Saturday, January 11
Shadow

Duk Labarai

Ji Martanin da Hadiza Gabon tawa wani da yace mata ta bashi kudi

Ji Martanin da Hadiza Gabon tawa wani da yace mata ta bashi kudi

Duk Labarai, Hadiza Gabon
Tauraruwar Fina-finan Hausa, Hadiza Gabon ta wallafa wannan hoton nata a shafinta na sada zumunta inda masoyanya suka rika yabawa. Saidai wani ya roketa da ta yiwa mutane kyautar kudi kamar yanda dan siyasa na jihar Kaduna,Bello ElRufai ke yi. Saidai Hadizar ta mai martanin cewa, ya je ya samu aikin yi. Ya dai mayar mata da martanin cewa, ko ya kawo takardunsa ta bashi aiki a dakin hada shirye-shiryenta na Youtube? Daga nan dai Hadizar bata sake takashi ba. A baya dai, Abokiyar aikin Hadizar, Rahama Sadau ta rabawa masoyanta kudade ta shafukan sada zumunta na Facebook da Instagram.

Jimullar ‘yan Najeriya 55,910 ne aka kashe an kuma yi garkuwa da 20,000

Duk Labarai
Wata kungiya dake saka ido akan harkokin tsaro ORFA ta bayyana cewa daga shekarar 2019 zuwa 2023 an samu kashe mutane 55,910 da yin garkuwa da guda 20,000. Kungiyar tace kungiyoyin IS-WA-P da B0k0 Haram ne da takwarorinsu suka yi wadannan aika-aika. A ranar Alhamis ne kungiyar ta fitar da wannan bayani inda tace amma kiristoci ne suka fi fuskantar wannan matsala. Wakilin Kungiyar, Frans Vierhout ya bayyana cewa hakan ya nuna yanda lamuran tsaro suka tabarbare a Najeriya.
ABIN ALFAHRI: Matashi Dan Arewa Na Farko Da Ya Kammala Karatu A Fannin Magungunan Musulunci A Kasar Qatar

ABIN ALFAHRI: Matashi Dan Arewa Na Farko Da Ya Kammala Karatu A Fannin Magungunan Musulunci A Kasar Qatar

Duk Labarai
ABIN ALFAHRI: Matashi Dan Arewa Na Farko Da Ya Kammala Karatu A Fannin Magungunan Musulunci A Kasar Qatar. Dakta Muhammadu Kabiru Hassan (Dangwamna) dake Samaru Zaria ya zama mutum na farko da ya fito daga yankin Arewacin Nijeriya da ya kammala karantu a kasar Qatar National Museums Authority bangaren islamic herbal medicine curse. Daga karshe ya nemi jama'a da su yi masa addu'ada fatan alkairi, Allah Ya sa karatun da ya yi ya amfani muśùĺùñci gaba daya.
DA DUMI-DUMI: Sojoji Sun Harbe Wani DPO Na ‘Yan Sanda A Jihar Zamfara Har Lahira Kan Zargin Safarar Makamai

DA DUMI-DUMI: Sojoji Sun Harbe Wani DPO Na ‘Yan Sanda A Jihar Zamfara Har Lahira Kan Zargin Safarar Makamai

Duk Labarai
DA DUMI-DUMI: Sojoji Sun Harbe Wani DPO Na 'Yan Sanda A Jihar Zamfara Har Lahira Kan Zargin Safarar Makamai. Al'amarin dai ya faru ne a garin Ɗanmarke da ke karƙashin ƙaramar hukumar Bukkuyum ta jihar Zamfara, a ranar Larabar nan da daddare, kamar yadda wata sanarwa da rundunar ƴansandan jihar ta Zamfara ta fitar. Dpon an tsaida shi a checkpoint na dan marke da ke cikin Karama Hukumar Bukkuyum ta Jihar Zamfara ya ki tsayawa, wanda hakan yasa sojoji suka yi waya gaba domin su rufe hanya ga mota nan zuwa mai kala kaza, ga sunan zuwa. Nan da nan suka bi umurnin soji nan take sojoji su ka biyo motarsa yana zuwa ya isko an rufe hanya, bayan ya bayyana kan sa matsayin ɗan sanda ne, sai kuma ya fita daga motar zai gudu wanda hakan yasa sojojin suka bude masa wuta. Daga bisani ...
Atiku ya caccaki manufofin Tinubu kan ƙayyade shekarun shiga jami’a

Atiku ya caccaki manufofin Tinubu kan ƙayyade shekarun shiga jami’a

Duk Labarai
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi kakkausar suka ga manufar ma’aikatar ilimi ta tarayya na kayyade shekarun shiga jami’o’i, inda ya bayyana hakan a matsayin wani baƙon abu da zai janyo komabaya ga harkar ilimi a Najeriya A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku ya bayyana manufar a matsayin "zai haifar da naƙasu ga hakar ilimi" inda ya ce hakan ya saɓa wa ƙa'idojin tsarin ƙasar ta hanyar shiga ayyukan gwamnatocin jihohi. Atiku ya yi nuni da cewa ilimi na cikin abubuwan da ke cikin ƙundin tsarin mulkin Najeriya, wanda ya bai wa ƙananan hukumomin ƙasar karfi wajen tafiyar da harkokinsa. Ya yi allah-wadai da matakin da gwamnati ta ɗauka na kafa manufofin ilimi ba kamar yadda doka ta tanada ba inda ya bayyana cewa hakan ya saɓa wa ƙundin tsarin mulkin ƙasa...