Saturday, January 18
Shadow

Siyasa

A cikin watanni 11 da suka gabata, Shugaba Tinubu ya kashe Naira Biliyan 14.77 wajan kula da jiragen saman da yake hawa

A cikin watanni 11 da suka gabata, Shugaba Tinubu ya kashe Naira Biliyan 14.77 wajan kula da jiragen saman da yake hawa

labaran tinubu ayau, Siyasa
Gwammatin tarayya a karkashin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta kashe Naira Biliyan 14.77 wajan kula da jiragen da shugaban kasar ke amfani dasu a cikin watanni 11 da suka gabata. Hakan na zuwane a yayin da majalisar tarayya ta amince a sayowa shugaban kasar sabbin jirage 2. Kudin da za'a kashe wajan siyo sabbin jiragen sun kai Naira Biliyan 918.7 ko kuma dala Miliyan 623.4, kamar yanda kwamitin majalisar ya bayyana. Rahotanni dai sun bayyana cewa, jiragen da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da mataimakinsa,Kashim Shettima ke amfani dasu sun tsufa sosai suna bukatar a canjasu.
An Gudanar Da Addu’ar Cikar Mahaifiyar Shugaba Tinubu Shekaru Sha Daya Da Rasuwa

An Gudanar Da Addu’ar Cikar Mahaifiyar Shugaba Tinubu Shekaru Sha Daya Da Rasuwa

labaran tinubu ayau, Siyasa
An Gudanar Da Addu'ar Cikar Mahaifiyar Shugaba Tinubu Shekaru Sha Daya Da Rasuwa …wanda shugaban hukumar kula da almajirai ta kasa ya jagoranta a yau Juma'a Daga Mustapha Narasulu Nguru Shugaban hukumar kula da almajirai da yaran da ba sa zuwa makaranta na kasa, Dr. Muh'd Sani Idriss Phd ya jagoranci addu'a ga mahaifiyar Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu GCFR, wanda aka gabatar yau Juma'a. Shugaban hukumar ya yi addu'a a gare ta sosai a yau Juma'a 21/06/2024 a yayin da take cika shekaru sha daya da barin duniya. Cikin jawabansa ya rokar mata rahama ga Allah (SWT) kamar yadda addini ya tanadar. Muna fatan Allah Ya yi mata rahama da sauran y'an uwa musumal. Allah Ya sa Aljannah makoma.
Ji tsokanar da dan Sarki Muhammad Sanusi II, Ashraf Sanusi yawa Tsohon Gwamnan Kano, Ganduje

Ji tsokanar da dan Sarki Muhammad Sanusi II, Ashraf Sanusi yawa Tsohon Gwamnan Kano, Ganduje

Kano, Siyasa
{"remix_data":[],"source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Bayan hukuncin kotu kan rushe sabbin masarautun Kano, lamarin ya jawo cece-kuce a jihar inda mahawara ta yi zafi kuma kowane bangare tsakanin gwamnatin Kano, da Sarki Muhammad Sanusi II da Sarki Aminu Ado Bayero ke ikirarin yin nasara, Gwamnatin jihar ta sa a rushe gidan sarki na Nasarawa wanda sarki Aminu ke ciki. A wasu hotuna da bidiyo da suka watsu sosai a kafafen sada zumunta, an ga yanda motocin rushe gida suka je fadar ta Nasarawa. Yayin da yake mayar da martani akan wannan lamari, dan gidan Sarki Muhamma...

Abin Kunyane hukuncin da kotu ta yanke a Kano>>Inji Babban Lauya, Femi Falana

Siyasa
Babban kauya, Femi Falana ya bayyana cewa, abin munyane hukuncin da kotu ta yanke a Kano. Yace babbar kotun tarayya dake Kano bata da hurumin shiga harkar siyasar sarauta, hurumin kotun jiha ne. Yace kuma hukuncin da kotun ta yanke ya kawo rudani dan bai fito da hukuncin da kotun ke nufi ba baro-baro. Ya kara da cewa kotun daukaka kara ce dama dai take warware irin wannan matsala kuma yana da kyau ganin cewa yanzu an aikawa kotun daukaka kara shari'ar.
Ji yanda ta kaya bayan da gwamna Abba yace a rushe gidan Nasarawa da Sarki Aminu Ado Bayero ke zaune a ciki

Ji yanda ta kaya bayan da gwamna Abba yace a rushe gidan Nasarawa da Sarki Aminu Ado Bayero ke zaune a ciki

Kano, Siyasa
A jiyane dai rahotanni suka bayyana cewa, Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin rushe fadar Nasarawa wadda sarki Aminu Ado Bayero ke ciki da nufin gyarata. Saidai tuni jami'an tsaro sukawa fadar kawanya dan hana aiwatar da wannan umarni. A jiyandai, Tuni har an kai motocin dake rushe gida fadar ta Nasarawa amma lamarin bai tabbata ba. Tun a jiyan dai, Wasu masu sharhi akan al'amuran yau da kullun ke ganin cewa, wannan umarni kuskurene saboda ba'a kammala shari' ba. Daya daga cikin masu irin wannan ra'ayi shine, Salihu Tanko Yakasai wanda yace gwamnan zai saka ai masa dariya saboda wannan umarni da ya bayar: https://twitter.com/dawisu/status/1803884035124474006?t=sGU-jQHoxSU0qi4uYksphQ&s=19 Wannan hukuncin kotu dai ya kawo rudani a Kano inda kowane...