Friday, July 17
Shadow

Kalli Bidiyon Yanda ICPC suka hana Iyalan Malam Nasiru Ahmad El-Rufai bashi Abinci

Hukumar ICPC ta hana iyalan Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai bashi abinci.

Matarsa Aisha ce ta bayyana haka a wani Bidiyo data wallafa a kafafen sada zumunta inda tace gata ta zo kaiwa mijin nata abinci amma ICPC sun hanata ta bashi.

Hakanan Dansa, Hon. Bello El-Rufai ya tabbatar da hakan inda yace antinsu ta kaiwa babansu abinci a ofishin ICPC kamar yanda ta saba da yamma amma aka hanata shiga inda aka ce an hana shigar masa da abinci idan yamma ta yi.

Hakanan yace Likitansa ma ya je ganinsa aka hanashi ganinsa.

Yace wannan take hakki ne wanda bai kamata ba.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Wata mata da ciwon Dajin Nònò ya kamata, har aka yànqèshì, data shafa Hankicin da na yiwa addu'a, wani nonon ya sake fitowa>>Inji Fasto Enoch Adeboye

Ya bayyana cewa suna neman a dawowa da babansu hakkinsa na dan Adam kamar yanda kundin tsarin Mulkin Najeriya ya bashi dama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *