Wednesday, January 15
Shadow

Tsaro

An sace dalibai da wasu 25 a hanyar zuwa Nasarawa

An sace dalibai da wasu 25 a hanyar zuwa Nasarawa

Tsaro
Rahotanni sun bayyana cewa, an yi garkuwa da mutane 25 da kuma wasu dalibai akan hanyar Abuja zuwa Nasarawa. Lamarin ya farune ranar Juma'a kamar yanda jaridar Punch ta ruwaito kuma yawan wadanda aka yi garkuwa dasu sun kai 30. Direban motar dai ya kubuta inda ya kaiwa 'yansanda rahoton faruwar lamarin. Hukumar 'yansanda ta jihar Nasarawa ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin kakakinta,Rahman Nansel inda tace an kubutar da mutane 3 daga cikin wadanda aka yi garkuwa dasu kuma ana kan kokarin kubutar da sauran.
Kalli Hotunan wata maboyar ‘yan Bin-di-ga da ‘yansanda suka gano

Kalli Hotunan wata maboyar ‘yan Bin-di-ga da ‘yansanda suka gano

Abuja, Tsaro
'Yansanda a Abuja sun bankado wata maboyar 'yan Bindiga dake gidan Dogo a cikin daji Kweti dake kusa da babban birnin tarayya, Abuja. Kakakin 'yansandan Abuja, SP Josephine Adeh ta bayyana hakan ga manema labarai inda tace an bankado maboyar ne bayan samun bayanan sirri. An kama mutane 4 da ake zargi bayan da aka yi musayar wuta tsakaninsu da jami'an tsaron. Dukansu sun amsa cewa su masu garkuwa da mutanene. An kubutar da wasu da suka yi garkuwa dasu inda aka mika su hannun 'yan uwansu.
‘Yan sanda sun kama mutum huɗu kan zargin garkuwa da mutane a dazukan Abuja

‘Yan sanda sun kama mutum huɗu kan zargin garkuwa da mutane a dazukan Abuja

Tsaro
Rundunar 'yan sandan birnin Abuja, tare da haɗin gwiwa dakarun sahen yaƙi da manyan laifuka da 'yan sanda farin kaya, da mafarauta, sun wargaza sansanonin wasu 'yan bindiga a ƙauyen Gidan Dogo da dajin Kweti da ke kan iyakar Abuja da Kaduna. Cikin wata sanarwar jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar 'yan sandan birnin, SP Josephine Adeh, ta fitar ta ce bayan samun bayanan sirri, jami'an tsaron suka kai samame dajin ranar 7 ga watan Mayu, in da suka kama mutum huɗu da suke zargi. Sanarwar ta ce mutanen da suka kama, sun faɗa wa 'yan sanda cewa suna cikin wani gungun masu garkuwa da mutane mai suna, 'Mai One Million', waɗanda suke da alhakin kai hare-hare tare da garkuwa da mutane a birnin Abuja da kewaye. 'Samamen wanda aka samu musayar wuta tsakanin ɓangarorin biyu, ya tilasta wa 'ya...
Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan bindiga biyar tare ƙwato makamai a Kaduna

Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan bindiga biyar tare ƙwato makamai a Kaduna

Tsaro
Sojojin Najeriya da ke aiki da rundunar 'Operation Whirl Punch' mai yaƙi da masu garkuwa da mutane sun kashe 'yan bindiga biyar a yankin Dantarau da ke ƙaramar hukumar Kajuru a jihar Kaduna. Cikin wata sanarwa da kwamishin tsaro da al'amuran cikin gida na jihar, Samuel Aruwan ya fitar, ya ce dakarun sojin waɗanda ke aiki a yankunan ƙananan hukumomin Kachia da Kajuru sun kuma ƙwato makamai. ''Sojojin sun ƙwato bindiga ƙirar AK-47 guda biyu, da bindiga ƙirar gida guda ɗaya, ƙwason zuba alburushi na Ak-47 guda tara, da harsasai 250 da babura biyu da wayoyin oba-oba biyu'', in ji sanarwar. Sanarwar ta ƙara da cewa sojojin sun kuma lalata sansanonin 'yan bindigar a yankin Sabon Birnin Daji da ke ƙaramar hukumar Igabi. Aruwan ya kuma ce a lokacin samamen sojojin sun yi musayar wuta d...
Gwamnatin tarayya ta haramtawa ‘yan mata ‘yan kasa da shekaru 18 shiga Otal

Gwamnatin tarayya ta haramtawa ‘yan mata ‘yan kasa da shekaru 18 shiga Otal

Siyasa, Tsaro
Gwamnatin tarayya karkashin Ma'aikatar mata ta haramtawa Kananan yara 'yan kasa da shekaru 18 shiga otal. Ministar matan, Uju Ohaneye ce ta bayyana hakan inda tace dole duka otal din dake Najeriya dolene su bi wannan umarni. Tace duk Otal din da aka samu bai bi wannan umarni ba zai iya fuskantar hukuncin dakatarwa. Tace an dauki matakanne dan kawar da matsalar safarar 'yan mata. Hakan na zuwane dai a yayin da wasu bidiyon 'yan mata dake da shekarun tsakanin 15 zuwa 16 aka ga an yi safarar su zuwa kasar Ghana dan yin Karuwanci.
Hotunan Mahajjata da aka kama sun yi safarar Kwa-ya zuwa kasa me tsarki

Hotunan Mahajjata da aka kama sun yi safarar Kwa-ya zuwa kasa me tsarki

Hajjin Bana, Tsaro
Hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi ta NDLEA ta kama wasu mahajjata a otal din Emerald Hotel dake Ladipo a jihar Legas suna hadiye hodar Iblis da zasu tafi da ita kasa me tsarki. An kamasu ne ranar Laraba, 5 ga watan Yuni kamin tashin jirgin su zuwa kasa me tsarkin. Kakakin hukumar, Femi Babafemi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar inda yace wadanda aka kamadin, Usman Kamorudeen na da shekaru 31, sai kuma Olasunkanmi Owolabi me shekaru 46, akwai kuma Fatai Yekini me shekaru 38, sai Ayinla Kemi.me shekaru 34. Yace an kwace dauri 200 na hodar Iblis din daga hannun wadanda ake zargi.
Gwamnin ban tausai:Ji yanda mutane suka nutse a ruwa yayin da suka shiga kwale-kwale dan tserewa harin ‘yan Bin-di-ga a jihar Naina

Gwamnin ban tausai:Ji yanda mutane suka nutse a ruwa yayin da suka shiga kwale-kwale dan tserewa harin ‘yan Bin-di-ga a jihar Naina

Duk Labarai, Jihar Naija, Tsaro
Mutane aun nutse a ruwa yayin da suka shiga jirgin ruwa dan tserewa harin 'yan Bindiga a garin Gurmana dake karamar hukumar Shirori jihar Naija. Yawanci idan maharan suka kai hari, mutane kan tsere zuwa wani tsibiri har sai kura ta lafa kamin su koma gidajensu. Mutanen daai sun tserene ranar Laraba. Saidai ranar Alhamis, yayin da suke dawowa daga kan tsibirin da suka samu mafaka, mutane 4 sun mutu, bayan da jirgin ruwan da suke ciki yayi hadari.