Monday, June 29
Shadow

Duk Labarai

Alamomin ciwon ulcer

Duk Labarai
Menene cutar Ulcer? Cutar ulcer ko gyambon ciki, kamar yanda aka fi saninta da Hausa, ciwone dake samuwa a cikin dan adam ko kuma a cikin hanjinsa. Allah ya halicci wata kariya a cikin dan Adam. Kariyarce idan ta samu matsala, sai wasu sinadarai da jikin mutum ke samarwa na sarrafa abinci su ji mada ciwo a ciki ko a hancinsa. Ana iya maganin cutar ulcer cikin sauki. Amma idan aka barta ba tare da kulawa ba, tanawa mutum illa sosai. Abubuwan dake kawo cutar ulcer Abubuwan dake kawo cutar ulcer sun hada da: Cutar da Bakateriya ke sawa. Yawan shan magungunan Aspirin, ibuprofen, da naproxen. A likitance, abinci baya saka ulcer. Alamomin ciwon Ulcer Alamar ciwon ulcer ya danganta da tsananin ciwon. Mafi shaharar alamar ciwon ulcer itace jin zafi a tsakanin kirji ...
CIKIN HOTUNA: Rarara Ya Tallafawa Wasu daga cikin kin manoman Jihar Katsina, da Naira Miliyan Ashirin ( 20,000,000 ) Domin Suyi Chefanen Babbar Sallah

CIKIN HOTUNA: Rarara Ya Tallafawa Wasu daga cikin kin manoman Jihar Katsina, da Naira Miliyan Ashirin ( 20,000,000 ) Domin Suyi Chefanen Babbar Sallah

Duk Labarai
CIKIN HOTUNA: Rarara Ya Tallafawa Wasu daga cikin kin manoman Jihar Katsina, da Naira Miliyan Ashirin ( 20,000,000 ) Domin Suyi Chefanen Babbar Sallah. Anyi Taron Bada Tallafin Ne a Garin Kahutu Karamar Hukumar Danja Dake Jahar Katsina. Rabi'u Garba GayaMedia Aide To Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara.
Kotun Ƙolin Amurka ta amince da amfani da ƙwayoyin zubar da ciki

Kotun Ƙolin Amurka ta amince da amfani da ƙwayoyin zubar da ciki

Siyasa
Bakin Alƙalan Kotun Ƙolin Amurka yazo ɗaya wajen amincewa da amfani da ƙwayoyin zubar da ciki. Wani lamari da ake gani a matsayin nasara ga masu fafutukar 'yancin zubar da ciki. Kotun ta yi watsi da buƙatar ƙungiyoyin likitoci masu yaƙi da zubar da ciki da kuma 'yan gwagwarmaya da suke neman a taƙaita amfani da maganin Mifepristone. Kotun kolin ta ce ƙungiyoyin likitocin ba su da 'yanci shigar da ƙara kan hakan, kuma sun gaza gabatar da hujjojin cewa maganin Mifepristone yana cutarwa. Wannan ne babban hukuncin da kotun ta yanke, tun watsi da 'yancin zubar da ciki da kotun tarayyar ƙasar ta yi shekara biyu da suka gabata.

G7 ta amince a yi amfani da kadarorin Rasha da aka ƙwace a ƙasashen duniya

Siyasa
Ƙungiyar Ƙasashen G7 masu ƙarfin masana'atu sun amince a yi amfani da ribar kadarorin Rasha da aka ƙwace, domin bai wa Ukraine ta yi amfani da su. Biden ya ce yarjejeniyar za ta hada da tura bayanan sirri, da bai wa sojoji horo da bin dokokin NATO da zuba kuɗi a masana'antu da ke Ukraine domin ci gaba da samar da makamai. Biden ya ce burinsu shi ne samar wa Ukraine tsaro ''na gaske'', da kuma turmusa hancin Rasha da ƙawayenta a ƙasa. Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya ce wannan ba abu ne da Shugaba Putin zai kawar da kai ya kyale ba.
Ba za mu taɓa yin sulhu da ‘yan bindiga ba – Gwamnan Zamfara

Ba za mu taɓa yin sulhu da ‘yan bindiga ba – Gwamnan Zamfara

Duk Labarai
Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawan Dare ya jaddada ƙudurin gwamnatinsa na rashin yin sulhu da 'yan bindiga. Yayin da yake gabatar da jawabi bayan ya shiga wani tattaki da ƙungiyoyin matasan jihar suka shirya a wani ɓangare na bikin ranar Dimokradiyya, Gwamnan Dauda ya ce zai yi duk abin da ya dace domin maido da jihar kan turbar zaman lafiya. ''Jiharmu na da tarihin zaman lafiya, amma sannu a hankali abubuwa suka fara taɓarɓarewa, sakamakon ayyukan ɓata-gari'', inji gwamnan. Gwamnan ya ce matsalar tsaro matsala ce da ta shafi kowa da kowa, don haka ya yi kira ga al'ummar jihar su haɗa hannu wajen tabbatar da zaman lafiyar jihar. "A koyaushe ina faɗa ina maimaitawa bai kamata ka yi sulhu da kasasshe ba, mun ga yadda gwamnatocin da suka gabata suka yi yunƙurin sulhu da 'yan bindig...
Za a ci gaba da sauye-sauyen tattalin arziƙi duk da wahalhalun da ake fuskanta – Tinubu

