa: https://www.tiktok.com/@gbaramatuvoice/video/7372692648819215622?_t=8mnncGdWWP8&_r=1 Yayin da wasu ke yaba mai, wasu na ganin hakan bai dace ba a matsayinsa na gwamna.