Sunday, January 12
Shadow

Duk Labarai

Ka yaudare mu ba haka muka yi da kai ba>>Kungiyar Kwadago ta NLC ta soki Shugaba  Tinubu kan karin kudin man fetur

Ka yaudare mu ba haka muka yi da kai ba>>Kungiyar Kwadago ta NLC ta soki Shugaba Tinubu kan karin kudin man fetur

Duk Labarai
Kungiyar kwadago ta NLC ta soki shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu kan Karin kudin man fetur din da aka yi inda ta zargeshi da yaudara. Kungiyar tace Tinubu ya yaudaresu suka amince da Naira dubu 70 a matsayin mafi karancin Albashi bisa alkawarin ba za'a kara farashin man fetur ba amma ya yaudaresu. Shugaban kungiyar, Joe Ajaero ya bayyana hakan a cikin sanarwar inda yace suna kiran a janye wannan kari ko su dauki mataki. Yace zasu ci gaba da kasancewa tare da mutane a kowane irin hali.
Ji abinda ‘yan Bindiga suka yi a Minna babban birnin jihar Naija da ya tayar da hankula

Ji abinda ‘yan Bindiga suka yi a Minna babban birnin jihar Naija da ya tayar da hankula

Duk Labarai
'Yan Bindiga a babban birnin jihar Naija watau Minna sun shiga wani rukunin gidaje me suna M.I Wushishi Estate inda suka lalata ababen hawa sannan suka yi gargadin a tashi daga gidan ko kuma idan suka dawo zasu kashe duk wanda suka iske. Wani shaidan gani da ido yace lamarin ya farune da rana tsaka. Yace maharan sun shiga rukunin gidajenne yayin da mazajen gidan ke wuraren aiki. Kakakin 'Yansandan jihar, Wasiu Abiodun ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace amma yanzu kura ta lafa.
Shekaru 18 da suka gabata Shugaban Tinubu yaso gina matatar man fetur a Legas>>Dangote

Shekaru 18 da suka gabata Shugaban Tinubu yaso gina matatar man fetur a Legas>>Dangote

Duk Labarai
Shugaban kamfanin Rukunin Dangote, Aliko Dangote ya bayyana cewa,shekaru 18 da suka gabata,Shugaban kasa,Bola Ahmad Tinubu yana da burin gina matatar man fetur a Legas. Yace amma sai gashi shi ya samu damar ginawa. Yace burinsa shine, ya saka Afrika da Najeriya Alfahari. Yace dalilin kujiba-Kujibar gina matatar man fetur dinsa gashi duk yayi farin gashi. Yace a baya bashi da farin gashi amma yana alfahari da samunsa.
Gwamnatin Tinubu ta bada umarnin a fara sayar da man fetur akan sama da Naira Dubu daya kowace lita

Gwamnatin Tinubu ta bada umarnin a fara sayar da man fetur akan sama da Naira Dubu daya kowace lita

Duk Labarai
Karamin ministan man fetur, Heineken Lokpobiri ya bayar da umarni a fara sayar da man fetur a sama da Naira Dubu daya watau sama da farashin da ake dauka a Depot wanda Naira 1117 ne. Ya bayyana hakane a wajan wani taro a Abuja. Yace ta hakane kawai za'a hana masu fitar da man fetur zuwa kasashen waje daga Najeriya. Ya kuma zargi jami'an tsaro da hannu wajan taimakawa masu safarar man fetur din daga Najeriya zuwa wasu kasashe alhalin 'yan Najeriya ne aka yi tallafi dominsu.
Kalli Bidiyo ya Bayyana: Bidiyon sanatan Najeriya yana lalata da matar aure ya watsu sosai a shafukan sada zumunta

Kalli Bidiyo ya Bayyana: Bidiyon sanatan Najeriya yana lalata da matar aure ya watsu sosai a shafukan sada zumunta

Duk Labarai
Tsohon sanata da ya wakilci mazabar Adamawa ta Arewa a majalisar tarayya,Sanata Elisha Abbo ya sake bayyana a wata badakala wadda ke da kamanceceniya da irin badakalolin da ya shiga a baya. Sanata Abbo a wannan karin Bidiyon sa ne ya bayyana yana lalata da wata matar aure me suna Mrs. Wange Minso Kwagga. https://www.tiktok.com/@arewa_newz/video/7409967862627994886?_t=8pPTXDCiDgb&_r=1 Bidiyon dai ya watsu sosai a kafafen sada zumunta abba saboda tsiraici dake cikinsa ba zamu iya nuna muku shi a shafinmu ba. https://www.tiktok.com/@arewa_newz/video/7409999845064199429?_t=8pPTFAc7QEI&_r=1 A bangaren matar, Mrs. Kwagga ta fito ta bayyana nadama akan abinda suka aikata ita da sanatan inda tace yayi amfani da halin matsin da take ciki ne ya cimma burinsa akanta. San...
Wata Sabuwa: Gwamnati na shirin kara farashin man fetur zuwa Naira 1,405 dan tatsar kudaden da zata biya bashin da ‘yan kasuwar man fetur ke binta

Wata Sabuwa: Gwamnati na shirin kara farashin man fetur zuwa Naira 1,405 dan tatsar kudaden da zata biya bashin da ‘yan kasuwar man fetur ke binta

Duk Labarai
Wani sabon rahoton da ya bayyana na nuni da cewa za'a kara farashin man fetur zuwa akalla Naira 1000 akan kowace lita. 'Yan kasuwar man fetur din ne suka bayyanawa jaridar Vanguard hakan a wata zantawa da ta yi dasu. Hakan na zuwane bayan da kamfanin man fetur na kasa,NNPCL ya koka da bashin da ya masa yawa na 'yan kasuwar man fetur da suke kawo man a matsayin bashi. 'Yan kasuwar dai da yawa wanda na kssa da kasa ne aun ce sun daina kawowa Najeriya mai a bashi har sai an biyasu bashin da suke bi. Hakan yasa gwamnati zata iya kara farashin man fetur din dan ta samu kudaden da zata biya wancan bashin da ake binta. Ko kuma ta raba ta biya rabi 'yan kasa su biya rabi, hakanan kuma hakan na nufin lallai fa sai an kara farashin man saboda a yanzu gwamnati bata da kudin da zata ci ...
An kama Boka bayan da ya baiwa wani mutum maganin bindiga kuma aka yi gwajin harba bindigar saidai maganin bai yi aiki ba, Mutumin ya mutu

An kama Boka bayan da ya baiwa wani mutum maganin bindiga kuma aka yi gwajin harba bindigar saidai maganin bai yi aiki ba, Mutumin ya mutu

Duk Labarai
Wani boka me suna Timothy Dauda dan kimanin shekaru 19 a jihar Edo da yayi ikirarin yana da maganin Bindiga ya shiga hannu. An kamashine bayan da ya gwada maganin Bindigar akan wani amma maganin bai yi amfani ba,Bindigar ta kamashi ya mutu. Lamarin ya farune a yankin Onumu dake karamar hukumar Àkókò-Edo A jihar ta Edo Kakakin 'yansandan jihar SP Moses Joel Yamu ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace wanda ake zargi zai fuskanci hukunci.