Friday, February 7
Shadow

Maganin hawan jini

menene hawan jini

Hawan jini yana nufin idan jinin dake gudana a cikin jijiyoyinka gudunsa yayi yawa.

Idan aka maka gwaji ya nuna 120/80 to baka da hawan jini.

Amma indan ya zama 130/80 ko 140/90 ko 180/120 to jininka ya hau. Yawanci hawan jini bai cika nuna wata alama ba.

Idan aka barshi ba tare da an nemi magani ba, yana iya kawo ciwon zuciya ko shanyewar rabin jiki.

Cin abinci me gina jiki, da cin abinci wanda babu gishiri a cikinsa sosai yana taimakawa wajan magance matsalar hawan jini.

Hakanan motsa jiki da shan magani a bisa ka’ida duk suna kawo saukin cutar hawan jini da ikon Allah.

Karanta Wannan  Alamomin hawan jini

Maganin hawan jini ana samunsa ne ta hanyar cin abinci me gina jiki da motsa jiki akai-akai, da shan magani.

Idan ana neman maganin hawan jini na gargajiya, muna da maganin hawan jini sadidan wanda ke so yana iya mana magana ta WhatsApp a wannan lambar ko kira, muna aikawa kowace jiha, 09070701569.

Kalar motsa jikin da ake so me hawan jini yayi shine akalla ya rika yinsa a kullun na tsawon mintuna 30.

Kuma ba wai sai mutum yayi motsa jiki me wahalar wa ba, tafiya da sauri-sauri na tsawon mintuna 30 yana taimakawa sosai. Saidai masana kiwon lafiya sun ce sai mutum ya jera watanni 1-3 yana motsa jiki kullun kamin motsa jikin ya masa maganin hawan jini.

Karanta Wannan  Alamomin hawan jini

Hakanan idan me hawan jini yana shan taba, masana kiwon lafiya sun ce ya daina shan taba dan hakan zai taimaka masa sosai wajan maganin hawan jini.

Hakanan rage cin gishiri ko a rika amfani da gishiri kadan a cikin abinci yana taimakawa sosai wajan maganin hawan jini.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *