Monday, December 16
Shadow

Siyasa

Atiku ya jajanta wa Tinubu dangane da “zamewar” da ya yi

Atiku ya jajanta wa Tinubu dangane da “zamewar” da ya yi

labaran tinubu ayau, Siyasa
Mutumin da shugaba Tinubun ya kayar a zaɓen 2023, Atiku Abubakar na jam'iyyar adawa ta PDP, ya ce yana jajanta wa Bola Tinubu dangane da "zamewar" da ya yi. "Ina matukar jajanta wa shugaba Bola Tinubu dangane da ɗan hatsarin da ya samu a lokaci da yake ƙoƙarin zagaya masu fareti ranar dimokaraɗiyya. Ina fatan lafiyar lau." A baya-bayan nan dai an ga yadda tsohon mataimakin shugaban ƙasar, Atiku Abubakar ke ƙara ƙaimi wajen yin hamayya ta fuskar sukan abubuwan da yake ganin gwamnatin ba ta yi daidai ba.
Shettima ya buƙaci likitocin Najeriya su taimaka wajen inganta ƙasar

Shettima ya buƙaci likitocin Najeriya su taimaka wajen inganta ƙasar

Siyasa
Mataimakin shugaban ƙasar, Kashim Shettima ya yi kira ga likitocin ƙasar, su riƙa zama a ƙasar, don taimaka wa magance matsalar da ƙasar ke fuskanta ta ƙarancin likitoci. Shettima ya yi kiran ne a lokacin da ƙungiyar likitocin ƙasar - ƙarƙashin jagorancin sabon shugabanta, Farfesa Bala Audu - suka kai masa ziyara a ofishinsa ranar Talata. Mataimakin shugaban ƙasar ya nuna damuwa kan yadda likitocin ƙasar ke yawan ficewa daga ƙasar domin neman ayyuka a ƙasashen waje. A baya-bayan nan dai ana samun yawaitar ficewar likitocin Najeriya daga ƙasar, zuwa ƙasashen wajen domin samun ingantaccen albashi da yanayin aikin mai kyau. Sai dai mataimakin shugaban ƙasar, ya jaddada cewa gwamnatinsu na iya bakin ƙoƙarinsu wajen inganta yanayin aikin likitoci a ƙasar, musamman waɗanda suka zaɓi ...
YANZU-YANZU: Gwamnan Jihar Sokoto Ahmad Aliyu Ya Bada Umarnin Biyan Naira Dubu Talatin A Matsayin Kyautar Goron Sallah Ga Dukkanin Ma’aikatan Jihar Da Na Kananan Hukumomi A Gobe Alhamis

YANZU-YANZU: Gwamnan Jihar Sokoto Ahmad Aliyu Ya Bada Umarnin Biyan Naira Dubu Talatin A Matsayin Kyautar Goron Sallah Ga Dukkanin Ma’aikatan Jihar Da Na Kananan Hukumomi A Gobe Alhamis

Siyasa
Gwamnan Jihar Sokoto Ahmad Aliyu Ya Bada Umarnin Biyan Naira Dubu Talatin A Matsayin Kyautar Goron Sallah Ga Dukkanin Ma'aikatan Jihar Da Na Kananan Hukumomi A Gobe Alhamis. A yayin da masu karbar fansho da alawus za su more kyautar naira dubu ashirin duk a matsayin goron sallah. Daga Real Buroshi Mawaka Sokoto
Faduwar da Tinubu yayi zata iya faruwa akan kowa, Cewar Sheikh Pantami, saidai da yawa sun sokeshi akan bai ce komai ba kan kashe-kashen da ake a Arewa amma gashi yana kare shugaban kasa

Faduwar da Tinubu yayi zata iya faruwa akan kowa, Cewar Sheikh Pantami, saidai da yawa sun sokeshi akan bai ce komai ba kan kashe-kashen da ake a Arewa amma gashi yana kare shugaban kasa

Siyasa
Babban malamin Addinin Islama, sheikh Isa Ali Pantami ya yi martani kan faduwar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yayi a wajan bikin ranar dimokradiyya. Sheikh Pantami ya bayyana cewa, faduwar shugaban kasar bata da alaka da shugabanci kuma zata iya faruwa akan kowa. Ya bayar da shawarar cewa a rika kawar da akai akan irin wadannan labarai zai fi kyau. "This can happen to any of us. It has nothing to do with governance. The earlier we ignore this kind of news, the better. May the Almighty make Nigeria a better place for us." https://twitter.com/ProfIsaPantami/status/1800855807711645873?t=2C5Wqjfz1fhBeyMVkRXelw&s=19 Malam yayi martanine bayan da jaridar Vanguard ta wallafa labarin faduwar shugaban kasar. Saidai malam ya sha martani daga bakin wasu dake cewa bai yi mag...
Akwai yiyuwar Shugaba Tinubu zai yiwa majalisar Zartarwarsa garambawul inda za’a yiwa wasu ministoci canji, za’a kara kirkiro da wasu

