Wednesday, January 15
Shadow

Tsaro

Gwamnatin Abia ta sa ladan N25m ga wanda ya fallasa mutanen da suka kashe sojoji

Gwamnatin Abia ta sa ladan N25m ga wanda ya fallasa mutanen da suka kashe sojoji

Tsaro
Gwamnatin jihar Abia da ke kudu maso gabashin Najeriya ta saka ladan naira miliyan 25 ga duk mutumin da ya bayar da bayanan da za su taimaka a kama mutanen da suka kashe sojoji a jihar. Cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labaran jihar, Okey Kanu ya fitar, gwamnatin jihar ta aike da sakon ta'aziyya ga babban hafsan sojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja kan faruwar lamarin. A ranar Alhamis ne wasu 'yan bindiga suka afka wa sojoji a wani shingen bincike a mahadar Obikabia da ke yankin tsaunin Ogbor, tare da kona motar aikinsu. Rahotonni sun ce wasu sojojin sun samu tsallake rijiya da baya a harin. “Domin samun saukin kama maharan, gwamnati ta yi alkawarin bayar da ladan naira miliyan 25 ga duk wanda ya bayar da bayanan da za su taimaka wajen kama su,'' in ji s...
An kulle kasuwanni da makarantu yayin da sojoji ke nema  wanda suka kashe sojoji 5 a garin Aba

An kulle kasuwanni da makarantu yayin da sojoji ke nema wanda suka kashe sojoji 5 a garin Aba

Tsaro
Garin Aba ya rikice inda sojoji suka mamayeshi bayan kisan abokan aikinsu 5. Wasu da ake kira da 'yan Bindigar da ba'a san ko su wanene ba amma ana kyautata zaton 'yan IPOB ne kawai da suke fakewa da wannan sunan suka yi kisan. Sun yi kisanne ranar Laraba bayan sun tursasa kowa ya je gida ya zauna dan tunawa da mutanen da suka mutu a yakin Biafra. Lamarin yasa hukumar sojojin Najeriya ta sha Alwashin sai ta rama wannan kisa da kakkausar murya. Rahoton jaridar Vanguard yace sojojin sun shiga kasuwanni suka tursasa mutane suka kulle shaguna da kuma a jiya, Juma'a yawanci yara basu je makaranta ba a garin. Hakanan an ga jirage masu saukar Angulu suna shawagi a sararin samaniyar wajan.
Idan har yau, Kwanaki 3 bayan shugaban kasa yayi dokar sabon taken Najeriya baka iya rerashi ba, kai me laifine kana cin amanar kasa, kuma idan aka kamaka zaka dandana kudarka>>Hukumar ‘Yansanda

Idan har yau, Kwanaki 3 bayan shugaban kasa yayi dokar sabon taken Najeriya baka iya rerashi ba, kai me laifine kana cin amanar kasa, kuma idan aka kamaka zaka dandana kudarka>>Hukumar ‘Yansanda

Siyasa, Tsaro
Hukumar 'yansandan jihar Legas ta bakin tsohuwar kakakin hukumar, Dolapo Badmus ta bayyana cewa rashin iya taken Najeriya, kwakaki 3 bayan shugaban kasa ya saka shi a matsayin doka babban laifi ne. Ta bayyana hakane a shafinta na Instagram inda take bayar da misalin wani me makaranta data sa a kama saboda yana rera tsohon taken Najeriyar. Tace rashin iya taken Najeriyar cin amanar kasa ne. Ta baiwa mutane shawarar su samu lauyoyi su musu karin bayani. ‘’If, as at today, three days after the President of Federal Republic of Nigeria signed and assented the New National Anthem into law and you are not able to recite it in a whole, then you are a suspect I just passed through a private school and I could here them singing the old National Anthem! "Arise oh compatriots"! (We are...
Za’a kama shugaban wata makaranta saboda ya bar dalibansa na rera tsohon taken Najeriya

Za’a kama shugaban wata makaranta saboda ya bar dalibansa na rera tsohon taken Najeriya

