fbpx
Monday, May 16
Shadow

Kasuwanci

Gwamnatin tarayya ta rage harajin shigo da motoci daga kasar waje zuwa kaso 20

Gwamnatin tarayya ta rage harajin shigo da motoci daga kasar waje zuwa kaso 20

Kasuwanci
Gwamnatin tarayya ta sanar da rage harajin da take karba akan motocin da aka shigo dasu daga kasar waje daga kaso 35 zuwa kaso 20.   Kakakin hukumar kwastam, Timi Bomodi ne ya bayyana haka bayan da jaridar The Cable ta tuntubeshi.   Ya bayyana cewa, wannan ragin zai yi amfani akan dabbi da tsaffin motocin da aka shigo dasu Najeriya daga kasashen waje.   Ya kuma bayyana cewa, Tuni suka fara aiki da wannan sabon tsari.
Duk da matsin tattalin Arziki:Dangote da sauran masu kudin Najeriya sun kara kudancewa

Duk da matsin tattalin Arziki:Dangote da sauran masu kudin Najeriya sun kara kudancewa

Kasuwanci
Jaridar Forbes me fitar da jadawalin masu kudin Duniya, tace masu kudin Najeriya sun kara kudancewa a shekarar 2022.   Hakan na faruwa ne duk da cewa zuwa cutar coronavirus ya karade Duniya inda aka samu matsin tattalin arziki.   Dangote wanda shine na daya a Africa ya samu karin arziki daga biliyan $11.5 a shekarar 2021 zuwa biliyan $14 a shekarar 2022.   Mike Adenuga kuwa ya samu karin arziki ne daga biliyan $6.1 a shekarar 2021 zuwa Biliyan $7.3 a shekarar 2022.   Shi kuwa Abdulsamad Rabiu ya samu karuwar arziki daga Biliyan $4.9 a shekarar 2021 zuwa Biliyan $6.9 a shekarar 2022.
Mutanen Najeriya da yawa sun harzuka saboda rufe musu layukan waya duk da cewa sun yi musu rijista da NIN

Mutanen Najeriya da yawa sun harzuka saboda rufe musu layukan waya duk da cewa sun yi musu rijista da NIN

Kasuwanci
A jiyane aka fara dakatar da layukan wayar hannu bayan umarnin gwamnatin tarayya na rufe layukan da basu yi rijista da NIN ba.   Saidai lamarin ya rutsa da wadanda suka yiwa layukan nasi rijista wanda hakan ya harzukasu.   Zuwa yanzu dai an rufe layukan waya da suka kai miliyan 75, saidai ta rutsa da hadda wanda suke da rijista.   Saidai tuni MTN ta bayar da hakuri inda tace duk wanda aka rufewa layin waya bisa kuskure ya aika a gyara masa.   An dai mutane na layin kammala rijistar NIN bayan fara aiwatar da dokar rufe layukan.
Banki Musulunci yana da amfani sosai – Sanusi Lamido Sanusi

Banki Musulunci yana da amfani sosai – Sanusi Lamido Sanusi

Kasuwanci
Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Alhaji Muhammadu Sanusi, ya zargi wasu ‘yan Najeriya da yin amfani da addini domin a boye gaskiya. Ya yi magana a kan cece-kucen da ya biyo bayan bullo da tsarin hada-hadar kudi da babu ruwa wanda aka fi sani da bankin Musulunci. Sanusi, wanda ya kasance bako a wajen taron harkar kasuwanci na kasa a karo na 5, wanda kungiyar musulmi maza masu sha’awar kasuwanci da sana’o’i da suka gudanar a jami’ar Legas, ya ce babban bankin CBN ya yi kokarin bayyana wa mutane cewa babu wani abu kamar mayar da kirista Musulmai a cikin bankin Musulunci a kasar nan. Sai dai ya ce babban bankin na CBN ba zai iya tsayawa ba saboda ‘yan kalilan din da suka ki sauraron bayanin bankin koli, yana mai cewa alfanun tsarin bankin Musulunci na da yawa....
Katar Airways ta kaddamar da yin jigila a Kano

