Sunday, November 22
Shadow

Duk Labarai

Yanda Atiku Abubakar yayi yunkurin tsigeni dan ya zama shugaban kasa>>Inji Tsohon Shugaban kasa, Obasanjo

Yanda Atiku Abubakar yayi yunkurin tsigeni dan ya zama shugaban kasa>>Inji Tsohon Shugaban kasa, Obasanjo

Duk Labarai
Tsohon shugaban kasa, Janar Olusegun Obasanjo me murabus ya bayyana cewa mataimakinsa, Atiku Abubakar ya shirya tsigeshi dan ya sama shugaban kasa. Yace Atiku ya kira taro a ofis dinsa dake fadar shugaban kasa lokacin shi Obasanjon baya nan. Yace Atiku sun gana da Kakakin majalisa na wancan lokacin, watau Ghali Umar Na'abba inda ya bashi Naira Miliyan 5 sannan yace a fara shirin tsige Obasanjo. Yace shi kuma a wancan lokacin shugaban ma'aikatansa na fadar shugaban kasa ya nadarmasa duk abinda aka tattauna ya bashi yaji. Yace duk da haka Atiku bai hakura ba, yaci gaba da neman tsigeshi sannan aka rika daina mu'amala dashi aka rika samun Atiku a matsayin mataimakinsa.
Shugaba Tinubu ya kara yawan Rundunar sojojin Najeriya daga 8 zuwa 12, sannan ya amince a dauki Sabbin sojoji dubu Ashirin da takwas

Shugaba Tinubu ya kara yawan Rundunar sojojin Najeriya daga 8 zuwa 12, sannan ya amince a dauki Sabbin sojoji dubu Ashirin da takwas

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya amince da fadada Hukumar sojojin Najeriya inda ya fadada rundunar daga 8 zuwa 12. Me magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a wata sanarwa inda yace shugaba yayi hakanne dan inganta bangaren tsaro. sannan yace Shugaba Tinubu ya amince a dauki karin sojoji dubu ashirin da takwas da kuma amincewa a siyo makamai dan inganta tsaro. Ga yanda sabbin rundunar sojojin zata kasance kamar haka: 1 Division Headquarters – Kaduna (Kaduna, Kano, Katsina and Jigawa States) 2 Division Headquarters – Ibadan (Oyo, Osun, Ekiti and Ondo States) 3 Division Headquarters – Jos (Plateau, Bauchi and Gombe States) 5 Division Headquarters – Makurdi (Benue, Nasarawa and Kogi States) 6 Division Headquarters – Port Harcourt (Rivers, ...
Tonon silili: Na rantawa Gwamnan Kaduna, Uba Sani Naira Miliyan 30 yayi yakin neman zabe da alkawarin zai mayar da Naira Miliyan 100 idan ya zama gwamna amma yanzu ya hanani kudina>>Inji Ummi El-Rufai (TUGE)

Tonon silili: Na rantawa Gwamnan Kaduna, Uba Sani Naira Miliyan 30 yayi yakin neman zabe da alkawarin zai mayar da Naira Miliyan 100 idan ya zama gwamna amma yanzu ya hanani kudina>>Inji Ummi El-Rufai (TUGE)

Duk Labarai
Daya daga cikin yaran tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai me suna Ummi El-Rufai TUGE ta zargi gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani da kin biyanta bashin Naira Miliyan 30. Tace Ta ranta masa Naira Miliyan 30 yayi yakin neman zabe da alkawarin cewa idan ya zama Gwamna zai mayar mata da riba kudin su zama Naira Miliyan 100 amma yanzu yaki biyanta. Tace ita a yanzu ma ba wai ribar take nema ba, tana neman kudinta su fito ne watau Miliyan 30 din. Tace A wancan lokacin da suka yi yakin nema zabe kowa ya sani babu kudi ana Cashless inda tace dalili kenan da Uba Sani ya roketa ta bashi rancan wadancan kudin. Tace duk da dai itama tasan son banza ne ya kaita amma dai ya biyata hakkinta, ta bayyana hakane a shafinta na Tiktok a wani dogon Bidiyon data wallafa. h...
Tonon Silili: Wallahi a gabana aka yi Lalata da Sadiya Haruna Matar Gfresh>>Inji Shatu, Tsohuwar kawar Sadiya Haruna

Tonon Silili: Wallahi a gabana aka yi Lalata da Sadiya Haruna Matar Gfresh>>Inji Shatu, Tsohuwar kawar Sadiya Haruna

