Maganin hawan jini
menene hawan jini
Hawan jini yana nufin idan jinin dake gudana a cikin jijiyoyinka gudunsa yayi yawa.
Idan aka maka gwaji ya nuna 120/80 to baka da hawan jini.
Amma indan ya zama 130/80 ko 140/90 ko 180/120 to jininka ya hau. Yawanci hawan jini bai cika nuna wata alama ba.
Idan aka barshi ba tare da an nemi magani ba, yana iya kawo ciwon zuciya ko shanyewar rabin jiki.
Cin abinci me gina jiki, da cin abinci wanda babu gishiri a cikinsa sosai yana taimakawa wajan magance matsalar hawan jini.
Hakanan motsa jiki da shan magani a bisa ka'ida duk suna kawo saukin cutar hawan jini da ikon Allah.
Maganin hawan jini ana samunsa ne ta hanyar cin abinci me gina jiki da motsa jiki akai-akai, da shan magani.
Idan ana neman maganin hawan jini na gargajiya, muna da maganin hawan ...