Saturday, December 14
Shadow

labaran tinubu ayau

A cikin watanni 11 da suka gabata, Shugaba Tinubu ya kashe Naira Biliyan 14.77 wajan kula da jiragen saman da yake hawa

A cikin watanni 11 da suka gabata, Shugaba Tinubu ya kashe Naira Biliyan 14.77 wajan kula da jiragen saman da yake hawa

labaran tinubu ayau, Siyasa
Gwammatin tarayya a karkashin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta kashe Naira Biliyan 14.77 wajan kula da jiragen da shugaban kasar ke amfani dasu a cikin watanni 11 da suka gabata. Hakan na zuwane a yayin da majalisar tarayya ta amince a sayowa shugaban kasar sabbin jirage 2. Kudin da za'a kashe wajan siyo sabbin jiragen sun kai Naira Biliyan 918.7 ko kuma dala Miliyan 623.4, kamar yanda kwamitin majalisar ya bayyana. Rahotanni dai sun bayyana cewa, jiragen da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da mataimakinsa,Kashim Shettima ke amfani dasu sun tsufa sosai suna bukatar a canjasu.
An Gudanar Da Addu’ar Cikar Mahaifiyar Shugaba Tinubu Shekaru Sha Daya Da Rasuwa

An Gudanar Da Addu’ar Cikar Mahaifiyar Shugaba Tinubu Shekaru Sha Daya Da Rasuwa

labaran tinubu ayau, Siyasa
An Gudanar Da Addu'ar Cikar Mahaifiyar Shugaba Tinubu Shekaru Sha Daya Da Rasuwa …wanda shugaban hukumar kula da almajirai ta kasa ya jagoranta a yau Juma'a Daga Mustapha Narasulu Nguru Shugaban hukumar kula da almajirai da yaran da ba sa zuwa makaranta na kasa, Dr. Muh'd Sani Idriss Phd ya jagoranci addu'a ga mahaifiyar Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu GCFR, wanda aka gabatar yau Juma'a. Shugaban hukumar ya yi addu'a a gare ta sosai a yau Juma'a 21/06/2024 a yayin da take cika shekaru sha daya da barin duniya. Cikin jawabansa ya rokar mata rahama ga Allah (SWT) kamar yadda addini ya tanadar. Muna fatan Allah Ya yi mata rahama da sauran y'an uwa musumal. Allah Ya sa Aljannah makoma.
Babu Alamar Abubuwa zasu yi sauki a gwamnatin Tinubu>>Inji Archbishop Nwaobia

Babu Alamar Abubuwa zasu yi sauki a gwamnatin Tinubu>>Inji Archbishop Nwaobia

labaran tinubu ayau, Siyasa
Wani babban malamin Kiristanci Archbishop Nwaobia ya bayyana cewa babu alamar lamura zasu gyaru a gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. A hirar da wakilin jaridar sunnewsonline suka yi dashi, ya bayyana cewa faduwar darajar Naira akan Dalar Amurka matsala ce babba wadda ta jefa 'yan Najeriya da yawa cikin halin wahala. Yace kuma gwamnatin Tinubu ta kasa samo hanyar warware wannan matsala. Ya kara da cewa, Sam Gwamnatin Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu bata da alkibla dan ta kasa dasa tushen ci gaban Najeriya.
Atiku ya jajanta wa Tinubu dangane da “zamewar” da ya yi

Atiku ya jajanta wa Tinubu dangane da “zamewar” da ya yi

labaran tinubu ayau, Siyasa
Mutumin da shugaba Tinubun ya kayar a zaɓen 2023, Atiku Abubakar na jam'iyyar adawa ta PDP, ya ce yana jajanta wa Bola Tinubu dangane da "zamewar" da ya yi. "Ina matukar jajanta wa shugaba Bola Tinubu dangane da ɗan hatsarin da ya samu a lokaci da yake ƙoƙarin zagaya masu fareti ranar dimokaraɗiyya. Ina fatan lafiyar lau." A baya-bayan nan dai an ga yadda tsohon mataimakin shugaban ƙasar, Atiku Abubakar ke ƙara ƙaimi wajen yin hamayya ta fuskar sukan abubuwan da yake ganin gwamnatin ba ta yi daidai ba.
Akwai yiyuwar Shugaba Tinubu zai yiwa majalisar Zartarwarsa garambawul inda za’a yiwa wasu ministoci canji, za’a kara kirkiro da wasu