Akwai yiyuwar Shugaba Tinubu zai yiwa majalisar Zartarwarsa garambawul inda za’a yiwa wasu ministoci canji, za’a kara kirkiro da wasu

labaran tinubu ayau, Siyasa
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya kammala shiri tsaf dan yiwa majalisar zartarwarsa garambawul inda za'a kirkiro karin wasu ministoci da ma'aikatu. Daily Trust tace daga cikin sabbin ma'aikatun da ake son kirkirowa akwai ta kula da dabbobi wadda za'a cire daga ma'aikatar noma. Wannan ma'aikatar ana tunanin zata kawo mafita ga rikicin manoma da makiyaya dake faruwa duk shekara. Hakanan bayan kirkirar sabbin ma'aikatu ana kuma tunanin shugaban kasan zai samar da kananan ministoci a sauran ma'aikatun da basu dasu. Masu kula da al'amuran yau da kullun da masu sharhi a harkokin siyasa sun caccaki gwamnatin Tinubu saboda kin saka kananan ministoci a wasu ma'aikatu
Ba A Bi Umarnin Da Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya Bayar Na Sake Fasalin Naira Ba>>Tsohon Daraktan CBN Ga Kotu

Ba A Bi Umarnin Da Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya Bayar Na Sake Fasalin Naira Ba>>Tsohon Daraktan CBN Ga Kotu

labaran tinubu ayau, Siyasa
Tsohon Daraktan Ayyuka na Kudi a Babban Bankin Najeriya (CBN), Ahmed Bello Umar, ya shaida wa babbar kotun Abuja da ke Maitama cewa ba a bi umarnin da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar na sake fasalin Naira ba. Ya bayyana cewa takardar kudin Naira da aka sake gyarawa a karkashin tsohon Gwamna Godwin Emefiele sun sha bamban da bayanan da tsohon shugaban kasar ya amince da su. Daga: Abbas Yakubu Yaura
Da Dumi-Dumi: ‘Nan Ba da Jimawa Ba Za Mu Aikawa Majalisa Da Kudirin Doka Kan Sabon Albashin Ma’aikata’ – Tinubu

Da Dumi-Dumi: ‘Nan Ba da Jimawa Ba Za Mu Aikawa Majalisa Da Kudirin Doka Kan Sabon Albashin Ma’aikata’ – Tinubu

labaran tinubu ayau, Siyasa
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce nan ba da dadewa ba zai aika da sabuwar dokar mafi karancin albashi ga majalisar dokokin kasar Tinubu ya bayyana hakan ne a jawabinsa na ranar dimokradiyya a ranar Laraba. Ya ce gwamnatinsa ba ta murkushe kungiyar kwadago ba kamar yadda gwamnatin kama-karya ta yi. “Mun yi shawarwari cikin nasara kuma mun yi tattaunawa tare da kungiyoyin kwadago a kan mafi karancin albashi na kasa, nan ba da jimawa ba za mu aika da kudirin zartarwa ga Majalisar Dokoki ta kasa domin tabbatar da abin da aka amince da shi a cikin shekaru biyar masu zuwa ko kasa da haka,” in ji shi. Ku tuna cewa kwamitin mafi karancin albashi na kasa ya mika rahotonsa ga shugaban kasa a ranar Litinin. A cikin rahoton, gwamnatin tarayya ta gabatar da shawarar mafi karancin alb...
Akwai barazanar ambaliya a jihohi 31 da ƙananan hukumomi 148′

Akwai barazanar ambaliya a jihohi 31 da ƙananan hukumomi 148′

Siyasa
Hukumar Bayar da agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA ta ce akwai hasashen jihohin ƙasar 31 da ƙananan hukumomi 148 ka iya fuskantar ambaliya a damunar bana. Hukumar ta buƙaci gwamnatocin jihohin ƙasar da su bi gargaɗinta sannan su aiwatar da matakan kariya daga bala'in ambaliya domin tabbatar da kare rayuka da dukiyoyi al'umma. Shugabar hukumar, Zubaida Umar wadda ta tabbatar da hakan a yayin wata ganawa da jami'an gwamnatin jihar Edo, ta nanata muhimmancin haɗa ƙarfi da ƙarfe da jihar wajen samar da shirin ko-ta-kwana domin tunkarar barazanar ta ambaliya. Hukumar ta NEMA dai ba ta lissafa jerin sunayen jihohin da ƙananan hukumomi ba amma ta ce yawanci birane da garuruwan da ke kusa da ruwa ka iya fuskantar barazanar.