Ba mu cimma yarjejeniya da gwamnati kan mafi ƙarancin albashi ba – NLC
Ƙungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta soki lamirin bayanin da shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya yi kan cewa an cimma matsaya game da sabon albashin ma'aikata mafi karanci a ƙasar.
Ƙungiyar ƙwadagon ta kuma dage kan buƙatarta ta neman sabon mafi karancin albashi na kasa ya kasance naira 250,000.
A yayin da yake jawabi a ranar Laraba, lokacin bikin ranar dimokuradiyya, Tinubu ya ce an cimma matsaya kan batun sabon mafi karancin albashin da aka dade ana muhawara a kai tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadago.
Shugaban ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba za a aika da wani kudirin doka na zartarwa ga majalisar dokokin ƙasar domin ta tsara sabuwar yarjejeniyar mafi karancin albashi.
Sai dai a wata sanarwa da NLC ta fitar a jiya Laraba, muƙaddashin shugaban NLC, Prince Adewale Adeya...







