Friday, January 9
Shadow

Duk Labarai

Hotuna:Kalli ta’addancin da ‘yan Kungiyar I-POB dake son kafa kasar Biafra suka yi na kona motoci da kashe mutane a jiya Laraba

Hotuna:Kalli ta’addancin da ‘yan Kungiyar I-POB dake son kafa kasar Biafra suka yi na kona motoci da kashe mutane a jiya Laraba

Tsaro
Rahotanni sunce a jiya, Laraba, 'yan Bindigar da ake kira da wanda ba'a sani ba amma ake kyautata zaton 'yan kungiyar IPOB ne dake son kafa kasar Biafra sun kai hari kan kasuwar Nkwo Ibagwa dake karamar hukumar Igbo-Eze South ta jihar Enugu. 'Yan bindigar sun rika harbi a iska wanda yayi sanadiyyar kisan wannan matashin da hotonsa ke kasa. 'Yan uwa da abokan arziki da yawa sun koka da rashin wannan matashi da aka yi inda da yawa suka hau shafukan Facebook suke alhinin rashin matashin. Hakanan rahoton Sahara Reports yace 'yan Bindigar sun kona kayan 'yan kasuwa da motoci wanda aka yi kiyasin sun kai na miliyoyin Naira.
Gwamnatin tarayya ta gayyaci kungiyar kwadago, NLC ta dawo a ci gaba da tattaunawa game da mafi karancin Albashi

Gwamnatin tarayya ta gayyaci kungiyar kwadago, NLC ta dawo a ci gaba da tattaunawa game da mafi karancin Albashi

Siyasa
A jiya Laraba, wasu majiyoyi sun bayyana cewa, Gwamnatin tarayya ta gayyaci kungiyar Kwadago ta dawo a ci gaba da tattaunawa kan maganar mafi karancin Albashi. A zama na karshe dai an tashi baram-baram bayan da NLC din taki amincewa da Naira dubu 60 a matsayin mafi karancin Albashi. Hakanan wata majiyar tace kungiyar kwadagon ta amince da cewa zata amsa gayyatar ta gwamnati. Kungiyar dai ta baiwa Gwamnati nan da karshen watan Mayu da muke ciki a gama maganar mafi karancin Albashin ko kuma ta tafi yajin aiki.
Jirgin kasa dake jigila tsakanin Kaduna zuwa Abuja ya taka tare da kashe yara mata tagwaye a jihar Naija

Jirgin kasa dake jigila tsakanin Kaduna zuwa Abuja ya taka tare da kashe yara mata tagwaye a jihar Naija

Duk Labarai
Jirgin kasan daya taso daga Abuja zuwa Kaduna ya kashe kananan yaran wanda tagwayene mata a karamar hukumar Tafa. Lamarin ya farune da misalin karfe 10 na safe ranar Asabar, kamar yanda jaridar The Cable ta ruwaito. Yaran, Hassana and Hussaina Baro shekarar su daya da watanni 6. Kakakin 'yansandan jihar Naija, Wasiu Abiodun ya tabbatar da daruwar lamarin. Yace yaran suna wasa ne akan titin jirgin kasan kamin lamarin ya faru.
Hotuna:Sojojin kasar Nijar sun kama kasurgumin dan Bindigar nan, Kachalla Baleri

Hotuna:Sojojin kasar Nijar sun kama kasurgumin dan Bindigar nan, Kachalla Baleri

Tsaro
Sojojin kasar Nijar sun kama kasurgumin dan Bindiga, Kachalla Baleri. Masanin harkar tsaro, Zagazola Makama ne ya bayyana hakan inda yace an kamashine a Rouga Kowa Gwani. Baleri wanda dan Shinkafine ya addabi mutane a Zamfara, Sokoto da Maradi. Ya jagorancin kisan mutane da yawa da kuma garkuwa da mutane da yawa. Yana daya daga cikin na hannun damar Kachalla Bello Turji kuma shine mutum na 40 mafi hadari da sojojin Najeriya suke nema ruwa a jallo.
Hotuna: Matashi Ya Raba Litattafai Gudu Dubu Goma Kyauta Ga Dalibai Domin Taya Gwamna Abba Murna Cika Shekara Guda Akan Mulki

Hotuna: Matashi Ya Raba Litattafai Gudu Dubu Goma Kyauta Ga Dalibai Domin Taya Gwamna Abba Murna Cika Shekara Guda Akan Mulki

Duk Labarai
Matashi Ya Raba Litattafai Gudu Dubu Goma Kyauta Ga Dalibai Domin Taya Gwamna Abba Murna Cika Shekara Guda Akan Mulki Shugaban Gidauniyar Sharu Sarakin Kwankwasiyya free computer training, Hon. Sharu Saraki ya rabawa dalibai littafin kimanin dubu goma domin taya Mai girma Gwamnan Kano Eng. Abba Kabir Yusuf murnar cika shekara daya akan mulki. Sannan kuma gidauniyar ta sake daukar nauyin dalibai mata ilimin kwamfuta kyauta a gidaunyar dake kan titin Airport road kusa da gidan man Danmarna kwanar kotun No-Man's-land.
YANZU-YANZU: Ga sabon taken Najeriya da za a koma yin amfani dashi daga yau dinnan:

YANZU-YANZU: Ga sabon taken Najeriya da za a koma yin amfani dashi daga yau dinnan:

Siyasa
YANZU-YANZU: Ga sabon taken Najeriya da za a koma yin amfani dashi daga yau dinnan: Wanda ya rubuta - Lilian Jean Williams (1960) wanda yayi kidansa - Franca Benda Ga Sabon Taken National Anthem din Nigeria ⤵️ Nigeria, we hail thee,Our own dear native land,Though tribe and tongue may differ,In brotherhood, we stand,Nigerians all, and proud to serveOur sovereign Motherland. Our flag shall be a symbolThat truth and justice reign,In peace or battle honour’d,And this we count as gain,To hand on to our childrenA banner without stain. O God of all creation,Grant this our one request,Help us to build a nationWhere no man is oppressed,And so with peace and plentyNigeria may be blessed. Ku bayyana mana ra'ayinku kan wannan mataki da shugaban kasa ya dauka na canja taken Najeriya....