Akwai yiyuwar Shugaba Tinubu zai yiwa majalisar Zartarwarsa garambawul inda za’a yiwa wasu ministoci canji, za’a kara kirkiro da wasu

labaran tinubu ayau, Siyasa
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya kammala shiri tsaf dan yiwa majalisar zartarwarsa garambawul inda za'a kirkiro karin wasu ministoci da ma'aikatu. Daily Trust tace daga cikin sabbin ma'aikatun da ake son kirkirowa akwai ta kula da dabbobi wadda za'a cire daga ma'aikatar noma. Wannan ma'aikatar ana tunanin zata kawo mafita ga rikicin manoma da makiyaya dake faruwa duk shekara. Hakanan bayan kirkirar sabbin ma'aikatu ana kuma tunanin shugaban kasan zai samar da kananan ministoci a sauran ma'aikatun da basu dasu. Masu kula da al'amuran yau da kullun da masu sharhi a harkokin siyasa sun caccaki gwamnatin Tinubu saboda kin saka kananan ministoci a wasu ma'aikatu
Ba A Bi Umarnin Da Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya Bayar Na Sake Fasalin Naira Ba>>Tsohon Daraktan CBN Ga Kotu

Ba A Bi Umarnin Da Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya Bayar Na Sake Fasalin Naira Ba>>Tsohon Daraktan CBN Ga Kotu

labaran tinubu ayau, Siyasa
Tsohon Daraktan Ayyuka na Kudi a Babban Bankin Najeriya (CBN), Ahmed Bello Umar, ya shaida wa babbar kotun Abuja da ke Maitama cewa ba a bi umarnin da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar na sake fasalin Naira ba. Ya bayyana cewa takardar kudin Naira da aka sake gyarawa a karkashin tsohon Gwamna Godwin Emefiele sun sha bamban da bayanan da tsohon shugaban kasar ya amince da su. Daga: Abbas Yakubu Yaura
Da Dumi-Dumi: ‘Nan Ba da Jimawa Ba Za Mu Aikawa Majalisa Da Kudirin Doka Kan Sabon Albashin Ma’aikata’ – Tinubu

Da Dumi-Dumi: ‘Nan Ba da Jimawa Ba Za Mu Aikawa Majalisa Da Kudirin Doka Kan Sabon Albashin Ma’aikata’ – Tinubu

labaran tinubu ayau, Siyasa
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce nan ba da dadewa ba zai aika da sabuwar dokar mafi karancin albashi ga majalisar dokokin kasar Tinubu ya bayyana hakan ne a jawabinsa na ranar dimokradiyya a ranar Laraba. Ya ce gwamnatinsa ba ta murkushe kungiyar kwadago ba kamar yadda gwamnatin kama-karya ta yi. “Mun yi shawarwari cikin nasara kuma mun yi tattaunawa tare da kungiyoyin kwadago a kan mafi karancin albashi na kasa, nan ba da jimawa ba za mu aika da kudirin zartarwa ga Majalisar Dokoki ta kasa domin tabbatar da abin da aka amince da shi a cikin shekaru biyar masu zuwa ko kasa da haka,” in ji shi. Ku tuna cewa kwamitin mafi karancin albashi na kasa ya mika rahotonsa ga shugaban kasa a ranar Litinin. A cikin rahoton, gwamnatin tarayya ta gabatar da shawarar mafi karancin alb...
Tinubu bai faɗi nawa albashi mafi ƙanƙanta zai kasance ba a jawabinsa

Tinubu bai faɗi nawa albashi mafi ƙanƙanta zai kasance ba a jawabinsa

labaran tinubu ayau, Siyasa
Shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta aike da ƙudiri ga Majalisar Dokokin ƙasar wanda zai kunshi adadin abin da aka amince da shi ya zama albashi mafi ƙanƙanta ga ma'aikata a "matsayin wani ɓangare na "dokokinmu" a shekaru biyar ko ƙasa da haka masu zuwa. Shugaban wanda ya faɗi hakan ne a yayin jawabinsa ga ƴan Najeriya albarkacin ranar dimukraɗiyya, ya ce lallai yana sane da halin matsin tattalin arzikin da 'yan najeriyar ke ciki. To sai dai ya nemi "yan ƙasar da su tallafa wajen cimma "dimukraɗiyyar da za ta tabbatar da cigaban tattalin arziki." Ƴan Najeriya dai sun yi fatan jin ƙarin albashin da suka samu daga bakin shugaban nasu a jawabin nasa na safiyar Talata. A ranar Litinin ne dai kwamitin mutum 37 da aka kafa kan albashin mafi ƙanƙanta ya miƙa rahotonsa bayan kwashe kima...