Duk Labarai
Shatu wadda tsohuwar Mutuniyar Sadiya Haruna ce ta bayyana cewa Sadiya Haruna ta nemeta su yi Mahdygo amma ta kiya. Sannan tace a gabanta aka yi lalata da Sadiya Haruna. Ta bayyana hakane a wani TiktokLive da aka yi da ita inda take bayar da labarin yanda ta tsere bayan Sadiya Haruna taso ta yi Mahdygo da ita ta hanyar Qarfi. Sannan Tace duka wadannan maganganu da take fada ba wai da ka bane, tana da shaida da hujjoji. https://www.tiktok.com/@mrfunny2471/video/7665772472054091029?_r=1&u_code=ejaikd8elj8058&preview_pb=0&sharer_language=en&_d=ejaij098emc1h5&share_item_id=7665772472054091029&source=h5_m&timestamp=1784876945&user_id=7483197776647635989&sec_user_id=MS4wLjABAAAAN7fVbcc0mzRzgIxdVwTekj-Bzgfq381B8aILPWs15fqP6aFNZ5GwIpbLEwMTYvVW&s...
Tauraron Streamer na Najeriya, Peller ya nuna Shanu 12 da zai yanka a bikin aurensa da Budurwarsa Jarvis

Tauraron Streamer na Najeriya, Peller ya nuna Shanu 12 da zai yanka a bikin aurensa da Budurwarsa Jarvis

Duk Labarai
Tauraron Streamer, Peller ya nuna Shanu 12 da zai yanka a bikinsu da Budurwarsa, Jarvis. Ya nuna hakanne a wani Bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta inda masoyansa ke ta yabawa da fadar cewa za'a sha Biki na gani na fada. https://twitter.com/i/status/2080390295615648121 Hakanan an ga Hotuna da Bidiyo na Prewedding dinssu. Saidai abinda yafi daukar hankali shine ganin cewa ashe Peller tuni ya dirkawa Jarvis ciki. https://twitter.com/i/status/2079904991746171323
Maimakon ka kama Girmanka ka zabi yin abin kana nan mutane da bata min suna>>Shugaba Tinubu ya gayawa Atiku bayan da Atikun ya kaiwa Shugaban Amurka tsokacin zargin Tinubu da safarar Qaya

Maimakon ka kama Girmanka ka zabi yin abin kana nan mutane da bata min suna>>Shugaba Tinubu ya gayawa Atiku bayan da Atikun ya kaiwa Shugaban Amurka tsokacin zargin Tinubu da safarar Qaya

Duk Labarai
Fadar Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta mayar da martani kan rahoton cewa, Atiku Abubakar ya kaiwa shugaban kasar Amirka, Donald Trump tsegumin cewa ana zargin Shugaba Tinubu da safarar Qaya. A sanarwar da ya fitar ta bakin me magana da yawunsa, Bayo Onanuga, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yace Atikun ya kamata a sanshi da kima da kamun kai da sanin ya kamata Yace amma duk ya zubar da wannan ya koma yin abubuwan kananan mutane na zubar da girma. Yace Tuni kotu ta wankeshi akan maganar zargin safarar qaya. Yace kamata yayi Atiku ya kawo tsare-tsaren da zai yi amfani dasu dan gyara Najeriya wanda hakan zai ja hankalin 'yan kasa su zabeshi amma ba bata suna ba. Yace Shi abinda Atikun yayi ko a jikinsa. Yace amma fa shima Atikun da a kasar China yake da tuni an dade da Sh...
Kalli Bidiyon: Farfesa Sheikh Isa Ali Pantami da ya dauki hankula bayan da aka ganshi yana zara idanu yana fadar babu wanda ya isa ya musu barazana

Kalli Bidiyon: Farfesa Sheikh Isa Ali Pantami da ya dauki hankula bayan da aka ganshi yana zara idanu yana fadar babu wanda ya isa ya musu barazana

Duk Labarai
Wani Bidiyo Dan takarar Gwamnan jihar Gombe kuma malamin Addinin Islama, Farfesa Sheikh Isa Ali Pantami ya karade kafafen sada zumunta. An ga malam yana zaro idanu yana cewa shin na muku kama da wanda za'a yiwa Barazana? https://www.tiktok.com/@halilullah17/video/7664946356754124052?_r=1&_t=ZS-98IDJpxULP5 Bidiyon ya dauki hankula sosai inda aka ga matasa na dauka wasu ma suna barkwanci dashi.
An zargi Tauraruwar fina-finan Hausa, Lulu da fitar da Bidiyon Update

An zargi Tauraruwar fina-finan Hausa, Lulu da fitar da Bidiyon Update

Duk Labarai
An zargi Tauraruwar fina-finan Hausa, Lulu da fitar da Bidiyon update din wata. Sannan an zargeta da zuwa ta nuna Bidiyon ga mahaifiyar me Bidiyon, sannan an zargeta da dukan mahaifiyar wadda suke fadan. I da labarin ke cewa, wai wata daga Amurka ta kira tasa an kamata sannan an mata na jaki. Bayan watsuwar lamarin a kafafen sada zumunta, Lulu ta fito ta yi karin haske kan lamarin. Tace duka wancan labarin ba gaskiya bane, bata fitar da Bidiyon update din kowa ba, sannan bata daki mahaifiyar kowa ba sannan ba'a kamata ba hakanan kuma ba'a daketa ba. Ta yi zargin cewa wasu ne kawai dake neman suna da sunansu suke yada labaran karya akanta amma babu wani abu makamancin hakan da ya faru da ita. Lulu tace ba halinta bane ta rika fitar da tsiraicin mutane ba.