Saturday, January 18
Shadow

Siyasa

Ya kamata a wayar da kan Mutane: Irin yanda yawan mutane ke karuwa a Najeriya na damuna>>Shugaba Buhari

Ya kamata a wayar da kan Mutane: Irin yanda yawan mutane ke karuwa a Najeriya na damuna>>Shugaba Buhari

Siyasa
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, irin yanda yawan mutane ke karuwa a Najeriya lamarin na damunshi. Ya bayar da shawarar cewa, ya kamata a wayar da kawunan mutane game da hakan. Shugaban ya bayyana hakane bayan kammala sallar Idi a jiya, Lahadi. Ya kuma bayyana farin cikinsa kan yanda mutane da yawa suka rungumi harkar Noma. Shugaban yace nasarar kasa ta dogara ne akan zamun shuwagabanni masu nasara akai-akai.
Babu Alamar Abubuwa zasu yi sauki a gwamnatin Tinubu>>Inji Archbishop Nwaobia

Babu Alamar Abubuwa zasu yi sauki a gwamnatin Tinubu>>Inji Archbishop Nwaobia

labaran tinubu ayau, Siyasa
Wani babban malamin Kiristanci Archbishop Nwaobia ya bayyana cewa babu alamar lamura zasu gyaru a gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. A hirar da wakilin jaridar sunnewsonline suka yi dashi, ya bayyana cewa faduwar darajar Naira akan Dalar Amurka matsala ce babba wadda ta jefa 'yan Najeriya da yawa cikin halin wahala. Yace kuma gwamnatin Tinubu ta kasa samo hanyar warware wannan matsala. Ya kara da cewa, Sam Gwamnatin Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu bata da alkibla dan ta kasa dasa tushen ci gaban Najeriya.
Kuma Dai: Kungiyar Kwadago, NLC tace zata iya amincewa idan gwamnati ta biya kasa da Naira dubu dari biyu da hamsin(250,000) a matsayin mafi karancin Albashi

Kuma Dai: Kungiyar Kwadago, NLC tace zata iya amincewa idan gwamnati ta biya kasa da Naira dubu dari biyu da hamsin(250,000) a matsayin mafi karancin Albashi

Siyasa
Kungiyar Kwadago ta NLC ta bayyana cewa bata nace akan sai gwamnatin tarayya ta biya naira dubu dari biyu da hamsin(250,000) ba a matsayin mafi karancin Albashi ba. Shugaban kungiyar kwadago ta TUC, Festus Osifo ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa dashi. Yace a shirye suke su amince da kasa da Naira dubu dari biyu da hamsin (250,00) a matsayin mafi karancin Albashin. Gwamnatin tarayya dai bata bayyana matsayar ta ba kan mafi karancin albashin ba.
Kwamitin Majalisar Wakilai Ya Bada Shawarar Samawa Tinubu Da Shettima Sabbin Jiragen Sama

Kwamitin Majalisar Wakilai Ya Bada Shawarar Samawa Tinubu Da Shettima Sabbin Jiragen Sama

Siyasa
Kwamitin Majalisar Wakilai akan Tsaron Kasa da Tattara Bayanan Sirri ya bukaci gwamnatin tarayya ta sayawa Shugaban Kasa Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima sabbin jiragen sama. Shawarar kwamitin na kunshe ne a cikin rahoton da kwamitin ya fitar bayan gudanar da bincike akan lafiyar jiragen saman fadar shugaban kasa. A watan Mayun daya gabata, majalisar wakilan ta umarci kwamitin ya gudanar da cikakken bincike akan jiragen saman fadar shugaban kasar domin tantance lafiyarsu. Shawarar ta biyo bayan kudirin da Dan Majalisa Satomi Ahmad ya gabatar, wanda aka tafka mahawara akan sa. Wasu daga cikin 'yan majalisar sun bada shawarar cewar kamata yayi shugaban kasar ya rika shiga jirgin sama ko motar haya idan zai yi balaguro. Kudirin na Satomi Ahmad ya biyo bayan rahoton s...
Kotun Ƙolin Amurka ta amince da amfani da ƙwayoyin zubar da ciki

