Abin Takaici: Ji yanda aka bar na’urar dake nuna inda ‘yan Bindiga suke ta lalace da gangan
Wani tsohon babban jami'in dansanda ya bayyana yanda aka bar na'urar dake nuna inda 'yan bindiga suke ta lalace.
Na'urar dai ana amfani da ita wajan sanin inda 'yan Bindiga suke a yayin da suka yi amfani da waya kuma a kamasu.
A baya an yi amfani da wannan na'ura wajan kama wadanda suka yi garkuwa da Olu Falae kuma aka kwace kudaden fansar da suka karba na Miliyan 5.
Saidai a yayin da Na'urar ke hannun kulawar 'yansanda kuma aka rika samun shuwagabannin 'yansanda daban-daban,wasu basu san ma yanda ake amfani da ita ba.
Yayin da wasu sun sani amma suka ki bayar da kudin da za'a rika sabuntata da kuma biyan kudin wata-wata na tabbatar da tana aiki.
Hakan yasa na'urar ta lalace aka daina amfani da ita kwata-kwata.
Hakanan na'urar a karshe komawa ta yi 'yan siyasa na amfani d...