Siyasa, Tsaro
Tsohuwar kakakin 'yansandan jihar Legas, Dolapo Badmus ta yi kiran a kama shugaban wata makaranta me zaman kanta da babban malamin makarantaar saboda rera tsohon taken Najeriya. Ta bayyana cewa, ta zo wucewa ta kusa da makarantar ne sai ta ji suna rera tsohon taken Najeriyar. Tace tuni ta yiwa 'yansanda magana kan a kamasu tare da gurfanar dasu a gaban kotu dan musu hukunci. Tace kwanaki 3 bayan da shugaban kasa ya sakawa dokar canja taken Najeriyar hannu, duk wanda aka samu bai iyashi ba, to me laifi ne. Tace kada wanda ya tambayeta laifin me suka yi, duk wanda ke da tambaya, ya samu lauya ya masa karin bayani. Tace duk wanda bai iya sabon taken Najeriya ba, to yana cin amanar kasane. ‘’If, as at today, three days after the President of Federal Republic of Nigeria sign...
Kalli Hotuna: An kamashi da ma-ka-mai wanda yake shirin sayarwa da ‘yan Bindiga

Kalli Hotuna: An kamashi da ma-ka-mai wanda yake shirin sayarwa da ‘yan Bindiga

Tsaro
'Yansanda a jihar Filato sun kama wani mutum me matsakaitan shekaru da makamai da yake shirin kaiwa 'yan Bindiga. Mutumin ya taho ne daga jihar Zamfara. An kama mutuminne a tashar mota ta NTA park dake Jos. Shugaban tashar, Ibrahim Maikwudi ya tabbatarwa da manema labarai da faruwar lamarin. Yace kadan ya rage mutane su kashe wanda ake zargin amma jami'an tsaro suka tseratar dashi.
A cikin shekara daya da muka yi muna mulki, mun yi maganin Boko Haram>>Gwamnatin Tinubu

A cikin shekara daya da muka yi muna mulki, mun yi maganin Boko Haram>>Gwamnatin Tinubu

Tsaro
Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta bayyana cewa ta yi nasarar yin maganin kungiyar Boko Haram. Gwamnatin ta bayyana hakane ta bakin sakataren gwamnatin tarayyar, George Akume. Ya bayyana hakane a Abuja wajan kaddamar da wani Littafi da aka yi kan cika shekara daya da kafuwar Gwamnatin Tinubu. Yace babu wanda zai yi jayayyar cewa gwamnatin Bola Ahmad Tinubu ta yi nasarar gamawa da Kungiyar Boko Haram. Saidai yace har yanzu suna yaki da Kungiyar masu garkuwa da mutane.
Zamu rama kashe mana sojoji 5 da kungiyar IPOB suka yi, zamu tabbatar mun yi maganinsu>>Inji Hukumar sojojin Najeriya

Zamu rama kashe mana sojoji 5 da kungiyar IPOB suka yi, zamu tabbatar mun yi maganinsu>>Inji Hukumar sojojin Najeriya

Tsaro
Hukumar sojojin Najeriya ta tabbatar da kisan sojoji 5 da kungiyar IPOB suka yi. Hukumar tace an kashe sojojin ne dake rundunar Operation UDO KA da aka kai Obikabia. Tace akwai kuma farar hula 6 da suma aka kashe a yayin harin. Kakakin hedikwatar tsaro, Majo Janar Edward ne ya bayyana hakan inda yace zasu tabbatar sun rama wannan kisan da aka musu. Hukumar sojin tace maharan sun je wajanne a motocin Prado 3 dake da bakin gilashi sannan akwai wasu kuma a yankin da suma suka farwa sojojin.
Hoto: Dansanda ya kash-she wannan matashin saboda yaki bashi cin hancin Naira 200

Hoto: Dansanda ya kash-she wannan matashin saboda yaki bashi cin hancin Naira 200

Tsaro
Ana zargin 'yansanda sun kashe wannan mutumin me shekaru 40 a titin Azikoro Road dake Yenagoa ta jihar Bayelsa saboda yaki bada cin hancin Naira dari biyu(200). Rahoto ya bayyana cewa, mutumin me suna Benalayefa Asiayei yana kan hanyarsa ta komawa gidane daga wajan aiki da misalin karfe 8 na yamma yayin da aka kasheshi. Bayan da 'yansandan suka kasheshi, sun tsere daga wajan amma wani daga cikin shaidun abinda ya faru sun dauki hotunansu. Kakakin 'yansandan jihar, Musa Mohammed ya tabbatar da faruwar lamarin kuma yace sun tantance wanda ake zargi. Iyalan mamakin sun ce suna neman adalci.