Kotun Ƙolin Amurka ta amince da amfani da ƙwayoyin zubar da ciki

Siyasa
Bakin Alƙalan Kotun Ƙolin Amurka yazo ɗaya wajen amincewa da amfani da ƙwayoyin zubar da ciki. Wani lamari da ake gani a matsayin nasara ga masu fafutukar 'yancin zubar da ciki. Kotun ta yi watsi da buƙatar ƙungiyoyin likitoci masu yaƙi da zubar da ciki da kuma 'yan gwagwarmaya da suke neman a taƙaita amfani da maganin Mifepristone. Kotun kolin ta ce ƙungiyoyin likitocin ba su da 'yanci shigar da ƙara kan hakan, kuma sun gaza gabatar da hujjojin cewa maganin Mifepristone yana cutarwa. Wannan ne babban hukuncin da kotun ta yanke, tun watsi da 'yancin zubar da ciki da kotun tarayyar ƙasar ta yi shekara biyu da suka gabata.

G7 ta amince a yi amfani da kadarorin Rasha da aka ƙwace a ƙasashen duniya

Siyasa
Ƙungiyar Ƙasashen G7 masu ƙarfin masana'atu sun amince a yi amfani da ribar kadarorin Rasha da aka ƙwace, domin bai wa Ukraine ta yi amfani da su. Biden ya ce yarjejeniyar za ta hada da tura bayanan sirri, da bai wa sojoji horo da bin dokokin NATO da zuba kuɗi a masana'antu da ke Ukraine domin ci gaba da samar da makamai. Biden ya ce burinsu shi ne samar wa Ukraine tsaro ''na gaske'', da kuma turmusa hancin Rasha da ƙawayenta a ƙasa. Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya ce wannan ba abu ne da Shugaba Putin zai kawar da kai ya kyale ba.
Za a ci gaba da sauye-sauyen tattalin arziƙi duk da wahalhalun da ake fuskanta – Tinubu

Za a ci gaba da sauye-sauyen tattalin arziƙi duk da wahalhalun da ake fuskanta – Tinubu

Siyasa
Shugaban Najeriya Bola Tinubu, ya ce sauye-sauyen da gwamnatinsa ta yi ya zama dole wajen gyara tattalin arzikin kasar, duk kuwa da kara wahalhalun da ake fuskanta da ke janyo fushin jama'a. Tinubu ya bayyana hakan ne a jawabinsa na jiya a yayin bikin ranar dimokuradiyyar Najeriya. “Na fahimci matsalolin tattalin arziki da muke fuskanta a matsayinmu na kasa. Tattalin arzikinmu yana cikin tsananin bukatar gyara shekaru da yawa. Ba a daidaita shi ba saboda an gina shi a kan kura-kurai na dogaro da kudaden shigar da ake samu daga hako man fetur,” inji Tinubu. Tun bayan hawansa ƙaragar mulki a bara, Tinubu ya cire da tallafin man fetur wanda ya haddasa tashin gwauron zabin sufuri da farashin abinci da sauran kayayyakin masarufi a fadin kasar. Dubban ‘yan Najeriya ne suka fito kan t...
Ba mu cimma yarjejeniya da gwamnati kan mafi ƙarancin albashi ba – NLC

Ba mu cimma yarjejeniya da gwamnati kan mafi ƙarancin albashi ba – NLC

Siyasa
Ƙungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta soki lamirin bayanin da shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya yi kan cewa an cimma matsaya game da sabon albashin ma'aikata mafi karanci a ƙasar. Ƙungiyar ƙwadagon ta kuma dage kan buƙatarta ta neman sabon mafi karancin albashi na kasa ya kasance naira 250,000. A yayin da yake jawabi a ranar Laraba, lokacin bikin ranar dimokuradiyya, Tinubu ya ce an cimma matsaya kan batun sabon mafi karancin albashin da aka dade ana muhawara a kai tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadago. Shugaban ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba za a aika da wani kudirin doka na zartarwa ga majalisar dokokin ƙasar domin ta tsara sabuwar yarjejeniyar mafi karancin albashi. Sai dai a wata sanarwa da NLC ta fitar a jiya Laraba, muƙaddashin shugaban NLC, Prince Adewale Adeya...