Katar Airways ta kaddamar da yin jigila a Kano

Kasuwanci
Jirgin na farko na Qatar Airways ya sauka a Filin Jirgin Sama na Mallam Aminu Kano, MAKIA. Jirgin ya sauka ne cikin farin ciki da ga masu ruwa da tsaki a harkar sufurin jiragen sama. Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa jirgin, Boeing 787 Dreamliner, ya sauka a filin jirgin da misalin karfe 11:10 na safe. Jami’an hukumar kula da filayen tashi da saukar jiragen sama na tarayyar Najeriya FAAN ne su ka tarbe jirgin ta hanyar fesa masa ruwa kamar yadda a ka saba. Jirgin na Qatar zai fara jigilar fasinjoji zuwa Kano a wani bangare na shirin fadada kasar. Hakan zai biyo bayan Fatakwal, Jihar Ribas ranar Alhamis. Mai Martaba Sarkin Kano Aminu Ado Bayero da Jami’an Gwamnatin Jihar Kano da Kamfanin Jiragen Sama na Qatar Airways da dai sauransu sun tarbi Jirgin Qatar Airways zuw...
Karya ake mana: Ba sayar da shinkafar da muka kwace daga hannun ‘yan kasuwa ba muke>>Inji hukumar Kwastam

Karya ake mana: Ba sayar da shinkafar da muka kwace daga hannun ‘yan kasuwa ba muke>>Inji hukumar Kwastam

Kasuwanci
Hukumar Kwastam ta bayyana cewa basa sayar da shinkafar da suka kwace daga hannun 'yan kasuwa.   Tace duk rade radin da ake akan hakan ba gaskiya bane.   Tace idan shinkafar da suka kwace me kyauce, zasu baiwa 'yan gudun hijira, idan kuma ba mai kyau bace, to zasu baiwa masu gidajen kaji.   Daya daga cikin kwamandan Kwastam, Dera Nnadi ne ya bayyana haka.
Arzikin Dangote ya ƙaru da dala biliyan biyu

Arzikin Dangote ya ƙaru da dala biliyan biyu

Kasuwanci
Arzikin Aliko Dangote ya ƙaru matuƙa yayin da yake yunƙurin kammala shekarar 2021 da arzikin da bai taɓa samu ba cikin shekara bakwai sakamakon haɓakar ribarsa a ɓangaren siminti. Haɓakar kasuwar hannun jari a kamfaninsa na siminti da kuma tashin farashin man fetur da takin zamani sun taimaka wa Dangote inda dukiyarsa ta ƙaru da dala biliyan 2.3 a 2021 zuwa biliyan 20.1 jumilla, kamar yadda mujallar Bloomberg ta ruwaito. Rabon da dukiyarsa ta kai yawan haka tun 2014, lokacin da ta kai dala biliyan 26.7 a watan Yunin shekarar, a cewar jaridar. Tashin farashin kayayyakin gini a Najeriya, wadda ke da mafi girman tattalin arziki a Afirka, sun haɓaka ƙarfin jarin kamfanin Dangote Cement plc. Nan gaba kaɗan ake sa ran Dangote zai kammala ginin matatar man fetur kan dala biliyan 19, wadda z...
Bamu da iko akan farashin Gas din girki>>Gwamnatin Tarayya

Bamu da iko akan farashin Gas din girki>>Gwamnatin Tarayya

Kasuwanci
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa bata da iko akan farashin gas din girki dake ta hauhawa.   Shugaba Buhari ya bayyana damuwa kan lamarin, kuma farashin gas din na tafiyane da farashin da ake amfani dashi a Duniya.   Karamin Ministan man fetur, Timipre Sylva ne ya bayyana haka inda yace gwamnati ta tsame hannunta daga harkar gas dan haka ba itace ke kula da farashinsa ba.