Za a ci gaba da sauye-sauyen tattalin arziƙi duk da wahalhalun da ake fuskanta – Tinubu

Siyasa
Shugaban Najeriya Bola Tinubu, ya ce sauye-sauyen da gwamnatinsa ta yi ya zama dole wajen gyara tattalin arzikin kasar, duk kuwa da kara wahalhalun da ake fuskanta da ke janyo fushin jama'a. Tinubu ya bayyana hakan ne a jawabinsa na jiya a yayin bikin ranar dimokuradiyyar Najeriya. “Na fahimci matsalolin tattalin arziki da muke fuskanta a matsayinmu na kasa. Tattalin arzikinmu yana cikin tsananin bukatar gyara shekaru da yawa. Ba a daidaita shi ba saboda an gina shi a kan kura-kurai na dogaro da kudaden shigar da ake samu daga hako man fetur,” inji Tinubu. Tun bayan hawansa ƙaragar mulki a bara, Tinubu ya cire da tallafin man fetur wanda ya haddasa tashin gwauron zabin sufuri da farashin abinci da sauran kayayyakin masarufi a fadin kasar. Dubban ‘yan Najeriya ne suka fito kan t...
Ba mu cimma yarjejeniya da gwamnati kan mafi ƙarancin albashi ba – NLC

Ba mu cimma yarjejeniya da gwamnati kan mafi ƙarancin albashi ba – NLC

Siyasa
Ƙungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta soki lamirin bayanin da shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya yi kan cewa an cimma matsaya game da sabon albashin ma'aikata mafi karanci a ƙasar. Ƙungiyar ƙwadagon ta kuma dage kan buƙatarta ta neman sabon mafi karancin albashi na kasa ya kasance naira 250,000. A yayin da yake jawabi a ranar Laraba, lokacin bikin ranar dimokuradiyya, Tinubu ya ce an cimma matsaya kan batun sabon mafi karancin albashin da aka dade ana muhawara a kai tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadago. Shugaban ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba za a aika da wani kudirin doka na zartarwa ga majalisar dokokin ƙasar domin ta tsara sabuwar yarjejeniyar mafi karancin albashi. Sai dai a wata sanarwa da NLC ta fitar a jiya Laraba, muƙaddashin shugaban NLC, Prince Adewale Adeya...
Masu fama da kwalara na ƙaruwa a Najeriya

Masu fama da kwalara na ƙaruwa a Najeriya

Duk Labarai
Hukumar hana yaɗuwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta fitar da sanarwar fadakar da jama'a game da ƙaruwar kamuwa da cutar kwalara a fadin kasar yayin da damina ke ƙara kamari. An samu rahoton bullar cutar a jihar Legas a baya-bayan nan, lamarin da ya ƙara dagula al'amura. Daga ranar 1 ga watan Janairu zuwa 11 ga watan Yunin 2024, an samu jimillar mutum 1,141 da ake zargi da kamuwa da cutar kwalara da kuma 65 da aka tabbatar sun kamu da cutar, kuma mutum 30 sun ne suka mutu duk daga ƙananan hukumomi 96 a faɗin jihohi 30 sakamakon cutar. Jihohin da suka fi fama da cutar, waɗanda ke bayar da kashi 90% na yaɗuwar cutar sun hada da Bayelsa da Zamfara da Abia da Cross River da Bauchi da Delta da Katsina da Imo da Nasarawa da kuma Legas. Kungiyar kwararru kan hana yaɗuwar cuttutuka ta ka...
Ba faɗuwa na yi ba, na rusuna ne don girmama dimokuraɗiyya – Tinubu

Ba faɗuwa na yi ba, na rusuna ne don girmama dimokuraɗiyya – Tinubu

Siyasa
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya mayar da martani kan faduwar da ya yi lokacin bikin ranar dimokuraɗiyya ta 12 ga watan Yunin 2024. Bidiyon faduwar shugaban ya yaɗu a shafukan sada zumunta wanda ya nuna Tinubu a lokacin da yake yunkurin shiga motar faretin a dandalin Eagle Square da ke Abuja inda ya rasa wani mataki wajen hawar motar ya faɗi. Tinubu mai shekaru 72, ya ce dimokraɗiyya ta cancanci faduwa. Da yake magana game da abin da ya faru a ranar Laraba, shugaban ya yi dariya da cewa "na rusuna ne don girmama dimokraɗiyya" a salon Yarbawa. Shugaba Tinubu ya kuma yi amfani da taron liyafar cin abincin na bikin dimokraɗiyya wajen kira ga hadin kan Nijeriya, ba tare da la’akari da kabila ko addini ko siyasa ba. Ya kuma jaddada cewa hadin kan Najeriya ba abu ne da za a iya yi...